'Rashin tsaftar baki ne ke haifar da cutar Noma mai kisan yara'

Bayanan bidiyo, Dr Shafi'u Abdul'aziz

Latsa wannan hoton da ke sama domin kallon hirar

Yau ce ranar yaki da cutar Noma mai bata fuskar yara kanana ta Najeriya.

Fatan gwamnatin Najeriya dai shi ne kawo karshen cutar daga nan zuwa shekarar 2030.

Hakan ne ya sa hukumomin lafiya na Najeriya da kungiyar Agaji ta likitocin kasa da kasa ta Medicines San Frontier, MSF ke taro a asibitin kula da cutar ta Noma da ke Sokoto.

Dr Shafi’u Abdul’aziz Gwadabawa, shi ne shugaban asibitin na Noma da ke Sokoto kuma ya yi wa BBC karin bayani dangane da wannan cuta.