Me ya sa Trump ke takura wa shugaban Venezuela?

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sumbaci tutar ƙasar yayin wani bikin rantsar da wasu ƙungiyoyin al'umma

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Vanessa Buschschlüter
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan Latin Amurka
  • Lokacin karatu: Minti 7

Shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da matsa lamba kan Shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

A wani ɓangare na takurar da Washington ke yi masa, a ranar 10 ga watan Disamba Amurka ta kama wani jirgin ruwa a gabar tekun Venezuela bisa zarginsa da safarar man da aka ƙaƙaba takunkumi a kansa.

An girke jiragen ruwan yaƙin Amurka a kusa da ƙasar da ke yankin kudancin Amurka kuma an kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa da ake zargin suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi.

Gwamnatin Trump ta kuma ƙara ninka lada kan bayanan da za su taimaka a kai ga kama Maduro.

Wane ne Nicolás Maduro?

Sugaba Nicolas Maduro na Venezuela

Asalin hoton, Reuters

Nicolás Maduro ya yi fice ne a ƙarƙashin jagorancin shugaba Hugo Chavez da jam'iyyarsa ta United Socialist Party of Venezuela (PSUV).

Maduro, tsohon direban bas kuma shugaban ƙungiyar ƙwadago, ya gaji Chavez kuma ya kasance shugaban ƙasa tun 2013.

A cikin shekaru 26 da Chavez da Maduro suka kwashe suna mulki, jam'iyyarsu ta samu iko da manyan cibiyoyi da suka haɗa da majalisar dokokin ƙasar, da galibin ɓangaren shari'a, da kuma hukumar zaɓe.

A shekarar 2024, an ayyana Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, duk da cewa ƙuri'un da ƴan adawa suka tattara sun nuna cewa ɗan takararsu Edmundo González ne ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.

González dai ya maye gurbin babbar ƴar adawar ƙasar María Corina Machado a zaɓen bayan da aka hana ta tsayawa takara.

An ba ta lambar yabo ta Nobel Peace Prize a watan Oktoba saboda "gwagwarmayar da ta yi don tabbatar da adalci da yunƙurin kawo sauyi daga mulkin kama-karya zuwa dimokraɗiyya".

Machado ta yi fatali da dokar hana tafiye-tafiye da aka ƙaƙaba ma ta kuma ta nufi birnin Oslo a watan Disamba don karɓar lambar yabon bayan ta shafe watanni tana ɓoye.

Me ya sa Trump ya karkata akalarsa kan Venezuela?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Trump ya zargi Maduro da hannu a kwararowar dubban daruruwan ƴan ci-rani daga Venezuela zuwa Amurka.

Suna cikin ƴan Venezuela kusan miliyan takwas da aka ƙiyasta sun tsere daga rikicin tattalin arzikin ƙasar da kuma danniya tun shekara ta 2013.

Ba tare da bayar da shaida ba, Trump ya zargi Maduro da "buɗe ƙofofin da gidajen yari da asibitocin mahaukata " ya kuma "tilasta" fursunonin yin hijira zuwa Amurka.

Trump ya kuma mayar da hankali kan yaƙi da kwararar ƙwayoyi cikin Amurka - musamman ƙwayar fentanyl da hodar Iblis.

Ya ayyana wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka na Venezuela biyu - Tren de Aragua da Cartel de los Soles - a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje kuma ya yi zargin cewa Maduro ne ke jagorantar ƙungiyar Cartel de los Soles.

Maduro ya yi daɗe yana musanta cewa shi shugaban ƙungiyar ne, ya kuma zargi Amurka da yin amfani da "yaƙin da ta ke da miyagun ƙwayoyi" a matsayin uzuri na ƙoƙarin tsige shi da kuma wawashe dimbin arzikin mai na Venezuela.

Manazarta sun yi nuni da cewa, Cartel de los Soles ba ƙungiya ce mai matakai na shugabanci ba, amma kalma ce da ake amfani da ita wajen siffanta jami'an da ke cin hanci da rashawa da suka bar hodar iblis ta na bi ta cikin ƙasar Venezuela.

Me ya sa Amurka ta girke jiragen ruwan yaƙi a yankin Caribbean?

USS Gerald Ford na daga cikin jiragen ruwan yaƙi da aka girke a yankin is Caribbean

Asalin hoton, US Navy/Reuters

Bayanan hoto, USS Gerald Ford na daga cikin jiragen ruwan yaƙi da aka girke a yankin is Caribbean

Amurka ta tura dakarun soji 15,000 da kuma tarin jiragen ruwa masu daukar jiragen saman yaƙi, da na'urori masu lalata makami mai linzami, da kuma jiragen ruwan yaƙi da dama zuwa yankin Caribbean.

An bayyana manufar tura sojojin - mafi girma zuwa yankin tun lokacin da Amurka ta mamaye Panama a 1989, a matsayin dakatar da kwararar fentanyl da hodar iblis zuwa Amurka.

Daga cikin jiragen akwai jirgin USS Gerald Ford, jirgin ruwan yaƙi mafi girma a duniya. An bayar da rahoton cewa jirage masu saukar ungulu na Amurka sun taso daga cikinsa kafin a kame jirgin dakon mai a kusa da ƙasar Venezuela.

Amurka ta ce an yi amfani da jirgin ruwan da aka sanya wa takunkumi wurin yin dakon mai daga Venezuela da Iran. Venezuela ta bayyana matakin a matsayin wani abu na "fashi da makami a tekun ƙasa da ƙasa".

A cikin ƴan watannin nan, sojojin Amurka sun kuma kai hare-hare sama da 20 a kan jiragen ruwa da ake zargin suna ɗauke da ƙwayoyi inda aka kashe fiye da mutane 80.

Gwamnatin Trump ta yi iƙirarin cewa tana yaƙi ne da waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wadanda ta kuma zarga da gudanar da yaƙin sunƙuru a kan Amurka.

Amurka ta kuma bayyana waɗanda ke cikin jiragen a matsayin 'yan ta'addar narco", amma masana harkokin shari'a sun ce hare-haren ba a kan "manufofin soji na halal ba ne". Harin farko - a ranar 2 ga Satumba ya fi jan hankali musamman domin ba sau biyu aka kai hari kan jirgi guda, inda aka kashe waɗanda suka tsira daga harin na farko a karo na biyu.

Wani tsohon babban mai shigar da ƙara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya shaidawa BBC cewa hare-haren na sojojin Amurka ya faɗa cikin rukunin da ake yi wa laƙabi da 'kai hari kan fararen hula a lokacin zaman lafiya'.

A martanin da ta mayar, Fadar White House ta ce ta ɗauki matakin ne bisa ƙa'idojin yaƙi da makamai domin kare Amurka daga ƴan ta'addan msu "ƙoƙarin cutar da ƙasar mu... suna kuma lalata rayukan Amurkawa".

Ko Venezuela na cika Amurka da miyagun ƙwayoyi?

Ƙwararru a fannin yaƘi da fataucin miyagun Ƙwayoyi sun ce Venezuela ta kasance Ƙasa ce mai Ƙaramin Ƙarfi a harkar safarar muggan Ƙwayoyi a duniya, inda take aiki a matsayin kasa ta hanyar da ake safarar ƙwayoyin da aka sarrafa a wasu ƙasashen.

Makwabciyarta, Colombia, ita ce kan gaba wajen samar da hodar iblis amma akasarinsu ana safarar su ne zuwa Amurka ta wasu hanyoyi, ba ta Venezuela ba.

A cewar wani rahoton hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Amurka daga shekarar 2020, kusan kashi uku cikin huɗu na hodar Iblis da ke isa Amurka ana kiyasin ana safarar su ta tekun Pacific yayin da kaso kaɗan da ke zuwa ta jiragen ruwa masu ɗan karen gudu a cikin Caribbean.

Duk da haka, yawancin hare-haren da Amurka ta kai sun kasance a cikin Caribbean, tare da kaɗan a cikin Pacific.

A watan Satumba, Trump ya gaya wa shugabannin sojojin Amurka cewa jiragen ruwan da aka kai wa hari "an cika su da jakunkuna na farin hoda wanda galibi fentanyl ne da sauran ƙwayoyi".

Fentanyl magani ne da ake sarrafwa wanda ya fi ƙwayar heroin ƙarfi kusan sau 50 kuma ya zama babban maganin da ke da janyo mutuwa ta hanyar shan ƙawaya a Amurka.

Duk da haka, galibin fentanyl da ke yawo a duniya a Mexico ake sarrafa shi, kuma kusan duka na shiga Amurka ne ta iyakarta na yankin kudanci.

Ba a ambaci Venezuela a matsayin ƙasar da ke samar da fentanyl da ake shigo da su cikin Amurka ba a cikin rahoton hukumar ƴaki da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Amurka na shekarar 2025.

Mene ne adadin man da Venezuela ke fitarwa, kuma wa ke saya?

Man fetur dai shi ne babbar hanyar da gwamnatin Maduro ke samun kuɗaɗen shiga daga ƙasashen ƙetare, inda ribar da ake samu daga ɓangaren ke samar da sama da rabin kasafin kuɗin gwamnati.

A halin yanzu tana fitar da kusan ganga 900,000 a kowace rana. China ita ce babbar mai siya mna ƙasa Venezuela.

Sai dai duk da cewa wani ƙiyasi da Amurka ta yi ya nuna cewa Venezuela ce ke da mafi girman arzikin danyen mai a duniya, amma ta ce ba wani amfanin a-zo-a-gani ta ke yi da su ba.

Venezuela ta samar da kashi 0.8 cikin ɗari ne kacal na ɗanyen mai a duniya a shekarar 2023, a cewar Hukumar kula da makamashi ta Amurka (EIA), saboda ƙalubalen fasaha da kasafin kuɗi.

Bayan da ya bayyana cewa an kama tankar, Trump ya shaida wa manema labarai cewa: "Ina tsammanin za mu ajiye man."

A baya dai Amurka ta musanta zargin da Venezuela ke yi na cewa matsin lambar da Amurkan ke yi kan gwamnatin Maduro wani yunƙuri ne na samun damar wawashe albarkatun man fetur na ƙasar.

Ko Amurka na iya kai wa Venezule hari?

Trump ya tabbatar da cewa ya yi magana da Maduro ta wayar tarho a ranar 21 ga Nuwamba.

Yayin da bai bayyana abin da aka fada a hirar ba, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Trump ya bai wa Maduro wa'adin mako guda ya fice daga Venezuela tare da danginsa na kurkusa. An ce Maduro bai amince da wannan tayin da aka yi masa ba.

Kwana guda bayan cikar wa'adin, Trump ya ayyana rufe sararin samaniyar ƙasar ta Venezuela.

Tuni dai Trump ya yi barazanar ɗaukar mataki kan masu safarar muggan ƙwayoyi ƴan ƙasar Venezuela "ta kasa", amma bai bayyana yadda irin wannan aiki zai gudana ba.

Har ila yau, sakatariyar yaɗa labaran Trump ba ta yi watsi da yiwuwar jibge sojojin Amurka a ƙasa a Venezuela ba, ta na mai shaidawa manema labarai cewa "akwai zabin da shugaban ƙasa ke nazari a kai".

Ba ta kuma yi ƙarin bayani kan zaɓin ba amma masu sharhi na soji sun shafe makonni suna nuna cewa yawan sojojin Amurka da aka jibge a yankin Caribbean ya wuce wanda ake buƙata don yaƙi da masu safarra miyagun ƙwayoyi.

Bayan kama jirgin dakon mai, wata majiya ta shaida wa abokin huldar BBC, CBS News, cewa gwamnatin Trump na duba yiwuwar ɗaukar wasu matakai makamantan haka.