Ƙungiyoyin Saudiyya na zawarcin Maguire, Liverpool na son Michael Olise

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin Saudiyya na zawarcin dan wasan Manchester United Harry Maguire, Liverpool na zawarcin Michael Olise a matsayin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah, kana Manchester United ta kasa daukar Conor Gallagher.
Kungiyoyin Saudiyya na zawarcin dan wasan baya na Manchester United da Ingila Harry Maguire, mai shekara 32, kuma zai yi tunanin tashi daga kungiyar ne a karshen kakar wasa ta bana. (Sun)
Shugaban Crystal Palace Steve Parish ya tattauna da dan wasan Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, da danginsa bayan da ya soke cinikinsa a kan £35m zuwa Liverpool. (Mirror)
Liverpool na shirin zawarcin Guehi a watan Janairu, kuma suna duban dan wasan gaban Bayern Munich da Faransa, Michael Olise, mai shekara 23 a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 33.(Mail)
Bayern Munich ta shiga zawarcin Guehi, yayin da Real Madrid da Barcelona ke sa ido kansa (Express)
Dan wasan Liverpool da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 26, ya ce Bayern Munich ta neme shi kafin kulob din na Jamus ya sayi dan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, daga Reds maimakon. (ESPN)
Manchester United ta yi kokarin siyan dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 25, daga Atletico Madrid a cikin kwanaki biyun karshe na kasuwar musayar yan wasan kwallon kafa ta Turai, amma kulob din na Sipaniya ya yi watsi da bukatar. (Fabrizio Romano)
Liverpool, da Tottenham da Newcastle duk suna tunanin zawarcin dan wasan baya na Brighton da Netherlands Jan Paul van Hecke, mai shekara 25, a 2026. (Teamtalk)
Juventus na duba yiwuwar tsawaita kwantiragin Dusan Vlahovic a kulob din wanda zai kare a bazara mai zuwa. Dan wasan gaban Serbia din mai shekara 25, zai iya kulla yarjejeniya da wani kulob daga watan Janairu. (La Gazzetta dello Sport)
Manchester United za ta saurari tayin golan Turkiyya Altay Bayindir, mai shekara 27, da dan wasan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29, daga kungiyoyin Saudiyya da Turkiyya. (Sun)
Monaco ta ki amincewa da matakin AC Milan na neman dan wasan bayan Jamus Thilo Kehrer, mai shekara 28, a kwanakin karshe na kasuwar hada hadar yan wasa. (Fabrizio Romano)











