Waɗanne ɗalibai ne aka ɗauke wa wajibcin cin lissafi kafin shiga jami'a a Najeriya?

Wani ajin ɗaukar darasi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya ta bayyana sabon tsari da ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin malamai da ɗalibai a faɗin ƙasar, inda ta sanar da cewa ba za a sake wajabta wa ɗaliban sakandire da ke neman karatu a fannin da ba na kimmiya ba cin darasin lissafi kafin samun gurbin karatu a jami'a ko kwalejin fasaha ba.

Shekaru da dama, duk wanda yake neman shiga jami'a a Najeriya dole ne sai ya lashe darussa biyar a matakin 'credit' a jarabawar WAEC ko NECO, ciki har da Turanci, yayin da ake buƙatar lissafi a wasu fannonin, ko da da matakin 'E' ne.

Lamarin ya daɗe yana zama ƙalubale ga ɗalibai da dama, musamman waɗanda ke son karatu a fannonin adabi da tarihi da ilimin nazarin falsafa da da kuma harsuna.

Me wannan sabon tsarin ke nufi?

...

Asalin hoton, Getty Images

Dr Aliyu Usman Tilde, tsohon kwamishinan ilimi na jihar ya bayyana wa BBC cewa wannan mataki na nufin komawa tsarin da aka yi amfani da shi a baya.

"A da, an sauƙaƙe wa waɗanda ke son karatu a fannin da ba na kimiyya ba, kamar tarihi da siyasa, cewa ba sai sun samu kyakkyawan sakamako na 'credit' ba a lissafi, jarabawar gama sakandire," in ji Dr Tilde.

"Daga baya ne wasu gwamnatoci suka kawo sauye-sauye wanda ya sanya dole sai ɗaliban da ba na kimiyya ba, wato 'Arts' su samu sakamako mai kyau a lissafi, wanda hakan ya zama ƙalubale sosai ga masu sha'awar karatu a waɗannan fannoni."

Mai sharhin ya ƙara da cewa yana maraba da wannan tsarin saboda lissafi yana hana wasu ɗalibai shiga karatun fannin Arts da wasu ma dama.

"Idan aka ce sai sun iya lissafi, toh kusan an toshe musu hanyar shiga jami'a ne."

Ta yaya tsarin zai taimaka wa ɗalibai?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr. Tilde ya bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka matuƙa ga ɗalibai, musamman waɗanda ke son karantar fannonin Arts kamar tarihi da sauran su.

"Yanzu ɗalibi da yake son karantar 'Arts' ba sai ya samu kyakkyawan sakamako a lissafi ba, muddin yana da na Turanci da sauran fannoni da ake buƙata, ana iya ba shi damar shiga jami'a."

Amma kuma ga waɗanda suke son shiga kwalejin fasaha, Dr. Tilde ya bayyana cewa:

"A matakin difloma, idan abin da ɗalibin ke son karantawa bai shafi kimiyya da fasaha ba, to sakamako mai kyau na Turanci kawai ake buƙata.

"Idan kuma ɗalibin na son karantar fannin kimiyya ne, dole ne ya kasance yana da sakamako mai kyau a lissafi, ko da bai da kyakkyawan sakamako a Turanci.

"A matakin Babban Difloma kuma, ana buƙatar cewa dole ne waɗanda suka je kwalejin fasaha suna da 'credit' a lissafi da turanci ba tare da la'akari da fannin da suke son karantawa ba.

"Sai kuma waɗanda suke matakin NCE, idan har Arts suke son su karanta da social sciences, ana buƙatar dole su samu sakamakon 'credit' a turanci, amma ba lalle ba ne suna da shi a lissafi, amma kuma idan suna son su karanta kimiyya da fasaha, dole sai sun samu da 'credit' a lissafi."

Sai dai Dr. Tilde ya nuna damuwarsa a kan matakin NCE:

"A matakin NCE, wannan tsari yana bukatar gyara. Dalilin shi ne cewa wanda ke karatun NCE ana shirya shi ne ya zama malami domin koyarwa a makarantun firamare da ƙananan sakandire."

Ya ce, a makarantun gwamnati, malami guda ɗaya ne ke koyar da lissafi, Turanci, da sauran fannoni wato tsarin malamin ɗaya ga duk aji ɗaya kenan. Idan ɗalibin NCE bai iya lissafi ba, ta yaya zai koyar da yara? Za su tashi su ma ba za su iya lissafi ba wanda hakan zai cutar da su, wannan shi ne dalilin da ya sa dole ne wanda ke NCE ya iya Turanci da lissafi.

Mene ne tasirin wannan sabon tsarin?

Dr. Tilde ya ce babban tasirin wannan sabon tsarin shi ne zai sauƙaƙa wa ɗalibai shiga jami'a kuma su karanci abin da suke so.

Amma kuma ya ce tsarin zai iya jefa ɗaliban da suka karanci fannin da ba na kimmiya ba su tsinci kansu a fannonin da ke buƙartar lissafi ta ɓangare aiki idan sun gama karatu a rayuwarsu.

"Hakan na faruwa sosai, mutum na iya samun aikin da kwata-kwata bai da alaƙa da abin da ya karanta a jami'a."

"Ko da ma a ce mutum muƙami ya samu na siyasa, dole ne sai ya yi karo da lissafi."

Saboda haka ne Dr Tilde ya ce cire wajabcin samun sakamako me kyau a lissafi kafin shiga makarantun gaba da sakandire ka iya zama da amfani da kuma rashin amfani a gare su.