Mainoo na son ya bar Manchester United, Tottenham da Chelsea na zawarcin Simons

Asalin hoton, Getty Images
Kobbie Mainoo ya shaida wa Manchester United cewa yana son ya tafi wata kungiya a matsayin aro amma Man U ta na son dan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20 ya ci gaba da taka leda a wurinta.(Athletic - subscription required, external)
Wolves a shirye ta ke ta yi watsi da tayin fan miliyan 60 na Newcastle karo na uku kan dan wasa mai kai hari na Norway Jorgen Strand Larsen mai shekara 25 inda ta dage da cewa ba za ta cefanar da dan wasan a kasuwar musayar 'yan wasa ba. (Telegraph - subscription required, external)
Tottenham na gab da kulla yarjejeniya fan miliyan 60 da RB Leipzig kan dan wasan tsakiyar Netherlands Xavi Simons, mai shekara 22, bayan da suka yi yunkurin takawa Chelsea birki kan zawarcin da take yi dan wasan .(Telegraph - subscription required, external)
Bayan amincewa da farashin dan wasan mai kai hari na Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 21, Chelsea kuma ta shirya kai tayin fan miliyan 60 kan Simons na Leipzig.(Metro), external
Tottenham ta tuntubi Manchester City game da komawar dan wasan bayan Netherlands Nathan Ake mai shekara 30. (Givemesport), external
Aston Villa na dab da daukar dan wasan gaba, Marco Asensio kan kwantiragin din -din daga Paris St-Germain bayan dan wasan mai shekaru 29 dan kasar Sifaniya ya taka rawar gani yayin da yake zaman aro a Villa Park a bara.(L'Equipe - in French), external
Raunin da Romelu Lukaku yake fama da shi, ya sa zakarun Italiya watau Napoli ta shirya tsaf don daukar dan wasan gaban Manchester United Rasmus Hojlund mai shekaru 22 a matsayin aro, tare da wata yarjejeniya ta baki da aka cimma da dan wasan na Denmark.(Gianluca DiMarzio), external
Dan wasan Manchester United, mai shekara 26, dan kasar Holland Tyrell Malacia na shirin komawa Elche a matsayin aro na tsawon kaka daya bayan ya zabi kungiyar ta La Liga fiye da Lille.(Voetbal International - in Dutch, external)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kungiyar Cremonese wadda ta samu matsayi a Seria A tana zawarcin Jamie Vardy, mai shekara 38, tsohon dan wasa mai kai hari na Ingila wanda ba shi da kulob tun bayan barin Leicester City a karshen kakar wasan da ta wuce.(Times - subscription required, external)
Tsohon abokin wasan Vardy na Leicester kuma dan kasar Faransa N'Golo Kante na shirin komawa Turai bayan tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea mai shekaru 34 bayan da kungiyar Al-Ittihad na kasar Saudi Pro League ta yi wa AS Monaco da Paris FC tayin dan wasan(L'Equipe - in French), external
Crystal Palace ta soma shirye shiryen rabuwa da kyaftin dinta Marc Guehi mai shekara 25, wanda zai koma taka leda a Liverpool kafin wa'adin da ranar litinin kuma suna son fan miliyan 45 akan dan wasan(Express), external
Burnley na son dan wasan Benfica Florentino Luis mai shekara 26, sai dai Marseille da Roma su ma sun nu sha'awar sayan dan wasan bayan Portugal a wannan bazara. (Sky Sports, external)
Rangers ta tuntubi Everton a kan ta bata aron dan wasa mai kai hari na Portugal Youssef Chermiti mai shekara 21 (Sky Sports, external)
Za a duba lafiyar dan wasa mai tsaron bayan Paris FC kuma tsohon dan wasan Faransa Dimitri Colau mai shekara 19 a West Ham a ranar Asabar kafin ya sa hannu kan kwataragin shekaru hudu da Hammers.(Footmercato - in French, external)














