Liverpool na son ta sayi Isak kan fan miliyan 130, Hojlund na gab da komawa Napoli

Alexander Isak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 3

Ana sa ran Liverpool za ta gabatar da fan miliyan 130 don siyan dan wasa mai kai hari na Newcastle da Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, tare da Karin alawus-alawus da zai sa ya zama cinikin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Ingila. (Telegraph - subscription required, external)

Manchester United ta amince ta tura Rasmus Hojlund, mai shekara 22, aro na tsawon kakar wasa zuwa Napoli, tare da wani sharadi na siyansa kan fan miliyan 38.(Athletic - subscription required, external)

Brentford ta yi tayin kusan fan miliyan 45 kan dan wasan amus Maximilian Beier mai shekaru 22 da Borussia Dortmund ta ki amincewa da shi.(Athletic - subscription required, external)

Dan wasan tsakiyar RB Leipzig da Austria Christoph Baumgartner, mai shekara 26, na cikin 'yan wasa da Crystal Palace ke sha'awa. (Sky Sports, external)

Crystal Palace ta kuma kai tayin fan miliyan 8 kan dan wasan Bournemouth David Brooks, mai shekara 28, amma Cherries ba sa son siyar da dan.(Sun, external)

Roma ta yi wa Chelsea tayin sayen dan wasanta Tyrique George, amma Fulham da Crystal Palace da zakarun Jamus Bayern Munich suma suna sha'awar daukar kan dan wasan na Ingila mai shekaru 19.(Sky Sports, external)

AC Milan na zawarcin dan wasan bayan Manchester City Manuel Akanji, yayin da Crystal Palace kuma ke zawarcin dan kasar Switzerland mai shekara 30. (Sky Sports, external)

Monaco na son tsohon dan wasanta da ke taka leda a Chelsea Axel Disasi ya koma kungiyar kuma tana fatan dan wasa bayan Faransa mai shekara 27 zai sa hannu kan kwantaragin bada shi aro, sai dai Bournemouth da Aston Villa suma suna son su dauko dan wasan.(Footmercato - in French, external)

Liverpool da Roma na aiki kan yarjejeniyar karshe da za ta ba dan wasan bayan Girka Kostas Tsimikas, mai shekara 29, damar koma wa kungiyar ta Serie A club a matsayin aro . (Gianluca di Marzio - in Italian, external)

Marseille na sha'awar sayen dan wasan bayan Arsenal da Ukraine Oleksandr Zinchenko, amma albashin dan wasan mai shekaru 28 zai iya kawo cikas. (Athletic - subscription required, external)

Golan Italiya Gianluigi Donnarumma har yanzu yana sa ran barin Paris St-Germain kafin wa'adin da aka debar masa ya zo karshe kuma wata kungiya a Premier League da ba a bayyana sunanta ba ta bi sawun Manchester City a cikin masu zawarcin dan wasan mai shekaru 26.(Sky Sports, external)

AC Milan ta ki amincewa da tayin da Bournemouth tayi mata na bata aron dan wasan bayanta Alex Jimenez mai shekara 20 tare da zabin siyansa kan fan miliyan 17 (La Gazzetta dello Sport - in Italian, external)