Buƙatu 7 da ke sa ASUU shiga yajin aiki

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar malaman jami'a ta Najaeriya ASUU ta fara yajin aikin gargaɗi na makonni biyu bayan wa'adin da ta bai wa gwamnatin ƙasar domin biyan buƙatun ta ya jika a ranar Lahadi.
Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwuna, ya shaidawa wani taron manema labarai a jami'ar Abuja a ranar Lahadi cewa shugabannin ASUU sun cimma matsayar shiga yajin aikin ne bayan wa'adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnati daga ranar 28 ga watan Satumba ya cika, ba tare da gwamnatin ta yi abin da ya kamata ba.
Ya ce da wannan sanarwa "Muna umartar dukkan rassan ASUU su janye daga gudanar da duk wani aiki daga safiyar ranar Litinin 13 ga watan Oktoban 2025. Kuma yajin aikin gargaɗin zai shafi kowanne irin aiki da malaman jami'a ke yi, kamar yadda babban kwamitin ƙoli na shugabancin ƙungiyar ya amince.
Ƙungiyar malaman jami'ar ta zargi gwamnati da rashin mayar da hankali wajen aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakanin su, da kuma rashin gaskiya a tattaunawa da suke yi domin kaucewa shiga yajin aikin.
Buƙatu bakwai da ASUU ke son a biya mata
Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) reshen Jami'ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Ibrahim Tahir Suraj, ya bayyana irin buƙatun da ASUU ke nema daga gwamnatin tarayya yayin tattaunawa da BBC.
Ya ce ƙungiyar ta jima tana neman gwamnati ta biya hakkokinta da sauran buƙatu da suka haɗa da:
- Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009
ASUU na son gwamnati ta sabunta yarjejeniyar da aka cimma tun 2009, wadda ta shafi yadda ake gudanar da ayyukan jami'o'i da yanayin aiki da kula da koyarwa.
Wannan yarjejeniya ta haɗa da batutuwan zamantakewar ɗalibai da ikon jami'o'i su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba wato da bai cin gashin kansu kenan.
- Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami'o'i
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyar na buƙatar gwamnati ta riƙa ba da kuɗaɗen gudanarwa na jami'o'i domin a inganta:Azuzuwa da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan ɗalibai da asibitocin jami'o'i da kuma ɓangaren wasanni. ASUU na ganin wannan zai inganta karatu da bincike a jami'o'in ƙasar.
- Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi.
Malaman jami'a sun ce suna da haƙƙin albashi na wata uku da rabi da suka yi aiki amma ba a biya su ba. ASUU na so gwamnati ta biya wannan bashin nan da nan.
- Biyan su cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami'a
Ƙungiyar na neman a biya cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami'a fiye da shekara guda da ta wuce, wanda ba su ne suka nema ba amma gwamnati ta kasa cikawa.
- Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu.
ASUU ta bayyana cewa ana cire wasu kuɗaɗe daga albashin malaman da ake cewa za a tura su zuwa ƙungiyoyinsu amma har yanzu ba a tura ba. Wannan na haifar musu da matsala wajen biyan bukatunsu da suka dogara da wadannan kungiyoyi.
- Biyan ƙarin albashi ga malaman da aka ƙara musu muƙami
Wasu malaman da aka ƙara musu muƙami a jami'o'i sun ce har yanzu ba a biyasu ƙarin albashin da ya zo da sabon muƙaminsu ba, don haka ASUU na so gwamnati ta biya su bisa sabon matsayin da suke kai yanzu.
- Dakatar da korar ma'aikatan jami'o'i ba bisa ƙa'ida ba
ASUU ta nemi gwamnati ta dakatar da korar ma'aikata haka kawai, wanda shugaban ya kira da "victimization"
Farfesa Abdulkadir Muhammad, jami'in tsare-tsare na ƙungiyar ASUU reshen jihar Kano ya shaida wa BBC sun bai wa gwamnati duk wata damar da ta kamace ta.
''Saboda da haka muka ga babu abin da ya dace mu yi illa mu bai wa mabobinmu umarni su janye daga aiki na sati miyu, da fatan cewa wannan mataki da muka dauka zai fargar da gwamnati ya sa ta yi abin da ya kamata,'' In ji farfesa Muhammad.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar tana sane da yadda matakin nata zai iya shafar karatun ɗaluban su, amma kuma ba su da wani zaɓi da ya zarce shi.
''Yayin da kazo ka zauna ka ce ka ɗauki ma'aikaci ya yi maka aiki....ba ka iya biyan sa haƙƙin sa, wannan ma zai iya sa ma'aikacn bai yi abin da ya akamata ba kuma zai shafi ɗaluban.
Ƙungiyar malaman jami'ar dai ta ce sabuwar dambarwa a tsakanin ta da gwamnatin Najeriya ta samo asali ne daga halin ko in kula da gwamnatin ke nunawa a matakai daban-daban na tattaunawar neman mafita da suka yi a tsakanin su.
ASUU ta jajirce kan neman gwamnatin ta aiwatar da yarjejeniyar da ta ƙulla da ita a 2009, wadda ta yi tanadin yadda za a kula da walwalar malaman jami'ar, da kula da jami'oin ƙasar da kuma sauran batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin jami'a.
Martanin gwamnatin Najeriya
Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga ASUU, inda ta yi gargaɗin cewa za ta aiwatar da tsarin 'ba aiki, babu biyan albashi' kan malaman idan suka shiga yajin aikin.
Kakakin ma'aikatar ilimi ta Najeriya, Folasade Boriowo, ta ce gwamnati ta yi wa ƙungiyar tayi mai gwaɓi, kuma tana jiran martanin ta.
Ta ce daga cikin tayin da gwamnati ta yi wa ASUU har da matakan magance muhimman matsalolin da ƙungiyar ta gabatar da suka haɗa da inganta yanayin aiki da gyara a tsarin gudanar da jam'oi da kuma walwalar malaman.
Ta kuma zargi ASUU da rashin bayar da haɗin kai, duk da kokarin da ta ce gwamnati na yi domin kaucewa shiga yajin aikin.










