Trump ya buƙaci Putin ya kawo ƙarshen yaƙin Ukraine ko ya fuskanci takunkumi

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Sarah Rainsford
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Eastern Europe correspondent in Kyiv
- Marubuci, Robert Greenall
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi ga Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ko dai ya kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, ko ya ƙaƙaba masa takunkumai masu tsauri.
Ya bayyana hakan ne a kafar sadarwarsa ta Truth Social cewa, ƙoƙarin da yake yi na kawo ƙarshen yaƙin, yana yi wa Rasha da shugabanta Putin "alfarma" ne.
Trump ya sha bayyanawa a baya cewa zai jagoranci kawo ƙarshen yaƙin domin samar da maslaha a yaƙin.
Putin ya sha nanata cewa a shirye yake ya shiga duk wata tattaunawa da za ta kawo ƙarshen yaƙin, amma yana so Ukraine ta amince da wasu sharuɗɗa, ciki har da jingine yunƙurin shiga ƙungiyar Nato.
Kyiv ta sha faɗa a baya cewa ba za ta bari wasu yankunanta su koma ƙarƙashin Rasha ba, amma yanzu Shugaban Ƙasa Volodymyr Zelensky ya ce zai iya barin wasu yankunan da a yanzu haka aka mamaye su na wani ɗan lokaci.
A ranar Talata, Trump ya bayyana wa manema labarai cewa zai gana da Putin nan da wani ɗan lokaci, sannan akwai yiwuwar zai yi amfani da barazanar ƙaƙaba takunkumi idan shugaban na Rasha ya ƙi amincewa da buƙatar.
Trump ya rubuta cewa. "zan yi wa Rasha, wadda tattalin arzikinta yake taɓarɓarewa a yanzu, da shugabanta alfarma ne," kamar yadda ya rubuta.
"Ku sasanta, sannan ku bar yaƙin nan. Abubuwa na ta ƙara lalacewa ne. Idan ba mu sasanta ba, babu makawa face in ƙaƙaba musu takunkumi da ƙara haraji kan kayayyakin da Rasha ke sayarwa a Amurka, da wasu ƙasashen."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya cigaba da cewa, "ya kamata mu kawo ƙarshen yaƙin nan, wanda tun farko da ni ne shugaban ƙasa ma ba za a fara ba. Lokaci ya yi da za a shiga sulhu a samu maslaha."
Tun a farko, mataimakin jakadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya, Dmitry Polyanskiy ya bayyana wa Reuters cewa za su buƙaci sanin abubuwan da Trump ke buƙata a sasanci domin kawo ƙarshen yaƙin.
Shi ma Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya bayyana a taron tattalin arziki na duniya cewa ana buƙatar aƙalla dakarun wanzar da zaman lafiya 200,000 a cikin yarjejeniyar sasancin.
Sannan ya bayyana wa Bloomberg cewa ƙasarsa za ta buƙaci a sanya sojojin Amurka a cikin batun.
Trump bai bayyana waɗanne irin takunkumin tattalin arzikin zai ƙaƙaba wa Rasha ba, kuma a yaushe. Amma dama akwai wasu takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar.
A yanzu dai abubuwan da Amurka ta fi shigowa da shi daga Rasha shi ne takin zamani mai ɗauke da sinadarin phosphae da sinadarin platinum.
Volker ya shaida wa BBC cewa tattalin arzikin Rasha zai shiga tasku idan Trump ya ƙara zafafa takunkumin tattalin arziki a kan Rasha.

Asalin hoton, EPA
A kafofin sadarwa akwai saɓanin ra'ayi game da yunƙurin na Trump, inda wasu ke ganin takunkumin kaɗai bai wadatar ba.
Amma tambayar da ake yi ita ce shin Putin zai amince ya shiga tattaunawar sasancin?
Fitacciyar ƴar jarida, Margarita Simonyan, wadda take goyon bayan Putin sosai, ta fara bayyana wasu abubuwa da take ganin ya kamata a saka cikin tattaunawar, ciki har da tsagita wuta.
Wannan na nufin a daina yaƙin a yankunan Ukraine guda huɗu da Putin ya sanar da ƙwacewa sama da shekara biyu da suka gabata, ciki har da Zaporizhzhia, wanda yanzu rabinta ke hannun Kyiv.
A tattaunawarsa da BBC a ranar Alhamis, Volker ya ce yana tunanin za a samu nasara, sannan ya ƙara da cewa abun da Amurka ta fi buƙata a yanzu shi ne a dakatar da yaƙin, sannan a hana Putin cigaba da kai hare-hare.
Me Ukraine ta ce game da batun?
Ministan harkokin wajen Ukraine ya ce ƙasarsa na maraba da saƙon Shugaban Ƙasa Donald Trump, inda ya yi barazanar ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumi da ruɓanya haraji idan har Putin bai kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar ta Ukraine ba.
"Lallai muna maraba da wannan saƙon na Shugaba Trump," in ji Andriy Sybiha, a lokacin da yake jawabi a taron tattalin arziki na duniya da ake yi a birnin Davos.
"Mun yi amannar cewa Trump zai samu nasara," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa yana fata Ukraine za ta "kawo sauyi a yanayin amfani da diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin tare da tsara hanyoyin samar da zaman lafiya mai ɗorewa."
Tun da farko, ƙasar Ukraine ta yaba wa Trump, sannan ta ce, "mun shirya shiga tattaunawa domin samar da matsaya mai kyau."











