Manyan ƙalubalan da ke jiran Rishi Sunak kan dangantar Birtaniya da ƙasashen duniya

Mutumin da zai zama firaministan Birtaniya a ranar Talatar nan zai gaji tarin matsalolin diflomasiyya da kasashen duniya.

Rishi Sunak zai fuskanci matsalolin da suka hada da yakin Ukraine da na karancin makamashi da ya shafi duniya, musamman ma kasarsa.

BBC ta duba ire-iren matsalolin da ke jiran sabon firaminista a fagen dangantakar diflomasiyyar Birtaniya.

Da zarar ya saka kafa cikin gida mai lamba 10 a titin Downing, wanda nan ne fadar firaministan Birtaniyya, shugabannin kasashen duniya za su yi abin da suka saba, wato mika ma Rishi Sunak sakonnin taya murna.

Sai dai takwarorinsa na duniya za su rika tambayar kawunansu, ko wannan jagoran Birtnaiyar na biyar cikin shekara shida zai iya samar da yanayin natsuwar siyasa ga kasar, yayin da jagororin da ya gada suka gaza?

Mista Sunak yayi alkawarin ci gaba da taimaka wa Ukraine da kayan yaki, yayin da ake fargabar Rasha na iya daukan wasu tsauraran matakai.

Sai dai ya yi takatsantsan wajen goyon bayan kara yawan kudaden da Birtaniya ke kashewa a bangaren tsaro, kamar yadda matar da zai gada ta so yi.

Yana kuma cikin masu goyon bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, amma wasu jami'an tarayyar a Brussels na ganin yana da damar warware watsu matsalolin da suka shafi dangantakar kasarsa da nahiyar ta Turai.

A daya bangaren kuwa, wasu shugabannin za su sa ido domin ganin yadda zai tunkari China, kasar da ya ce babbar mai hatsari ce ga tsarin tsaro na duniya.

Sannan wasu a kasasshen kudancin duniya za su sa ido domin ganin ko zai rage yawan kudaden tallafi da Birtaniya ke ba su - yayin da yake kokarin hana tatalin arzikin Birtaniya ci gaba da tangal-tangal.