An gano wani sabon wata a sararin samaniya

Watan wanda aka yi wa laƙabi da 2025 PN7 ya daɗe yana tafiya tare da duniyarmu tsawon kusan shekara 60 (wannan zanen hotonsa ne)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Watan wanda aka yi wa laƙabi da 2025 PN7 ya daɗe yana tafiya tare da duniyarmu tsawon kusan shekara 60 (wannan zanen hotonsa ne)
    • Marubuci, Sandrine Lungumbu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Masana kimiyyar sararin samaniya sun gano cewa duniya ta samu wani sabon maƙwabci - wani sabon tauraro da ya yi kama da wata, wanda zai ci gaba da kasancewa a falaƙi har zuwa shekara ta 2083.

To amma kuma fa ba shi kadai ba ne sabon da aka gano cikin taurarin a kusa da duniyarmu, yayin da muke kewaya rana.

Watan wanda karami ne da kuma aka yi masa lakabi da 2025 PN7, ya dade yana tafiya tare da duniyarmu tsawon gomman shekaru.

''Su irin wadannan taurari masu kama da wata suna da ban sha'awa domin ba wai suna kewaya duniyarmu ba ne kamar yadda ainahin shi wata yake kewaya duniyarmu ba, suna dai harabar duniyarmu ne,'' in ji Dr Jenifer Millard, masaniyar harkokin sararin samaniya a cibiyar hangen taurari ta Fifth Star Labs da ke Wales.

Wannan wata ba wani babba ba ne karami wanda tsawonsa kusan mita 20 ne kawai.

Dr Millard ta sheda wa BBC cewa girmansa kamar wani dan gini ne na ofis. ''Kuma muna ganin ya kasance wajen shekara 60, sannan zai iya kra wata shekara 60 din.

Masu bincike na cibiyar nazarin sararin samaniya na Pan-STARRS da ke Hawaii, a Amurka ne suka gano shi.

Cibiyar tana da manya-manyan na'urori na hangen samaniya da ake amfani da su wajen duba taurari da sauran abebadai na sararin sama da ke kusa da duniyarmu.

Yanzu dai ana gano cewa duniyarmu tana da jimillar irin wadannan taurari da suke kamar wata a kusa da ita har guda takwas, da wasu kananan watannin da ba a san yawansu ba, da kuma wasu daban guda biyu wadanda su ma na rikida a gansu kamar wata.

To amma kuma a dukkaninsu babu wanda yake kamar ainahin watan da muka sani.

Taurari masu kama da wata

Ana kiran irin wadannan duwatsu da ke yawo a sararin samniya ne da suna kamar wata, saboda muna ganin suna kewaya duniyarmu ne kamar yadda wata yake yi.

Amma kuma idan aka tsaya aka yi musu kallon tsanaki za a ga a zahiri duwatsu ne irin na samaniya suke kewaya rana kamar yadda duniyarmu ke yi.

Sai dai kuma dukkanin irin wadannan abubuwa na samaniya da muke ganinsu kamar wata amma kanana ne, na wucin-gadi ne suna nan ne zuwa wasu gomman shekaru kawai ko kuma karni amma ba sa kasancewa dindindin a nan.

Hoton wani babban dutse na karfe a sama da ke kan hanyar karo da wata, can kuma ga duniyarmu ana iya hange a baya, da aka dauki hoton daga samaniya.

Asalin hoton, Getty Images

Ƙananan watanni

Shi mitsitsin wata sabanin wannan da ya gabata da muke magana a kansa, abu ne da yake kewaya duniya ko babban tauraro.

'Yan mitsitsan watanni da suke kusa da duniyarmu, 'yan kananan duwatsu ne ko buraguzai na samaniya wadanda maganadisun duniyarmu ke janyo su kusa da duniyar - kuma suna kasancewa a nan ne tsawon kasa da shekara daya kawai.

'Yan kanana ne da suke da wuyar gani, domin zuwa yanzu guda hudu kawai aka taba gani, kuma ma zuwa yanzu sun ba ce ba sa kusa da duniyar tamu a yanzu.

An ga na karshe ne a watan Agusta na 2024, wanda aka yi wa lakabi da 2024 PT5, kuma tsawonshi kamar mita 10 ne kawai.

Nazarin da aka yi a kansa ya nuna alamun cewa, kamar wani bangare ne na dutsen wata da ya balgace, da dadewa, a hankali maganadisun duniyarmu ya janyo shi daga baya kuma ya koma da'irar da ya baro.

Zanen hoton wani dan karamin dutsen samaniya a kusa da wata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ganin wannan dan mitsitsin wata da aka yi wa laƙabi da 2024 PT5 wani bangace ne na wata da ya samu bayan wani dutsen na samaniya ya yi karo da wata

Wata mai baduhu

Daga cikin nau'uka uku na abubuwan da muke dangantawa ko kira da wata za mu iya cewa, wanda yake baduhu shi ne ya fi ban mamaki da kasa gano siddabarunsa.

Ana ganin kamar wani dunkulen gajimare ne ko kura da ke kewaya duniyarmu - ta bayanta ko kuma ta gabanta, yayin da duniyar ke kewaya rana - to amma dai har yanzu babu wani cikakken bayani na kimiyya ko ma dai akwai wannan abu da masana ke kira da wata mai baduhu.

To amma duk da haka Dr Millarda na ganin abu ne da ya kamata a yi nazari a kai.

Masaniyar ta ce : ''Akwai kura mai yawa a samaniya. Ba za a yi mamaki ba idan wadannan burbushin abubuwa da kura ke tattare da su, su ne maganadisun duniya yake janyowa kusa da duniyar.''

Ko waɗannan ƙananan watanni suna da haɗari?

Duk da yadda suke da kusanci da duniyarmu wadannan abubuwa kanana da masana kimiyyar samaniya ke kira kananan watanni, ba su taba zuwa kusa da kusa da za a iya cewa za su iya haddasa wata matsala ga duniyarmu ba.

Hatta wadanda suka fi kusa da duniyarmu ma, suna can nesa sosai idan aka kwatanta nisan da ke tsakanin duniyarmu da wata.

''Ko da ma sun tunkaro duniyarmu, suna tahowa ne a hankali sosai, za mu iya hangensu, har mu iya yin gargadi domin daukar mataki, '' in ji Dr Millard.

Waɗanne duniyoyi kuma suke da irin waɗannan abubuwa masu kama da wata?

An ga irin waɗannan abubuwa masu kama da wata a da'irar duniyar Jupiter, da Venus, da Saturn, da Neptune, da kuma Pluto (Wannan zane ne)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ga irin waɗannan abubuwa masu kama da wata a da'irar duniyar Jupiter, da Venus, da Saturn, da Neptune, da kuma Pluto (Wannan zane ne)
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A 'yan gomman shekarun da suka gabata ne kawai aka iya kera na'urorin hangen sararin samaniya da suke iya ganin ire-iren wadannan 'yan kanana ko mitsi-mitsin duwatsu na sararin samaniya ( wadanda s muke iya kira kamar wata ko taurari)

Baya ga sababbin fasahohin da aka samu a wannan zamanin na gano duwatsun, an kuma samu cigaban da za a iya lissafin tafiyarsu, ta yadda za a iya tabbatar da cewa lalle kam wadannan kananan duwatsu masu wuya ko sarkakiyar fahimta lalle tamkar wata suke.

Dr Millard ta ce : ''Ba wai wasu abubuwa ba ne masu wuyar sha'ani na daban ba, a'a, suna da wuyar gani ne kawai. Idan har suna da wuyar gani a kusa da duniyarmu, to ka duba ka gani ta yaya koma za a iya ganinsu a wani wajen da yake nesa da duniyarmu a samaniya.''

Zuwa yanzu dai an ga irin waɗannan abubuwa masu kama da wata a da'irar duniyar

Jupiter, da Venus, da Saturn, da Neptune, da kuma Pluto, kuma mai yuwuwa za a iya gano wasu a nan gaba.

''Saboda shi sararin samaniya da duniyoyin da ke cikinsa har yanzu yana gudana tare kuma da sauyawa. Ba wai abu ba ne da ya mutu ko yake tsaye cak, komai tafiya yake akai-akai,'' in ji Dr Millard.