Zelensky ya kori shugaban dakarun da ke ba shi tsaro kan zargin kitsa kashe shi

..

Asalin hoton, Eugen Kotenko / Ukrinform/Future Publishing via Getty Image

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya kori shugaban dakarun da ke ba shi tsaro bayan an kama mutum biyu daga cikin 'yan tawagar bisa zargin kitsa kashe shugaban.

Serhiy Rud ya jagoranci tawagar da ke bai wa shugaban tsaro tun 2019.

Ba a bayar da wani dalilin da ya sa aka cire shi ba, wanda aka sanar a wani ɗan taƙaitaccen jawabin da shugaban ya yi.

To sai dai tawagar ba shugaban kawai take bai wa tsaro ba har da sauran jiga-jigan jami'an gwamnati da iyalansu a Ukraine.

Ana dai zargin mutanen guda biyu masu muƙamin kanal waɗanda aka ɗaure ranar Talata bisa kasancewarsa jami'in wata ƙungiya wadda akalarta ke ƙarƙashin hukumar tsaro ta Rasha.

Mista Zelensky ya ɗaɗe yana nanata batun maƙarƙashiyar da aka ƙulla na kashe shi, to sai dai bayanan da ke fitowa na baya-bayan nan ya nuna yadda tawagar da ke ba shi tsaro ke cikin batun dumu-dumu.

Makircin ya kuma hari shugaban bayanan sirri na sojojin ƙasar, Kyrylo Budanov da kuma shugaban hukumar tsaro ta ƙasar, Vasyl Maluk.

Mr Malyuk ya faɗi a wannan makon cewa za a aiwatar da shirin ne " a matsayin wata kyauta" ga Putin kafin rantsar da shugaban a matsayin shugaban Rasha a karo na biyar ranar Talata.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar tsaron Ukraine ta ce an tsara yadda makusantan mai tsaron lafiyar shugaba Zalensky za su yi garkuwa da shi daga bisani su kashe shi, inda shi kuma mista Budanov zai fuskanci harin roka da jirage maras matuƙa da kuma gurneti.

Babu wata manuniya da ke alaƙanta Serhiy Rud mai shekara 47 da zarge-zargen duk dai ɗaya daga cikin kanal-kanal ɗin da suke a ɗaure, Andriy Huk ana yi masa kallon wani abokin Serhiy ɗin.

Rahotanni daga Ukraine na cewa sun mutanen biyu sun yi karatu tare a wata makarantar horon soji da ke kan iyaka shekaru da suka gabata.

Manjo Janar Rud ya yi aiki a rundunar sojin Ukraine a shekarunsa na samartaka, sannan ya kwashe shekarunsa na aiki yana mai mayar da hankali kan tsaron ƙasar.

Tun bayan nan ne kuma sojojin Rasha na sama masu amfani da malafar tashi sama suka yi ƙoƙarin sauka a birnin Kyiv domin su kashe shugaba Zelensky da safiyar ranakun farko-farkon watan Fabrairun 2022.

Shugaban na Ukraine ya ce a farkon mamayar Rasha a Ukraine, shi ne "lamba ɗaya" a mutanen da aka so kashewa.

Shugaba Zelensky ya sha yin sauye-sauye ga manyan jami'an tsaron ƙasar Ukraine, sannan a ranar Alhamis ya sake sanar da ɗauke kwamandan rundunar musamman, Kanal Serhiy Lupanchuk daga muƙaminsa wata ɗaya da fara aikin.

An sauya mutumin wanda ya jagoranci tsaron ƙasar Ukraine a shekarun biyun farko na cikakkiyar mamayar Rasha a Ukraine, Janar Valeri Zaluzhnyi a watan Fabrairu.

Yanzu haka an naɗa shi a matsayin jakadan ƙasar ta Ukraine a Burtaniya sannan kuma an ba shi laƙanin "Hero of Ukraine" wato gwarzon ƙasar Ukraine.