Liverpool da Man City za su fuskanci Real Madrid a Champions League

Kylian Mbappe da Vinicius Junior

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kylian Mbappe da Vinicius Junior na cikin 'yanwasan da suka fi taka rawar gani a Real Madrid
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool da Manchester City za su fuskanci zakarun gasar Champions League karo 15 Real Madrid a matakin rukuni, yayin da Tottenham da Newcastle za su fafata da mai riƙe da kofin Paris Saint-German.

An ƙaddamar da sabon jadawalin gasar mai tawaga 36 ne a bara, wadda a yanzu za ta ƙunshi ƙungiyoyin Premier League shida karon farko a tarihi. Sai dai ba za su kara da juna ba har sai an kai zagayen 'yan 16.

Ban da Real da za ta fuskanta, Liverpool za kuma ta gwabza da Atletico Madrid da Inter Milan.

Ita kuma Man City za ta buga da ƙungiyoyin Napoli da Borussia Dortmund.

Zakarun gasar Club World Cup Chelsea za ta ɓarje gumi da Bayern Munich, yayin da ita ma Arsenal za ta take wasa da Bayern ɗin.

Daga cikin kulob-kulob ɗin da Newcastle za ta fuskanta akwai Barcelona, yayin da Tottenham za ta buga da Monaco da Dortmund.

Za a fara buga gasar a ranar Talata 16 ga watan Satumba, amma sai nan gaba za a bayyana cikakken jadawalin buga wasannin na gasar 2025-26.

Za a buga wasan ƙarshe na gasar a birnin Budapest na ƙasar Hungary.

Tawagogin da ƙungiyoyin Premier za su kara da su

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Liverpool: Real Madrid (home), Inter Milan (away), Atletico Madrid (home), Eintracht Frankfurt (away), PSV Eindhoven (home), Marseille (away), Qarabag (home) and Galatasaray (away).

Manchester City: Borussia Dortmund (home), Real Madrid (away), Bayer Leverkusen (home), Villarreal (away), Napoli (home), Bodo/Glimt (away), Galatasaray (home) and Monaco (away).

Chelsea: Barcelona (home), Bayern Munich (away), Benfica (home), Atalanta (away), Ajax (home), Napoli (away), Pafos (home) and Qarabag (away)

Arsenal: Bayern Munich (home), Inter Milan (away), Atletico Madrid (away), Club Brugge (home), Olympiacos (away), Slavia Prague (home), Kairat Almaty (away) and Athletic Bilbao (home).

Tottenham: Borussia Dortmund (home), Paris St-Germain (away), Villarreal (home), Eintracht Frankfurt (away), Slavia Prague (home), Bodo/Glimt (away) Copenhagen (home) and Monaco (away).

Newcastle: Barcelona (home), Paris St-Germain (away), Benfica (home), Bayer Leverkusen (away), PSV (home), Marseille (away), Athletic Bilbao (home) and Union SG (away).