Barcelona na son Guehi, Manchester United za ta ci gaba da zawarcin Baleba

Marc Guehi
Bayanan hoto, Marc Guehi
Lokacin karatu: Minti 3

Barcelona ta bi sahun Liverpool da Real Madrid wajan zawarcin dan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi mai shekara 25. (Sport - in Spanish), external

Dan wasan bayan Liverpool Joe Gomez,mai shekara 28, ya ja hankalin Crystal Palace da Brighton a ranar da wa'adin musayar 'yan wasa ya zo karshe sai dai dan wasan Ingila ya ci gaba da kasancewa a Anfield ya yin da Liverpool ta kasa dauko Guehi. (Football Insider, external)

Dan wasan bayan Ingila James Tarkowski mai shekara 31, da dan wasan bayan Ukraine Vitalii Mykolenko mai shekara 26, da dan wasan tsakiyar Ingilla James Garner mai shekara 24 za su san makomarsu a Everton ya yin da 'yan wasa su uku sun kai watan karshe na kwantaraginsu na tsawo wata 12 (Times - subscription required), external

Manchester United za ta iya komawa Brighton don daukar dan wasan tsakiya Carlos Baleba a shekara mai zuwa, bayan da suka gaza a yunkurinsu na sayen dan wasan Kamaru mai shekara 21 a kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara. (GiveMeSport, external)

Fulham za ta ba da ingantaccen kwantiragi ga Rodrigo Muniz bayan da suka nace kan dan wasan Brazil mai shekara 24 duk da sha'awar da kungiyar Atalanta ta Serie A ta nuna kan 'dan wasan a bazara. (GiveMeSport, external)

Ana sa ran Emiliano Martinez zai koma cikin tawagar Aston Villa bayan golan Argentina mai shekaru 33 ya kasa samun damar komawa Manchester United a ranar karshe. (Athletic - subscription required, external)

Martinez ya shirya yin watsi da tayi daga Saudi Pro League da Turkish Super Lig, inda har yanzu kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a bude take, domin ya ci gaba da zama a Villa har zuwa wata kakar wasa. (Football Insider, external)

Yunkurin Tottenham na daukar Jan Paul van Hecke, mai shekara 25, ya kara karfi bayan dan wasan bayan Netherlands ya yanke shawarar dakatar da sanya hannu kan sabon kwantiragi a Brighton.(GiveMeSport, external)

Watakila Rangers ta koma da wani sabon tayi kan dan wasan Crystal Palace Jesurun Rak-Sakyi bayan da kungiyar yankin Scotland ta kasa cimma wa'adin sayan dan wasan Ingila mai shekara 22 (Football Insider, external)

Wolves ta Sanya wani sharadi a cikin yarjejeniyar aro wanda ya ba dan wasan gaba Sasa Kalajdzic, mai shekara 28, damar shiga LASK wanda ke nufin za su iya kiransa a watan Janairu. Haka kuma kungiyar ta Ostiriya ba ta da wani zabi na siyan dan wasan karkashin wani bangare na yarjejeniyar (Express & Star), external