Man United za ta dauki Antony kan sama da fam miliyan 80

Manchester United ta amince za ta dauki dan kwallon Ajax dan kasar Brazil, Antony.

Ana cewar United za ta sayi dan wasan kan sama da fam miliyan 80.75 da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 4.25.

Nan gaba kadan dan wasan mai shekara 22 zai je Manchester, domin a auna koshin lafiyarsa, daga nan ya saka hannu kan kunshin yarjejeniya.

Antony zai yi kafada da kafada da Harry Maguire a matakin wadanda ta dauka da dan karen tsada - Paul Pogba ne mafi tsada da United ta saya daga Juventus kan fam miliyan 89 a tarihin kungiyar.

United za ta ziyarci Leicester City a wasan mako na biyar a Premier League ranar Alhamis 1 ga watan Satumba, sai dai Antony zai jira sai ya samu takardar izinin taka leda a Burtaniya kafin ya fara yi wa kungiyar wasa.

Mai buga tamaula daga gaba zai zama na biyar da United ta dauka a bana, bayan mai tsaron baya, Lisandro Martinez da mai wasa daga tsakiya, Casemiro daga Real Madrid da mai tsaron baya, Tyrell Malacia daga Feyenoord da kuma Christian Eriksen wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford.

Sai dai an ci gaba da kalamai kan makomar Cristiano Ronaldo ko zai amince ya karasa kaka daya da ta rage masa ko zai koma inda zai buga Champions League.

United ta yi ta shida a kakar da ta wuce, saboda haka za ta kara a Europa League gasar da Ronaldo bai shirya bugawa ba.