Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda zaftare tallafin Birtaniya zai yi illa ga Afirka
- Marubuci, James Landale
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
- Marubuci, Chris Graham
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Gwamnatin Birtaniya ta bayyana shirinta na rage tallafin ƙasashen waje, kuma tallafin karatun yara da kuma ilimin mata a Afirka ne ke fuskantar zaftarewa mafi girma.
A Fabrairu Gwamnatin ta ce za ta zaftare tallafin ƙasashen waje da kaso 40% - daga kaso 0.5% na kuɗin shigar take samu zuwa kashi 0.3% - don ƙara kuɗin da take kashewa kan tsaro zuwa kashi 2.5% sakamakon matsin lamba daga Amurka.
Wani rahoton Ofishin Harkokin Ketare na Birtaniya ya nuna cewa mafi yawan zaftarewar zai faru a Afirka, yayin da rage abin da take kashewa a kan lafiyar mata da tsaftace ruwa zai ƙara hatsarin mutuwa da kamuwa da cututtuka.
Masu ba da tallafi sun soki wannan yunƙuri, inda suka ce zaftarewar za ta shafi mutanen da suka shiga hatsari a faɗin duniya.
Amma gwamnatin ta ce kuɗin da ake kashewa a kan hukumomin bayar da agaji kamar Bankin Duniya - ba za su taɓu ba, ciki har da Haɗakar tallafin riagakafi ta Gavi, kuma ta ce Birtaniya za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa ta bayar da tallafi a yankunan da ake rikici kamar Gaza, Ukraine da kuma Sudan.
Ministan ci gaba Baroness Chapman ta ce: "Mutanen Birtaniya da kuma mutanen da ake tallafawa a faɗin duniya sai sun fi cin moriyar duk wani fam kuma bayanan da muke da su na nuna yadda muka fara samun nasara dangane da hakan."
Gwamnatin ta ce zaftarewar ta bi wani tsari "na tsanaki na yin nazari kan tallafin" da ministar ta samar, wanda ya mayar da hankali kan "ɗabbƙawa, yin abubuwa kan tsari, da kuma kare shirye-shiryen da ake son yi na ba da tallafi da kuma tabbtar da an kawo ƙarshen wasu shirye-shiryen cikin tsanaki."
Ofishin harkokin ƙetare ya ce tallafin da ake bai wa wasu ƙasashe zai ragu kuma ƙungiyoyin ba da tallafi da ake ganin ba sa yin aikinsu yadda ake tsammani za su fuskanci zaftarewar kuɗaɗe. Ba a dai sanar da waɗanne ƙasashe hakan zai shafa ba.
Wannan yunƙurin ya gamu da suka daga Shugabar Kwamitin Kasa da Kasa ta Ci gaba, Sarah Champion, wadda ta ce wasu yanke-yanken za su "cutar da mutane mafi shiga hatsari a duniya."
Monica Harding ta ce zaftare tallafin da Birtaniya ke yi zai "yi mummunar illa ga mutane mafi talauci a duniya".
"Wannan karon farko ne kawai - za mu ga zaftarewa mafi illa shekara mai zuwa," ta ƙara gargaɗi.
Bond, wata haɗaka ta ƙungiyoyin ba da agaji na Birtaniya ta ce akwai shaida ƙarara cewa gwamnatin na son zaftare kuɗin da take kashewa "a kan ilimi a ƙasashen da ke fuskantar rikici kamar South Sudan, Habasha da Somalia, da kuma abin mamaki Yankunan Falasɗinu da kuma Sudan, da gwamnatin ta ce za ta kare".
"Akwai damuwa cewa ƙuɗaɗen da ake kashewa don Afirka, jinsi, ilimi da kuma ayyukan lafiya za su ragu," daraktan tsare-tsare na Bond Gideon Rabinowitz ya ce.
"Yankunan duniya da suka fi shiga hatsari, musamman waɗanda ke fuskantar rikici da kuma mata da yara za su samu koma baya sakamakon matakan da siyasa ta haifar.
"A lokacin da Amurka ta lalata duk wani shirin daidaita jinsi, kamata ya yi Birtaniya ta yi huɓɓasa, ba ta jaya ba."
Unicef, hukumar da ke kula da tallafa wa yara a Majalisar Dinkin Duniya ta ce zaftarewar "za ta haifar da illa maras adadi ga yara da mata" kuma ta kira shirin "wanda babu hikima a cikinsa".
Philip Goodwin, Shugaban Unicef a Birtaniya ya ce: "Muna kira ga gwamnati ta yi sabon shiri da zai bai wa yaran da ke cikin hatsari muhimmanci a shirye-shiryenta na ba da tallafi...
"A kalla kashi 25% na tallafi ya kamata a bayar da muhimmanci ga shirye-shiryen da ke kula da yara don tabbatar da cewa karatun yara da samar musu da abinci mai kyau da kuma kariya a tsare-tsaren ba da tallafi na Birtaniya."
Gidauniyar ba da tallafi ta Street Child ta faɗa wa BBC cewa wasu daga cikin ayyukanta na taimaka wa yara samun ilimi a Sierra Leone, Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo za su zo ƙarshe idan aka yi wannan zaftarewar.
Shugaban gidauniyar Tom Dannatt ya ce ilimi ne babban ginshiki na duniya, kuma rage tallafin abu ne na "rashin jin daɗi kuma maras dabara."
Bayar da tallafi ga ƙasashen ƙetare na ƙara fuskantar suka a shekarun baya-bayan nan, kuma wani minosta ya taba cewa mutane ba sa goyon bayan kashe kuɗi kan tallafi yanzu.
Wata hukuma da ta kuɓuta daga zaftare kuɗaɗe ita ce Bankin Duniya. Ofishin harkokin ƙetare ya tabbatar da cewa Kungiyar Ci gaba ta Kasa da Kasa (IDA) wanda ya ke kula da ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziƙi zai samu fam biliyan 1.98 daga gwamnatin Birtaniya cikin shekaru uku masu zuwa, lamarin da zai sa ƙungiyar ta tallafa wa mjtane biliyan 1.9.
Gwamnatocin Labour na Sir Tony Blair da Gordon Brown sun yi ƙoƙarin ƙara tallafin kasashen ƙetare zuwa kaso 0.7% na adadin kuɗin shigar da gwamnati ke samu.
An cimma wannan buri a 2013 ƙarƙashin gwamnatin haɗaka ta Conservative da Liberal Democat ta David Cameron, kafin a mayar da shi doka a 2015.
Duk da haka, an zaftare kuɗin tallafi zuwa kaso 0.5% na kuɗin shiga a 2021 ƙarƙashin Conservatives, inda aka ɗora alhakin hakan a kan cutar Covid.
Ƙarin bayani daga Will Ross