Chelsea na dab da mallakar Garnacho, AC Milan na farautar Nkunku

Alejandro Garnacho

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na gab da amincewa da yarjejeniyar fam miliyan 35 zuwa 40 kan sayar da ɗan wasanta na Argentina mai shekara 21, Alejandro Garnacho ga Chelsea. (Telegraph - subscription required, external)

AC Milan ta shiga fafutikar sayen ɗan wasan gaba a Chelsea, Christopher Nkunku, kuma ɗan wasan mai shekara 27 daga Faransa ya nuna sha'awar son zuwa ƙungiyar Bundesliga ta Bayern Munich ko RB Leipzig. (Athletic - subscription required, external)

Ana saran Newcastle ta inganta tayinta zuwa fam miliyan 60 kan ɗan wasan gaba Jorgen Strand Larsen bayan Wolves ta yi watsi da tayin fam miliyan 50 zuwa 55 kan ɗan wasan mai shekara 25 daga Norway. (Sky Sports, external)

Mai tsaron raga a Paris St-Germain, Gianluigi Donnarumma bai cire rai kan komawa Manchester City ba, musamman a wannan lokacin da ake ganin ɗan wasansu Ederson, zai tafi. (Sky Sports, external)

Babu tattaunaa tsakanin ƙungiyar Saudiyya Al-Nassr da Manchester City kan Ederson, amma Galatasaray na son saye ɗan wasan mai tsaron baya. (Fabrizio Romano, external)

A gefe guda, Manchester City ta sanarwa Tottenham cewa ba ta da niyyar sayar da ɗan wasanta mai shekara 21 daga Brazil, Savinho ko da kudin tayinsa ya kai £60m. (Fabrizio Romano, external)

West Ham na son sayen mai tsaron baya a Brazil John Victor mai shekara 29, daga Botafogo. (Sky Sports, external)

West Ham ta faɗawa Everton ta son ta cigaba da zama da Tomas Soucek bayan Merseyside ta bayyana bukatarta kan ɗan wasan na Jamhuriyar Czech mai shekara 30. (Athletic - subscription required, external)

Tottenham ta amince ta bada aron ɗan wasan baya na Croatia mai shekara 18, Luka Vuskovic zuwa ga Hamburg. (Standard, external)

Sunderland na fatan shawo kan West Ham domin saye Nayef Aguerd mai shekara 29, daga Marseille, yayinda AC Milan da AS Roma ke zawarcin matashin ɗan asalin Moroko. (Footmercato - in French, external)

Sunderland ta gabatar da tayin £24m kan ɗan wasan Bologna mai shekara 27 Jhon Lucumi daga Colombia. (Sky Sports, external)

Genoa na son saye ɗan wasa Maxwel Cornet daga West Ham bayan ɗan wasan na Ivory Coast ya burge Patrick Vieira a zamansa na aro tsakanin kakar 2024-25 season. (Tuttomercatoweb - in Italian, external)

Ɗan wasan Bournemouth mai shekara 25 daga Ivory Coast, Hamed Traore na shirin zuwa Marseille.. (Footmercato - in French, external)

Wolves na son ɗan wasan Genk Tolu Arokodare, mai shekara 24 daga Najeriya. (Sky Sports, external)