Putin ya fita daga raina - Trump

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Gary O'Donoghue
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief North America Correspondent
- Aiko rahoto daga, Washington
- Lokacin karatu: Minti 2
Donald Trump ya ce Vladmir Putin na Rasha ya sare masa, kamar yadda ya shaida wa BBC a tattauna ta musamman ta wayar tarho.
Shugaban na Amurka ya amsa tambaya lokacin da aka tambaye shi ko ya yarda da shugaban Rasha, ya yi martani cewa: ''Babu wanda na yarda da shi.''
Trump na waɗannan bayanai ne sa'o'i bayan ya sanar da shirin aike makamai ga Ukraine da gargaɗin lafta haraji kan Rasha muddin taƙi cimma yarjejeniyar tsagaita wuta nan da kwanaki 50.
A tattaunawar da ta taɓo abubuwa daban-daban daga ofishinsa, shugaban ya nuna yana tare da Nato, wanda a baya yake suka, tare da bayyana cikakken goyon-bayan ayyukanta na tsaro.
Shugaban ya bada damar tattaunawa da shi na mintina 20, bayan BBC ta tuntube shi domin tsokaci kan cika shekara guda da kokarin hallaka shi a Butler da ke, Pennsylvania.
Da aka tambaye shi kan ko tsallake rijiya da baya a harin da aka kai masa ya sauya masa rayuwa, Trump ya ce baya son ya rinka yawan tuna wa da batun.
"Ya ce ba na son tunanin ko lamarin ya sauya ni, "In ji Trump. Zama ana nazari a kai, a cewarsa "na iya sauya mun rayuwa."
Bayan ganawa da shugaban Nato Mark Rutte a fadar White House, shugaban ya yi amfani da damar da ya samu wajen bayanai da nuna takaicinsa da shugaban Rasha.
Trump ya ce ya yi tunanin za a cimma yarjejeniya a kan teburi da Rasha amma sai gashi an yi zama hudu ba a daidaita ba.
A lokacin da BBC ta yi masa tambaya idan hakan na nufi ya fita batun Putin, shugaban ya yi martani: ''Ina takaici kuma ya sare mun, amma dai ban kammala da shi ba. Amma dai ya ɓata mun rai."
Da aka tambaye shi kan ko wace dabara zai yi amfani da ita wajen tursasa wa Vladimir Putin ya ''daina zub da jini'' shugaban na Amurka ya ce, "Muna kokarin cimma hakan."
"Za mu samu fahimtar juna, iya abin da zance kenan, kuma ina ganin muna hanyar cimma hakan,' kuma shi da kansa ba zai sake rusa gini a Kyiv ba."

Asalin hoton, Getty Images
Sannan tattaunawar ta ci gaba a kan Nato, wanda a baya shugaba Trump ya sha caccaka a matsayin ''mara amfani''.
Da aka tambaye shi kan ko har yanzu yana kan wannan batu, ya ce, "A'a. Ina ganin a yanzu Nato ayyukanta sun inganta," saboda hadakar, na ''biyan hakokin da ke wuyanta''.
Ya ce yana da yaƙinin hada hannu tare, saboda hakan na nufin kananan ƙasashe na iya kare kansu daga manyan ƙasashe.
An tambaye Trump kan makomar Burtaniya a duniya, sai ya ce yana ganin ''kasa ce mai kyau'', kuma yana da kadarori a ƙasar".
Ya ce yana da anniyar kai ziyara a karo na biyu Burtaniya cikin watan Satumba wannan shekara.
Da aka masa tambaya me yake son cimma a ziyarar, Trump ya ce, "Ina son na samu lokaci mai armashi da girmama Sarki Charles, saboda mutumin kirki ne."











