Me ya janyo mummunar faɗuwar jarrabawar WAEC a Najeriya?

Sakamakon da hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Afirta ta Yamma, (WAEC) ta fitar ya nuna gagarumar faɗuwar ɗaliban Najeriya a bana.
A ranar Litinin ne shugaban hukumar a Najeriya, Amos Dangut ya bayyana fitar da sakamakon a lokacin wani jawabi ga manema labarai a ofishin hukumar da ke birnin Legas.
Sakamakon ya nuna cewa daga cikin ɗalibai 1,969,313 da suka rubuta jarrabawar, 754,545 (kashi 38.32 cikin 100) ne kawai suka samu kiredit a darussa biyar da suka ƙunshi Turanci da Lissafi.
Tuni iyaye da ɗaliban da masu ruwa da tsaki a fannin ilimin ƙasar suka fara nuna damuwarsu kan mummunan sakamakon jarrabawar.
'Mafi munin sakamakon cikin shekara biyar'

Asalin hoton, Facebook
Sakamakon wannan shekara ya nuna cewa shi ne mafi muni cikin shekara biyar da suka gabata.
A shekarar 2020, WAEC ta ce kashi 65.24 cikin 100 na kimanin miliyan 1.6 da suka rubuta jarrabawar ne suka samu kiredit a darussa biyar da suka ƙunshi Turanci da Lissafi.
Sai kuma 2021 aka samu ci gaba inda kashi 81.7 suka samu kiredit a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Amma a 2022 adadin ya ragu, inda ya koma kashi 76.36, yayin da a 2023 aka samu kashi 79.81, sai kuma a shekarar 2024 da ta gabata inda aka samu kashi 72 cikin 100 suka ci jarrabawar.
Me ya janyo mummunar faɗuwar?

Asalin hoton, AFP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙarancin ilimin kwamfuta: A jarrabbawar ta bana wasu cibiyoyin sun yi amfani da na'urorin kwamfuta wajen amsa jarrabawar kamar yadda ake yi a jarrabawar JAMB.
Hukumar ta WAEC ta danganta faɗuwar jarrabawar da ƙarancin ilimin kwamfuta ga ɗaliban da suka rubuta jarrabawar.
Dogara da satar amsa: Shugaban hukumar a Najeriya, Amos Danguta ya kuma wani abu da ya janyo faduwar shi ne yadda mafi yawan ɗalibai suka dogara da satar amsa a wannan karo hukumar ta fitar da mabambantan tambayoyi musamman na zaɓi-ka-tiƙa ga ɗaliban.
Mista Dangut ya ce WAEC ta fito da wannan salo ne domin magance satar jarrabawa da ɗaliban ke yi.
''An bayar da mabambantan tambayoyi ga ɗalibai a jarrabawar Turanci da Lissafi da Bayoloji da Ekonomi domin yi wa ɗaliban da suka dogara da kofar amsa ɓad-da-bami'', in ji shi.
Rashin kula da walwalar malamai: Shi kuwa Dakta Aliyu Tilde, mai sharhi kan al'amuran ilimi kuma tsohon kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi ya danganta faɗuwa jarrabawar da rashin kula da walwalar malaman makaranta.
''Tsadar rayuwa ta jefa malaman makaranta cikin halin tagayyara, lamarin da ya sa suka kawar da hankalinsu daga aikinsu na koyar da ɗalibai'', in ji shi.
Dakta Tilde ya ce malaman makaranta suna cikin rukunin mutane da samun kuɗinsu a ƙayyade yake wato ta hanyar albashi kawai.
''Kuma yanzu wannan albashin ba ya wadatar da su, don haka hankalinsu ya tashi ya koma neman abin da zai ci'', in ji Tilde.
Tasirin amfani da shafakan sada zumunta: Dakta Tilde ya ce wani abu da ya sa aka faɗi jarrabawar WAEC a bana shi ne amfani da shafukan sada zumunta.
''Wannan na ɗaya daga cikin manyan dalilan faɗuwar, saboda yadda hakan ke ɗauke wa ɗaliban hankali daga karatu''.
''A yanzu da yaro ya koma gida kawai ya ɗauki wayarsa ya riƙa cartin, ko shiga sauran shafukan sada zumunta, kai wasu ma ɗaliban da wayar suke zuwa aji'', in Dakta Tilde.
Mene ne makomar Ilimi nan gaba a Najeriya?

Asalin hoton, others
Wannan ne dai karo na biyu da ɗaliban Najeriya suka yi mummunar faɗuwa a wata babbar jarrabawa a ƙasar.
A watannin baya sakamakon da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makaratntu ta ƙasar, JAMB ta fitar ya nuna samun gagarumar faɗuwa jarrabawar.
Dakta Tilde ya ce matsawar aka tafi a haka makomar na cikin barazana, sai dai ya ce dole ne ɗalibai da gwamnati su zage dantse wajen maganec matsalar.
''Shi ɗan'adam a duk lokacin da ya samu kansa cikin wani hali da bai saba da shi ba, to yana ƙoƙarin gyarawa ta yadda zai saba da wannan abu, don haka dole ne ɗalibanmu su cire wa ransu batun satar jarrabawa'', in ji masanin ilimin.
Ya kuma ƙara da cewa dole ne ɗalibai su sabar wa kansu amfani da fasaha wajen amsa jarrabawar, tun da dai alamu sun nuna cewa da ita za a riƙa amsa jarrabawa a nan gaba.
Daga ɓangaren iyayen yara kuma tsohon kwamshinan ilimin ya ce dole ne gwamnati da iyaye da malamai da masu ruwa da tsaki su zage dantse wajen tabbatar da ɗalibai sun samu wadutar fasahar da kuma ilimin amfani da su.
''A wasu wuraren gwamnati tana ƙoƙarin samar da waɗannan na'urori amma sai a haɗa baki da wasu gurɓatattun malamai da masu gadi da wasu manyan a unguwa wajen sace waɗannan na'urori'', in ji Dakta Tilde.
Yana mai cewa lokaci ya yi da za a daina wannan ɗabi'a.
Ta yaya za a magance hakan a nan gaba?

Asalin hoton, Google
Iyaye: Dakta Tilde ya ce babban abin da ya kamata a yi shi ne iyaye a farko su cusa wa ɗalibai burin karatu a zukatansu.
''Ya kamata a ce yaro yana samun sa'a tara na karatu a gida, banda na makaranta, yana da kyau a ce yaro na da tambayoyin jarrabawa na aƙalla shekara 10 ya kuma iya amsa su'', in ji shi.
Malamai: A makaranta kuma Dakta Tilde ya ce dole ne malamai su riƙa faɗakar da ɗalibai game da makomarsu.
''Malamai su riƙa cusa musu aƙidar cewa kyautatuwar makomar rayuwarsu ta gaba ta dogara ne kan karatun da suke yi'', in ji shi.
Gwamnati: A nata ɓangare ita ma gwamnati ya kamata ta yi hoɓɓasa wajen samar da abubuwan da ake buƙata, a cewar Dakta Tilde.
''Yadda aka doshi amfani da na'ura wajen amsa jarrawabawa, dole ne gwamnati ta tabbatar da samar da isassun waɗannan na'urorin da ake buƙata domin wannan aiki.
Al'umma: Masanin harkokin ilimin ya ce su ma al'umma na da rawar da za su taka wajen magance wannan matsala.
"Ƙungiyar iyayen yara da malamai da sauran al'ummar gari su kula da waɗannan na'urori domin tabbatar da suna aiki yadda ya kamata domin yaransu su samu ingantaccen yanayin karatu, su kuma ci jarrabawa'', in ji shi.











