Isak ya matsu ya bar Newcastle, Man Utd na fatan daidaitawa da Lammens

Alexander Isak

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan Sweden Alexander Isak mai shekara 25, ya faɗa wa Newcastle yana son rabuwa da ita zuwa Liverpool duk da shiga tsakani da shugaban ƙungiyar, Yasir Al-Rumayyan da kuma tattaunawa da ɗaya daga cikin masu ƙungiyar, Jamie Reuben. (Telegraph - subscription required, external)

Manchester United ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Real Betis mai shekara 25, Antony wanda za ta ba shi damar ya je zaman aro kafin daga bisani a yanke hukuncin zaman dindindin. (Telegraph - subscription required, external)

Manchester United na kuma fatan nasarar saye mai tsaron raga, Senne Lammens daga Royal Antwerp kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa. (Telegraph - subscription required, external)

Real Madrid da Atletico Madrid na bibbiyar ɗan wasan Manchester United da Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20. (Mail, external)

Mainoo ya kuma kasance wanda Fulham ke hari, da kuma ɗan wasan Arsenal mai shekara 25, Reiss Nelson. (Teamtalk, external)

Porto na gab da cimma yarjejeniya zaman aro da ɗan wasan Arsenal mai shekara 25 daga Poland, Jakub Kiwior. (Sky Sports, external)

Crystal Palace na shirin shiga tattaunawa da ɗan wasan Liverpool Harvey Elliott mai shekara 22, yayin da suke kokarin neman wanda zai maye gurbin, Eberechi Eze mai shekara 27, da ya koma Arsenal. (Football Insider, external)

Bayer Leverkusen da Galatasaray na kalubalantar Crystal Palace a cinikin ɗan wasan Manchester City da Switzerland, Manuel Akanji. (Independent)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Brentford na son ɗauko ɗan wasan Borussia Dortmund mai shekara 22 daga Jamus, Max Beier, yayin da ita kuma ƙungiyar ta Bundesliga ke harin ɗan wasan Portugal, Fabio Silva mai shekara 23 daga Wolves. (Sky Sports, external)

Roma ta tattauna da Chelsea da wakilan Tyrique George kan saye ɗan wasan Ingila mai shekara 19. (Gianluca di Marzio - in Italian, external)

Alejandro Garnacho ya yi watsi da tayin Saudiyya sa'o'i 48 da suka gabata yayin da ake tattaunawa tsakanin Manchester United da Chelsea kan ɗan wasan mai shekara 21 daga Argentina. (Fabrizio Romano, external)

West Ham na gab da cimma yarjejeniyar fam miliyan 17.3 da ɗan wasan AS Monaco, Soungoutou Magassa. (Guardian, external)

Ana tunanin ɗan wasan Nottingham Forest da Ivory Coast, Ibrahim Sangare mai shekara 27, ya je West Ham, yayin da ƙungiyar ke nazari kan Junior Mwanga mai shekara 22, da mai taka leda a Middlesbrough Hayden Hackney, ɗan shekara 23. (Sky Sports, external)

Nottingham Forest ta gabatar da tayin fam miliyan 10 kan ɗan wasan Italiya, Nicolo Savona, mai shekara 22, amma Juventus ta yi fatali da tayin. (Gianluca di Marzio - in Italian, external)

Crystal Palace ta cimma yarjejeniya da Villarreal kan ɗan wasanta na Sifaniya mai shekara 22, Yeremy Pino kan £26m. (AS - in Spanish, external)

Ɗan wasan tsakiya a Liverpool James McConnell mai shekara 20, zai je Ajax. (Athletic - subscription required, external)