Tottenham ta maida hankali kan Akanji, Chelsea na son ta sayi Lopez daga Barcelona

Manuel Akanji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manuel Akanji
Lokacin karatu: Minti 3

Tottenham Hotspur ce ke kan gaba a zawarcin dan wasan bayan Manchester City Manuel Akanji, mai shekara 30, yayin da take neman doke AC Milan da Crystal Palace.(Gazetta Dello Sport - in Italian), external

Kocin Barcelona Hansi Flick ya ce yana da yakinin cewa dan wasan tsakiya mai shekara 22 Fermin Lopez, wanda ya sau biyu ya yi wa Sfaniya wasa ba zai bar kungiyar ba a wannan kasuwar musayyar 'yan wasa duk da ana alakanta shi da Chelsea.(ESPN), external

Sai dai Chelsea a shirye take ta yi wa Barcelona tayin yuro miliyan 90 kan Lopez (Mundo Deportivo - in Spanish), external

West Ham ta bi sahun kungiyoyin da ke son daukar Fabio Vieira daga Arsenal, sai dai Stuttgart da wata babbar kungiya ta Bundesliga na sha'awar dan wasan tsakiya na Portugal mai shekara 25.(Sky Sports Germany), external

Dan wasan bayan Manchester United da Morocco Noussair Mazraoui mai shekara 27, ya bayana a matsayin dan wasan da Juventus ke son ta dauka. (Gazetta Dello Sport - in Italian), external

RB Leipzig na son ta dauko dan wasan tsakiya na Liverpool da Ingila a tawagar 'yan wasa masu shekaru 21, Harvey Elliot mai shekara 22 a matsayin wanda zai maye gurbin Xavi Simons ,sai dai kungiyar ta Jamus ba ta amince da farashin da Reds ta sanya kan dan wasan ba (ESPN), external

Watakila Liverpool ta maida hankali kan dan wasan tsakiyar Aston Villa da Ingila Morgan Rogers mai shekara 23, idan ta cefanar da Elliott (Football Insider), external

Dan wasan mai kai hari na kasar Brazil Rodrygo, mai shekara 24, zai ci gaba da taka leda a Real Madrid a wannan kasuwar musayar 'yan wasa duk da cewa kungiyoyi da dama da suka hada da Liverpool da Arsenal na zawarcinsa.(Marca - in Spanish), external

Leeds United ta ci gaba da zawarcin dan wasan tsakiyar Leicester City da Morocco Bilal El Khannouss mai shekara 23 bayan yunkurinsu na neman Facundo Buonanotte na Brighton ya ruguje. (The Athletic - subscription required), external

Chelsea na tunanin cika sharudan yarjejeniyar sakin dan wasan Braga, Roger Fernandes, mai shekara 19, kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara. (A Bola - in Portuguese), external

Aston Villa na duba yuwuwar daukar dan wasan bayan Osasuna da Kamaru Enzo Boyomo mai shekara 23 a kan fan miliyan 21.25 ya yin da kocin kungiyar Unai Emery ke kokarin kara inganta 'yan wasansa masu tsaron bayar.(The Telegraph - subscription required), external

Kungiyoyi biyu na gasar Premier suna zawarcin dan wasan gaban Sevilla da Belgium Dodi Lukebakio, mai shekara 27, inda kungiyar ta Sfaniya ta shirya tsaf wajan karbar tayin kungiyoyi kafin karshen wa'adi musayar'yan wasa. (Fabrizio Romano)