Man United na neman sake ɗaukar Welbeck, Guehi ya fusata da rashin komawarsa Liverpool

Danny Welbeck

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Danny Welbeck
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan baya na Crystal Palace Marc Guehi ba ya sha'awar sanya hannu kan sabon kwantiragi bayan dakile komawarsa Liverpool, har yanzu Manchester United na shirin siyar da golanta Andre Onana, dan wasan tsakiyar Tottenham Yves Bissouma zai tafi.

Marc Guehi bai ji dadin yadda Crystal Palace ta dakile cinikinsa a kan fam miliyan 35 zuwa Liverpool ba, biyo bayan barazanar da mai horar da kungiyar Oliver Glasner ya yi ta yin murabus idan kungiyar ta sayar da dan wasan mai shekara 25. (Guardian)

Da a ce Liverpool ta taya Guehi a kan fan miliyan 55 to da Crystal Palace ta ci gaba da cinikinsa, ko da yake tana iya fuskantar hamayya daga Real Madrid wadda ke son daukarsa a kyauta. (Telegraph)

Guehi, wanda ke cikin shekararsa ta karshe a Crystal Palace, zai yi watsi da duk wani tayin sabon kwantaragi yayin da yake shirin barin kungiyar a kyauta a bazara. (Times)

Manchester United ta nemi ta sake siyan Danny Welbeck daga Brighton a wannan bazarar (Sports)

Har yanzu Manchester United na shirin siyar da golanta dan Kamaru Andre Onana mai shekaru 29 a cikin kwanaki masu zuwa (Team Talk)

Nottingham Forest na shirin dauko dan wasan tsakiya na Ingila Chinaza Nwosu, mai shekara 17, daga West Ham, bayan samun nasara a wasu manyan kungiyoyi. (Fabrizio Romano)

Tottenham na ci gaba da fatan siyar da dan wasan tsakiyar Mali Yves Bissouma, mai shekara 29, ga duk wata kungiya wadda har yanzu kasuwar musayar yan wasanta ke ci har yanzu. (The I)

Aston Villa ta yi farin cikin ci gaba da zama da Emiliano Martinez a kakar wasa ta bana, bayan rashin nasarar komawarsa Manchester United. kuma golan Argentinan mai shekaru 33 ba ya sha'awar shiga gasar Super Lig ta Turkiyya. (Fabrizio Romano)

Zakarun Scotland Celtic sun tuntubi Patrick Bamford, wanda ya bar Leeds United a wannan watan, a yunkurin sayo dan wasan Ingila mai shekaru 31 a kyauta. (Herald)