Aston Villa ta tattauna da Man U kan Sancho,Tottenham na zawarcin Lookman

Aston Villa ta tattauna da Manchester United kan daukar dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25(Athletic - subscription required), external
Haka kuma Aston Villa na zawarcin golan Royal Antwerp dan kasar Belgium Senne Lammens, mai shekara 23.(Fabrizio Romano), external
Tottenham ta tuntubi Atalanta kan dan wasan Najeriya Ademola Lookman amma tana fuskantar hamayya daga Bayern Munich kan dan wasan mai shekaru 27. (Sky Sports Germany), external
Galatasaray na tattaunawa da Tottenham kan cinikin dan wasan tsakiyar Mali Yves Bissouma, mai shekara 29 (Independent), external
AC Milan ta gabatar da tayin sayen dan wasan tsakiyar Liverpool Joe Gomez, mai shekara 28, a matsayin dan wasa na dindindin, inda kungiyoyin biyu sun tattauna kan sharuddan cinikin.(Fabrizio Romano), external
Fenerbahce tana aiki kan yarjejeniyar siyan golan Brazil Ederson, mai shekara 32, daga Manchester City bayan ta yi watsi da tayin yuro miliyan 10 na Galatasaray ta Turkiyya (Fabrizio Romano), external
Newcastle United na son ta dauko dan wasan Roma na kasar Ukraine Artem Dovbyk, mai shekara 28, kan fam miliyan 30, a matsayin aro da nufin siya.(Sun), external
Aston Villa ta kulla yarjejeniya da Aberdeen don siyan matashin dan wasan Scotland mai shekara 17 Fletcher Boyd. (Football Insider), external
Kungiyar Aston Villa ta Unai Emery na dab da daukar dan wasan baya na kasar Sweden Victor Lindelof, mai shekara 31, wanda ba da shi kwantaragi da wata kungiya bayan ya bar Manchester United . (Birmingham Live), external














