Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ba zan kalli bikin naɗin Sarki Charles ba
Miliyoyin mutane ne ake tsammanin za su halarci bikin naɗin sarautar Sarki Charles III da za a yi ranar 6 ga watan Mayu.
Wasu da dama za su yi murna da gagarumin taron, wasu za su yi shagali tare da murna, yayin da wasu kuma za su yi duk mai yiwuwa domin ƙauracewa wannan biki.
BBC ta tattauna da wasu mutane huɗu da suka ce ba za su halarci bikin ba.
‘Ɓata dukiyar al’umma ne’
Oli Silverwood-Cope ba ta da niyyar halartar taron. Ta ce mulkin sarauta, wani tsarin ne da ya tsufa kuma ya kamata a ruguza shi baki ɗaya.
“Ina ganin ɓata dukiyar jama'a ne kawai”, matar mai shekara 51 da ke zaune a Stroud ta faɗa.
A wajen Oli, tsarin ya ci karo da dimokraɗiyya, kamata ya yi masu abin hannu su riƙa jagorantar shi.
“Kuma da wannan tsarin a yanayin da mutane ke fama da yadda za su ci abinci, in ji ta.
A matsayinta na ungozoma, ta ce kamata ya yi a riƙa kashe kuɗaɗen al'umma ta hanyoyin da suka kamata.
“Ba a ƙara mana albashi ba tun 2010. Masarauta na da nata kuɗin amma duk da haka mu da muke biyan haraji mu za mu biya kuɗin da za a yi bikin, ana tsaka da wannan matsalar kuɗi”, in ji ta.
Maimakon kallon bikin ta ce ta gwammace ta tafi asibiti ta taimaka wa mata masu naƙuda.
‘Na gwammace na wuni a kwance ina cin fanke’
Tarek Ahmed ya ce bai damu da naɗin sarautar ba, "da har zai sa na sarayar da lokacina”.
“Na gwammace na kwanta a gado ina cin fanke”, in ji shugaban sashen kasuwanci na Kent mai shekara 21.
Tarek ya ce bai yanke shawara a kan ko zai iya goyon bayan Iyalan Gidan Sarauta ba ko kuma a'a .
“Idan suka sanya dukiyar ƙasa a hanyoyi na kyautata rayuwa. Hakan na nufin za a samu ƙarin kuɗi ga harkoki irin su tsarin inshorar lafiya da kuma ɓangaren ilimi.
Amma saɓanin haka ban san me zan ce ba,” in ji shi.
Wata ƙuri’ar jin ra'ayin jama'a da BBC ta ɗauki nauyi ta nuna gagarumin goyon baya ga tsarin mulukiya, inda kashi 58 cikin 100 suka goyi bayan ci gaba da kasancewar tsarin a kan zaɓaɓɓen shugaba, yayin da kashi 28 cikin 100 suka goyi bayan tsarin zaɓaɓɓen shugaba.
Tarek ya ce ya gwammace ya zauna da iyalinsa a safiyar Asabar da za a yi bikin don kallon sabon fim ɗin Avatar. Watakila ya kalli yadda bikin ya kaya daga baya.
“Wataƙila na kalli yadda aka yi masa naɗin a taƙaice– wanda hakan wani tarihi ne.
'A ganina Charles bai cancanci zama sarki ba'
Joana Firmino ta ce ba ta son Sarki Charles, kuma ba ta son ganin sa a matsayin wanda aka naɗa.
“Ina ganin mutane ba za su zama masu sha’awar abubuwan rayuwarsa ba”, in ji mai kai abinci a Kent 'yar shekara 21.
Joana mai ƙaunar Sarauniya Elizabeth II ce, kuma ta shiga matuƙar “damuwa’’ lokacin da ta mutu.
Damuwarta ita ce Sarki Charles “ba zai iya yanke hukuncin mai kyau ba” saboda matsalar da ke tsakaninsa da matarsa ta farko, Diana, Gimbiyar Wales.
Ta ce ɗansa Yarima William sai ya fi kyau da zama Sarki.
“Idan William za a naɗa, babu abin da zai hana ni kallo. Amma ba zan shafe awanni ina kallo ana naɗa mutumin da ba na so a matsayin sarki ba, kuma na yi imanin bai dace da sarautar ba”, in ji ta.
Maimakon haka, Joana za ta hau jirgi ta tafi Philippines ne don hutawa.
“Ba zan ɓata lokacina ba. Zan huta a cikin yanayin zafi da rana a bakin teku”, in ji ta.
'Aikin Eurovision ne zai min yawa ranar'
Luke Dudley yana aiki ne a matsayin mai kula da nuna Gasar Waƙe-waƙe ta Eurovision Song Contest ya ce yana da wani shiri da zai yi gwaji a kai a kai don haka ba zai iya gani bikin ba.
“Tsarin aikinmu zai zama a ƙure wanda kuma muke mayar da hankali sosai a kai”, in ji shi.
Mai shekara 21 ɗan asalin Manchester yana aiki ne a sashen samar da haske, aikinsa shi ne kunna fitilu ga masu gabatar da shiri.
Luke ba zai ji daɗin rashin kallon ba, “wani lokaci da ba za a manta da shi ba ne a tarihi”.
“Yan'uwa da abokan arziki sun shirya shagali, ba ƙaramin abin kunya ba ne.
Ina son shagali da bukukuwa”, in ji shi.
Duk da yake, Luke ba zai samu damar kallon wannan biki ba, amma ya ce ba kuma zai ji baƙin cikin zamowarsa a wuri irin Eurovision."