Ba mu san makomarmu ba a cikin gwamnatin Tinubu: in ji masu bukata ta musaman

Masu bukata ta musaman
Bayanan hoto, Masu bukata ta musaman sun koka kan nade-naden shugaba Tinubu

Wasu kungiyoyin masu bukata ta musamman a arewacin Nijeriya, sun fara tsokaci tare da korafi game da nade-naden mukamai da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a baya-bayan nan.

Northern Nigeria Disability Forum (NNDF) na daya daga cikin kungiyoyin da suka ce jikinsu ya fara yin sanyi kasancewar har yanzu babu mai lalura ta nakasa da Shugaba Tinubu ya nada muƙamin minista ko mai bayar da shawara.

Masu bukata ta musaman sun kuma ce sun lura da take-taken shugaba Bola Ahmed Tinubu kamar ba zai ba su wani mukami ba, saboda ana neman kamala nade naden, amma har yanzu layi ba zo kansu ba.

Alhaji Yarima Sulaiman Ibrahim shi ne shugaban masu bukata ta musaman shiyyar arewacin Nijeriya ya kuma shaidawa BBC cewa akwai dokar da ta bada dama a dama da su a sha’anin shugabanci:

“ Akwai dokar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a 2018, dokar ta ce duk nade-naden da za a yi a Nijeriya dole ne a bamu kashi biyar cikin dari”, in ji shi.

Alhaji Ibrahim ya yi misali da cewa idan za a dauki ministoci 40 a Najeriya, za su samu ministoci biyu kennan daga bangarensu.

“ A yanzu an nada minsitoci 48, ka ga za a bamu ministoci akalla guda 3”, In ji shi.

Masu bukata ta musaman a Najeriyar sun ce a yanzu a shugabancin da ake yi, ba su da minista, ba su da mai ba shugaban kasa shawara ko mamba a cikin kwamitin gudanarwa na ma’aikatu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sun kuma ce damuwarsu ita ce ba su ma san makomarsu ba a cikin gwamnatin shugaba Tinubu.

To sai dai a dayan bangaren mataimakin na musaman mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ya ce kamar akwai gaggawa a cikin a alamarin masu bukata ta musaman din.

” Wannan magana ta zuba ido, har yanzu ba a ga mukami ba, ina ganin kamar akwai alama ta gaggawa da ta yi yawa a cikin alamarin domin ya kamata a lura da cewa gwamnatin nan har yanzu mukaman da ta nada ‘yan kadan ne”,

” Ko kashi 10 cikin 100 ba a nada ba na mukaman da ya kamata a ce gwamnatin ta yi. Ya kamata a ce an zuba ido, a tsaya a ga me zai faru, har zuwa lokacin da gwamnatin za ta kamala, ko za ta yi ko kuma sai ta yi nisa a cikin wannan aiki na nade-naden mukamai kafin a fara yin korafi”, in ji shi.

Masu bukata ta musaman sun yi kira ga shugaban Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin kasar da su yi la'akari da masu bukata ta musaman idan za su bayar da mukamai saboda a cewarsu yin hakan zai taimaka wajan kula da alamuransu tare da rage yawan masu bara barace.