Spence zai zama Musulmi na farko a babbar tawagar Ingila cikin shekara 155

Djed Spence

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Djed Spence na taka wa Tottenham leda a baya daga gefen dama
Lokacin karatu: Minti 3

Djed Spence na fatan zama zakaran gwajin dafi a matsayin Musulmi na farko da zai taka wa babbar tawagar Ingila ta maza leda.

Ɗanwasan bayan na Tottenham ya buga wa tawagar 'yan ƙasa da shekara 21 leda sau shida, amma wannan ne karon farko da aka kira shi babbar tawagar da za ta buga wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.

Duk da cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ba ta adana bayanan addinin 'yanwasanta, an fahimci cewa Spence zai iya zama Musulmi na farko da zai taka mata leda.

"Abin alheri ne - abin murna. Na rasa ma kalaman da zan bayyana," a cewar ɗanwasan mai shekara 25.

"Ina yawan yin addu'a. Ina gode wa Allah a lokutan da nake cikin ƙunci. Na yi imanin cewa Allah yana tare da ni a kodayaushe. Wannan muhimmin abu ne a wurina, da addinina."

Tottenham ta tura ɗanƙwallon wasan aro har sau uku a Rennes, da Leeds, da Genoa.

Ingila za ta kara da Andorra a filin wasa na Villa Park ranar Asabar, kafin ta ziyarci Serbia a ranar Talata.

Spence ya ce ba shi jin wani ƙarin nauyi saboda addininsa, amma yana fatan rawar da zai taka za ta ƙarfafa wa sauran 'yanwasa masu zuwa gwiwa.

"Ba ni jin wani matsi a raina. Kawai ina taka leda ne ina murmushi, cikin nishaɗi," a cewarsa.

"Idan har zan iya kowa ma zai iya. Ba wai 'ya'yan Musulmi ba kawai, kowane yaro daga kowane addini. Kawai idan mutum ya mayar da hankali zai iya ko ma mene ne."

Yadda Spence ya samu gurbi a tawagar Ingila

Djed Spence

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Djed Spence kenan yake atasaye a sansanin tawagar Ingila ranar Laraba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafin 15 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, minti 64 kacal Spence ya buga a gasar Premier League a kakar 2004-25.

Bayan haka ne kuma ya buga minti 90 sau 19 cikin wasa 22 da ya buga wa Tottenham.

Sauyin da ya samu mai girma ne sosai. Da farko, tsohon mai horarwa Ange Postecoglou bai ma saka shi cikin tawagar ƙungiyar da ta buga gasar zakarun Turai ta Europa ba.

Har sai da aka kai zagayen 'yan 16 kafin ya buga minti 180 a wasan da suka doke AZ Alkamaar.

Sai kuma lokacin da ya shiga daga benci wasan ƙarshe da Tottenham ta doke Manchester United domin ɗaukar kofi karon farko cikin shekara 17, wanda ya ba su damar zuwa gasar Champions League.

Bayan buga wa Tottenham kowane minti a kakar wasa ta bana, Spence ya samu kira daga mai horarwa Thomas Tuchel.

"Tabbas abu ne muhimmi mutum ya samu damar taka wa Ingila leda," kamar yadda Spence ya bayyana.

"Kociyan ya tarɓe ni da kyau, kowa a nan ya ba ni kyakkyawar tarɓa. Kuma na taka leda a tawagar 'yan ƙasa da shekara 21, saboda haka na ɗan san yadda abin yake. Amma ban taɓa buga babbar tawaga ba."

A watan Maris na 2022 ne ya fara buga wa 'yan 21 wasa. Koci Lee Carsley ya so ya gayyaci Spence gasar European Championship ta 'yan ƙasa da shekara 21 amma sai rauni ya hana shi zuwa.

Lee Carsley ya taɓa faɗa wa BBC a farkon shekarar nan cewa: "Yana da ƙwarewa a fannoni; yadda yake jawo ƙwallo kuma ya yanka abokan hamayya, yake cin ƙwallon, yake tarewa. Ɗanwasa ne da ba shi da iyaka nan gaba."