Watakil Fernandes ya koma Saudiya, Arsenal za ta hana Besiktas zawarcin Trossard

Asalin hoton, PA Media
Dan wasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes, mai shekara 30, ya yi watsi da tayin da wasu kungiyoyin uku na Saudiyya suka yi masa a wannan bazara, inda dan wasan kasar Portugal ya zabi ci gaba da zama a Old Trafford. Sai dai kyaftin din United bai dakatar da tattaunawa da Saudiyya ba saboda wakilan kungiyoyin har yanzu suna da niyyar siyan shi a bazarar badi (Talksport), external
Bayern Munich na tunanin ko ta dauko dan wasan gefe na Liverpool Cody Gakpo a lokacin bazara. Dan wasan kasar Netherlands na cikin 'yan wasa masu kai hari da kungiyar ta Jamus ke sha'awa, wadda ta dauki tsohon abokin wasansa Luis Diaz. (Sky Sports), external
Chelsea ta samu tayin fam miliyan 59.5 daga kungiyar Al-Qadsiah ta Saudi Pro league kan dan wasan tsakiya na Brazil Andrey Santos. Dan wasan mai shekara 21 ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro Strasbourg da ke Faransa. (Mirror), external
Morgan Rogers ya fito a matsayin dan wasan da Tottenham ke son daukowa a watan Janairu. Kocin Spurs Thomas Frank yana goyon bayan dan wasan tsakiyar Aston Villa, mai shekara 23, wanda a halin yanzu yake taka leda a tawagar kwallon kafa ta Ingila. (Teamtalk), external
Bournemouth na tattaunawa da Olympiakos kan yarjejeniyar barin dan wasan Ingila Zain Silcott-Duberry mai shekaru 20 ya koma kungiyar ta Girka. (Sky Sports), external
Juventus na son daukar dan wasan tsakiyar Real Madrid, Dani Cebellos a watan Janairu. Tun a bazara ne kungiyar ta kasar Italiya ke zawarcin dan wasan kasar Sfaniya, mai shekara 29 amma ba su cimma matsaya ba. (JuveFC), external
Arsenal ba ta anniyar barin dan wasan Belgium Leandro Trossard ficewa daga kungiyar. An danganta dan wasan mai shekaru 30 da komawa Besiktas amma ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Arsenal a watan da ya gabata. (Fabrizio Romano), external
Dan wasan bayan Liverpool Giovanni Leoni, mai shekara 18, ya ki amincewa da komawa Newcastle a lokacin da yake Parma duk da cewa Magpies ta nuna cewa za ta ba kungiyar ta Italiya kudi fiye da na Liverpool don siyan shi. (Gazzetta di Parma via Football Italia), external
Manyan 'yan wasa a dakin sanya tufafi na Manchester United sun nuna damuwa kan halin da fanin tsaron gidan kungiyar ya ke ciki wanda ya bai wa Trabzonspor damar neman a ba ta aro dan wasan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29.(Star), external
Tsohon dan wasan Liverpool da Bayern Munich da Sfaniya Thiago Alcantara mai shekara 34, ya amince ya sake komawa Barcelona a matsayin daya daga cikin masu taimakawa kocin kungiyar Hansi Flick (Marca - in Spanish), external














