Trump da Putin za su gana - Kremlin

Hoton Donald Trump da Vladimir Putin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton Donald Trump da Vladimir Putin
    • Marubuci, Rachel Hagan & Laura Gozzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin sun amince su gana da juna a "cikin kwanaki masu zuwa", in ji fadar shugaban ƙasar Rasha.

Wannan ya biyo bayan kalamin Trump na cewa akwai "kyakkyawar fatar" zai gana da shugaban Rasha da na Ukraine "kwanan nan" domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya goyi bayan matakin, sai dai yayin da Putin ke cewa akwai yiwuwar ya gana da Zelensky, amma ya ce da alama ba nan kusa ba.

Wa'adin da shugaba Trump ya shata na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine, ko kuma ya ɗauki tsattsauran mataki zai ƙare ne a ranar Juma'a.

Ganawar Putin da Trump za ta faru ne bayan wata tattaunawar da aka yi tsakanin Putin da jakadan Amurka Steve Witkoff a ranar Laraba.

Witkoff ya kai irin wannan ziyara birnin Moscow kimanin sau huɗu a baya, sai dai babu wani abin a zo a gani da aka cimma.

Lokacin da ya yi jawabi ranar Alhamis, Putin ya ce yana iya yiwuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce za ta karɓi baƙuncin ganawar, wadda za a iya yi a mako mai zuwa.

Ya ce ganawa da Zelensky "ba nan kusa ba" kasancewar ba a cika "ƙa'idojin" da ya gindaya ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya Putin ya taɓa cewa zai gana da Zelensky ne kawai idan aka kai ƙarshe-ƙarshen tattaunawar sulhun. Ukraine da ƙawayenta sun yi watsi da buƙatun da Putin ya gabatar ta kawo ƙarshen yaƙin.

Zelensky ya nuna goyon bayansa ga taron na Outin da Trump, inda ya bayyana cewa an yi ganawa da dama - "duda ɗaya da ta ƙunshi ƙasashe biyu da kuma guda ɗaya ta ƙasashe uku" - kuma ya ƙara da cewa "wajibi ne" Tarayyar Turai ta zama cikin "duk wata tattaunawa."

Ya wallafa wani saƙo a shafin X cewa: "Ukraine ba ta jin shakkar duk wata tattaunawa kuma tana sa ran ita ma Rasha ta zama haka."

Lokacin da aka tambayi Trump a ranar Laraba ko Zelensky da Outin sun amince da wata tattaunawa ta tsawon kwana uku, Trump ya ce "akwai kyakkyawar fata."

A watan da ya gabata, Trump ya shaida wa BBC cewa bayan ziyara huɗu da Witkoff ya kai Moscow a baya, Putin ɗin ya ba shi kunya.

A yanzu Trump na yin magana cikin sassauci, inda ya faɗa wa manema labarai a ranar Laraba ce: "Ba zan ce an cimma nasara ba...mun dade muna ƙoƙari kan wannan lamari. Dubban yara ne suke mutuwa...Ni so nake na kawo ƙarshen lamarin."

A ranar Laraba, fadar shugaban Rasha ta Lremlin ta saki wata sanarwa game da ziyarar Witkoff, inda ta bayyana tattaunawara a matsayin "mai alfanu' tare da cewa dukkanin ɓangarorin biyu sun nuna "kyakkyawar aniya".

A ɓangare ɗaya Zelensky ya ce ya tattauna da Trump game da ziyarar Witkoff, tare da wasu shugabannin ƙasashen Turai.

Shugaban na Ukraine ya sha yin gargaɗin cewa Rasha za ta yi tattaunawar gaskiya ne kawai idan ta fara shiga matsalar kuɗi.

Russian President Vladimir Putin (L) and U.S. Special Envoy for the Middle East Steve Witkoff shake hands before a meeting at the Kremlin in Moscow

Asalin hoton, GAVRIIL GRIGOROV/SPUTNIK/KREMLIN POOL/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da jakadan Amurka Steve Witkoff a ɗaya daga cikin ganawar da suka yi a baya

Yayin da matsi ke ƙaruwa, Trump ya sanya hannu kan takardar umarnin shugaban ƙasa a ranar Laraba domin lafta harajin kashi 25 cikin ɗari kan abubuwan da Indiya ke sayar wa Amurka, bisa yadda take sayen man fetur daga Rasha.

Kafin sake komawa kan mulki a watan Janairu, Trump ya ce zai iya kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine cikin kwana ɗaya.

Har yanzu yaƙin na ci gaba sannan yana tsaurara barazanar da yake yi wa Rasha.

Jerin tattaunawa uku da aka yi tsakanin Ukraine da Rasha a Istanbul sun gaza nemo bakin zaren warware rikicin, kimanin shekara uku da rabi daga lokacin da Rasha ta ƙaddamar da samame a Ukraine.

Har yanzu Ukraine da ƙawayenta na Turai sun ƙi amincewa da sharuɗɗan da Rasha ta gindaya na kawo ƙarshen yaƙin.

Sharuɗɗan da Rasha ta gindaya sun hada da mayar da Ukraine ƙasar ƴar ba-ruwanmu, rage ƙarfin sojinta da watsar da ƙudurinta na shiga ƙungiyar Nato.

Rasha kuma na buƙatar Ukraine ta janye sojojinta daga yankuna huɗu da Rashar ta mamaye a kudu maso gabashin ƙasar.

Haka nan Rash ana son duniya ta amince da yankunan Donetsk da Luhansk da Kherson da Zaporzhzhia da kuma Crimea.

Sauran sharuɗɗan sun hada da haramta wa Ukraine shiga duk wata hadakar soji, taƙaita yawan dakarun sojin Ukraine, amincewa da Rashanci a matsayin harshen hukuma a Ukraine da kuma ɗage takunkuman da aka sa wa Rasha.

Haka nan Rasha ta sha yin watsi da buƙatar Ukraine ta yin ganawa tsakanin Zelensky da Putin.