Masana kimiyya na rububin samar da kwamfuta 'mai rai'

Zoe Kleinman take kallon wani faranti a ɗakin gwaji
Bayanan hoto, Abubuwan da ake haɗa kwamfuta mai tunanin ɗan'adam da su
    • Marubuci, Zoe Kleinman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan Fasaha
  • Lokacin karatu: Minti 3

Abu ne da ka iya zama almara, amma dai masana kimiyya na samun cigaba sosai wajen ƙirƙirar na'urar kwamfuta ta hanyar amfani da ƙwayoyin halitta na ɗan'adam.

Barka da zuwa duniyar kwamfuta mai tunani irin na ɗan'adam - wato biocomputing a Turance.

Daga cikin na gaba-gaba a wannan fanni akwai rukunin masana kimiyya a ƙasar Switzerland, waɗanda na haɗu da su.

Suna fatan wata rana za a samu cibiyoyi cike da kwamfutoci "masu rai" da za su taimaka wa ɓangaren ƙirƙirarriyar basira ta AI.

Wannan ne burin Dr Fred Jordan, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa cibiyar FinalSpark, wanda na ziyarta.

Mun fi sabawa da maganar kayan aiki (hardware) da kuma manhaja (software) a yanzu idan ana maganar kwamfuta.

Dr Jordan da abokan aikinsa na amfani da kalmar "wetware" wajen bayyana abin da suke aikin ƙirƙirowa.

Dr Jordan ya ce mutane da yawa na ganin maganar kwamfuta mai tunani irin na ɗan'adam kamar almara ce.

"A ɓangaren ƙirƙirarrun labarai na kimiyya, mutane sun sha ganin irin wannan yanayi tsawon lokaci," in ji shi.

Domin samun nasarar, FinalSpark kan fara ne da samo ƙwayoyin halitta wato cells daga jikin fatar ɗan'adam, wanda suke saya daga asibiti a Japan. Amma waɗanda suke bayar da kyautar ƙwayoyin ba su yarda a bayyana sunayensu.

"Akwai mutane da yawa da ke kawo kan su domin ba mu sadakar ƙwayoyin," a cewar Dr Jordan.

"Amma mukan zaɓi ƙwayoyin komai-da-ruwanka ne kawai da masu bayar da sadakar ke bayarwa, saboda ingancin ƙwayoyin na da tasiri matuƙa."

Hoton Dr Flora Brozzi kenan take aiki a cibiyar gwaji ta FinalSpark da ke Switzerland
Bayanan hoto, Masana kimiyya a Vevey, Switzerland na ƙirƙirar kwamfuta mai tunani irin na ɗan'adam daga ƙwayoyin halittar mutane
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ɗakin gwajin, masaniyar ilimin halitta Dr Flora Brozzi ta ba ni wani faranti ɗauke da wasu fararen ƙwallaye ƙanana.

Kowane ƙwallo daga ciki ƙarami ne sosai, wanda aka ƙirƙira daga ƙwayoyin halittar ɗan'adam, a matsayin ƙwaƙwalwar da za ta dinga tafiyar da ayyukan kwamfutar. Waɗannan su ake “organoids” wato gaɓoɓi.

Ba su kama ƙafar zama daidai da fasahar ƙwaƙwalwar ɗan'adam ba, amma suna kamanceceniya a siffa.

Bayan yin gwajin da zai ɗauki watanni, za a haɗa organoids (gaɓoɓi) da faifan lantarki wanda zai ba da damar madannan kwamfutar su yi aikin da aka nemi su yi.

Za a gane kwamfutar na aiki ko kuma a'a ta hanyar maƙala game-garin kwafuta a jikin na'urar gwajin.

Abu ne mai sauƙi. Za a danna maɓalli wanda shi kuma zai aika saƙon latironi zuwa farantan latironin. Idan ya yi aiki za a ga ɗan sauyi a jikin allon kwamfutar.

Na daddanna maɓalli, amma kawai sai ta daina aiki.

Da na tambayi me ya faru, Dr Jordan ya ce har yanzu akwai abubuwa da yawa da su ma ba su fahimta ba.

"Haka ma abin yake ga ƙirƙirarriyar basira," in ji shi.

"Za ka ba ta umarni domin samun bayani kan wani abu mai amfani.

"Misali, idan aka nuna mata hoton mage, za ka so ta yi bayani cewa mage ce," kamar yadda ya bayyana.

Hidimar samar da kwamfuta mai tunani irin na ɗan'am

Ba FinalSpark ne kaɗai masana kimiyya da ke aiki kan kamfutar mai tunani irin na ɗan'adam ba.

Kamfanin Cortical Lab a Australia ya sanar a 2022 cewa ya yi nasarar ƙirƙirar ƙwaƙwalwar kwamfutar da ta byar da damar buga wasan game mai suna Pong.

A Amurka, masu binicke a Jami'ar Johns Hopkins ma na gina "ƙananan ƙwaƙwale" domin gane yadda suke sarrafa bayanai - amma a fannin haɗa ƙwayoyin maganin matsalar ƙwaƙwalwa kamar Alzheimer's da kuma galahanga.

Ana fatan ƙirƙirarriyar basira ta AI za ta taimaka wajen samun nasara a wannan fanni nan gaba kaɗan.

Amma dai a yanzu, Dr Lena Smirnova da ke jagorantar binciken na Jami'ar Johns Hopkins, ta ce harkar wetware na da ƙayatarwa amma kuma har yanzu lamarin yana farko-farko.

"Kwamfutoci na biocomputer taimakawa ya kamata su yi - ba maye gurbin sauran ba," a cewarta.