Hukumar Lafiya ta sa noma a jerin cutukan da aka yi watsi da su

Asalin hoton, World Health Organisation/Web
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da sanarwar shigar da cutar noma a jerin cutukan ƙasashe masu zafi da aka yi watsi da su a duniya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar lafiya ta duniya ta ce matakin amincewar ya zo ne bayan wani taron kwamitin ƙwararrun masu ba da shawara kan cutukan ƙasashe masu zafi da aka yi watsi da su a karo na 17.
Sanarwar ta ce Najeriya ce ta jagoranci ƙoƙarin ganin an sanya cutar noma a jerin cutukan da aka yi watsi da su a cikin ƙasashe masu zafi. Ta ce matakin wani muhimmin ƙuduri ne na faɗaɗa ayyukan lafiya ga al.’ummomi mafiya rauni a duniya.
Noma, in ji ta, wata matsananciyar cuta ce da ke haddasa mutuwar wani sashen baki da fuska, kuma ta fi kama yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki a yankunan da ke cikin tsananin talauci.
Ta ce a kai – a kai cutar takan kai ga mutuwar yaro ɗungurungum, waɗanda suka yi tsawon rai kuma su yi fama da mummunar tawaya.
A cewarta, samun tabbataccen ƙiyasi na alƙaluman masu fama da cutar wani ƙalubale ne saboda saurin ci gaba da cutar ke yi da kuma tsangwamar da ke da alaƙa da ita, abin da ya sa wasu masu fama da cutar da yawa ba sa zuwa a yi musu gwajin lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar noma na farawa ne da haddasa raɗaɗi a leɓɓa, kuma matuƙar ba a yi gaggawar magancewa ba, sai ta bazu cikin sauri ta lalata naman fuska har ma da ƙasusuwa.
An fi samun cutar noma a ƙasashen kudu da hamada, ko da yake hukumar lafiya ta ce ana ba da rahoton samun cutar a Amurka da nahiyar Asiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an sanya noma a jerin cutukan ƙasashe masu zafi da aka yi watsi da su ne da nufin ƙara wayar da kai game da cutar a faɗin duniya da haɓaka bincike da ƙarfafa gwiwar samar da kuɗi da bunƙasa ƙoƙarin taƙaita bazuwar cutar.
A shekara ta 2023 ne gwamnatin Najeriya ta gabatar da roƙon a shigar da cutar cikin jerin cutukan ƙasashe masu zafi da aka yi watsi da su, a madadin ƙasashen ƙungiyar 32.
WHO ta ce roƙon ya samu tallafin bayanai masu tarin yawa da ke nuna lahanin cutar da rabe-rabenta, sannan ta gabatar da shaida da ke nuna cewa cutar ta cika sharuɗɗan shiga jerin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gindaya.
Hukumar ta ce shirye-shiryen da za a ɓullo da su don magance wannan cutar mummunar cuta za su bayar da gudunmawa wajen cimma shirin samar da ayyukan kula da lafiya ga kowa da kowa domin kuwa za su mayar da hankali ga al’ummomin da ba cika samun kulawa ba.











