'Rashin karfin soji na kawo mu na cikas a yakin mu da Rasha'

Voldymyr Zelensky

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Zelensky

Shugaba Vlodmyr Zelensky ya amince cewa matsalar rashin karfin soji da Ukraine ke fuskanta ta na dagula kwarin gwiwar dakarunta.

Ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labaru na Faransa watau AFP a ranar jajibirin fara aiwatar da sabuwar dokar da za ta tsawaita wa'adin aikin sojojojin kasar

Shugaba Zelensky ya sake nanata bukatar kasarsa na ganin an ba ta naurar kakabo makamai daga sama yana mai cewa a halin yanzu Ukraine ta na da kashi daya bisa hudu ne kawai kayan yakin da ake bukata.

''A halin yanzu muna bukatar makamin kakabo makamai daga sama akalla guda bakwai, ba na son na bayyana karin abin da mu ke da shi bayan wadanan makaman ba amma na san mu na da kashi 25 cikin 100 na makaman da ake bukata domin kare Ukraine daga hare haren ta sama na sojojin Rasha '' in ji shi.

Sai dai ya soki mambobin kungiyar tsaro ta NATO da suka hana kasarsa amfani da makaman da suka ba ta wajan kai wa yankunan Rasha hari dasu .

Dangane da hare -haren da Rasha ke kai wa a halin yanzu shugaba Zelenksy ya fadawa kamfanin dilancin labaru na AFP cewa ba ya tsamanin Rasha ta na da isasun sojojin da za su kai wa babban birnin kasar watau Kyiv hari , koda yake ya amince da cewa rashin wadattatun sojoji da Kasarsa ke fuskanta na kawo cikas ga kwarin gwiwar sojojin Ukraine

'' Akwai bukatar ganin mun fara amfani da sojojinmu da ke cikin shirin ko ta kwana. Akwai sansanonin da dama da ba bu kowa a cikinsu, a dan haka ya kamata mu dauki mataki domin mu rika sauya wa sojojinmu wuraren fagen daga lokaci zuwa lokaci saboda ta haka ne za a karfafa mu su kwarin gwiwa''

Sai dai Mista Zelensky ya dage da cewa kasarsa za ta amince ne kawai da abinda ya kira zaman lafiya mai adalci yana mai cewa a hanzarin samar da mafita kasashe yamma sun tsinci kansu cikin wani yanayi inda suke fargaba kan shan kayen Rasha ko Ukraine