Mutanen da suka samu shiga ƙunshin ministocin Tinubu

Ana ci gaba da tsokaci a kan ƙunshin sunayen mutum 28 da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattijan ƙasar don neman amincewarta kafin naɗa su ministoci.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godwill Akpabio ne ya gabatar da sunayen a gaban zauren majalisar.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya kafin ƙarewar wa'adin wata biyu da tsarin mulkin Najeriya ya gindayawa shugaban ƙasa ya tabbatar da naɗa ministocinsa.
Miƙa sunayen ga alama zai rage ka-ce-na-ce da jita-jitar da aka yi ta yaɗawa ne kawai game da sabbin ministocin da Tinubu zai yi aiki da su. Amma har yanzu da sauran tsalle, don kuwa daga lissafi kawai za a iya fahimtar cewa sunayen ba su cika ba.
Akwai jihohin da har yanzu ba a gabatar da sunan wakili/wakilansu a sabuwar majalisar ministocin Tinubu da zai kafa ba.
Bisa tanadin tsarin mulki, kowacce cikin jihohin Najeriya 36 da Abuja, babban birnin ƙasar, suna da damar samun aƙalla minista ɗaya,
Bugu da ƙari, an ga jihohin da suka samu minista biyu a jerin sunayen da aka gabatar kamar Hannatu Musawa da Arch Ahmed Ɗangiwa daga Katsina da Farfesa Ali Pate da Yusuf Maitama Tuggar daga Bauchi, sai Betta Edu da John Eno daga jihar Kuros Riba.
Jerin sunayen kamar yadda aka yi tsammani ya ƙunshi mutanen da suka fito ba kawai daga jam'iyya mai mulki ba, an ga har da sunayen 'yan adawa musamman daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP kamar Nyesom Wike.
Ban da sunayen tsoffin gwamnoni kamar Nasir El-rufa'i da David Umahi da Mohammed Badaru Abubakar, an ga sunayen ƙwararrun masana tattalin arziƙi da jami'an lafiya da lauyoyi sai kuma abokan ƙawancen Tinubu.
Daga cikin sunayen da za a iya cewa sun yi bazata har da Dele Alake, ƙasa da wata biyu da naɗa shi matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare.
Akwai Abubakar Kyari daga jihar Borno wanda ya riƙe muƙamin shugaban riƙo na jam'iyyar APC na ƙasa, ga Lateef Fagbemi babban lauyan Najeriya mai lambar SAN daga jihar Kwara.
Me ya faru da sauran jihohin?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yanzu dai a iya cewa kallo ya koma zuwa Kano da Osun da Gombe, suna cikin jihohin da ba a ga sunayen mutanensu ba a ƙunshin da Tinubu ya gabatar.
Shugaban dai ya cika ƙa'idar da tsarin mulki ya gidanya masa na gabatar da sunayen ministocinsa a cikin wata biyu, sai dai ba a san lokacin da zai miƙa cikon sunayen ba. Bai dai bayyana dalilin rashin miƙa sunayen gaba ɗayansu ba a lokaci guda.
Rahotanni dai sun ce an yi ta kai ruwa-rana game da jerin sunayen ministocin, bisa la'akari da hujjoji ko dalilai masu yawa da sai shugaban ƙasar ya yi la'akari da su wajen tantance mutanen da za su shiga ƙunshin ministocin nasa.
An ce lamarin ya ƙara zama mai wahalar sha'ani ga Tinubu, saboda buƙatun tabbatar da daidaiton addinai da muradinsa na son yin tafiya da 'yan adawa bisa ƙudurinsa na kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
Majalisar dattijai dai yanzu ta ɗage zamanta, inda ta tafi hutu.
Ana sa ran za ta dawo bakin aiki don fara tantance sunayen ministocin.
Ga sunayen mutanen da jihohinsu
- Abubakar Momoh - Edo
- Betta Edu - Kuros Riba
- Uche Nnaji - Enugu
- Joseph Utsev - Binuwai
- Hannatu Musawa Katsina
- Nkeiruka Chidubem Onyejocha - Abia
- Stella Okotete - Delta
- Uju Kennedy-Ohanenye - Anambra
- Ahmed Dangiwa - Katsina
- Olawale Edun - Ogun
- Imaan Suleman Ibrahim - Nasarawa
- Bello Muhammad Goronyo - Sokoto
- Nyesom Wike - Ribas
- David Umahi - Ebonyi
- Mohammad Badaru Abubakar - Jigawa
- Nasir El-rufa'i - Kaduna
- Lateef Fagbemi - Kwara
- Doris Aniche Uzoka - Imo
- Yusuf Maitama Tuggar - Bauchi
- Farfesa Ali Pate - Bauchi
- Ekerikpe Ekpo - Akwa Ibom
- Sani Abubakar Ɗanladi - Taraba
- Mohammed Idris - Neja
- Olubunmi Tunji Ojo - Ondo
- Dele Alake- Ekiti
- Waheed Adebayo Adelabu - Oyo
- John Eno - Kuros Riba
- Abubakar Kyari - Borno











