Yadda wasu mutane ke fama da lalurar rashin jin tsoro

Zanen hoton kan mutum
    • Marubuci, Jasmine Fox-Skelly
  • Lokacin karatu: Minti 6

Tsoro ɗaya ne daga cikin hanyoyin neman tsira da ke zuwa wa ɗan'adam, amma kuma akwai mutanen da ke da wata lalura da ke hana su jin tsoron gaba ɗaya.

Ta yaya irin waɗannan mutane ke gudanar da rayuwarsu ba tare da tsoro ba?

Yi tunani idan mutum ya faɗo daga jirgin sama ba tare da ya ji ko ɗar ba a zuciyarsa.

Abin da ya faru kenan da Jordy Cernik, wani ɗan Birtaniya, wanda aka yi wa tiyatar cire masa gaɓoɓin adrenal glands - waɗanda su ne ke kula da damuwa a jikin mutum. Hakan na faruwa ne idan adrenal glands ɗin suka fitar da sinadaran gajiya cortisol masu yawa a jikin mutum.

Tiyatar ta yi aiki fiye da yadda ake tunani, saboda tun daga lokacin Jordy ya daina jin tsoro. Amma kuma an samu wata matsala.

Lokacin da ya yi balaguro zuwa Disneyland a 2012, ya hau kan abin wasa mai majaujawa na roller coaster kuma bai ji wani tsoro ba. Daga baya, ya yi alkafira zuwa cikin kogi, ya hau motar da ke tafiya kan igiya - duka ba tare da ya ji wata faɗuwar gaba ba.

Ba a saba ganin abin da Cernik ya yi ba. Amma masu lalurar Auerbach-Wiethe sun san da hakan - kodayake su ma ba su da yawa a duniya. Mutum 400 kacal aka taɓa samu da ita a duniya.

Wata mace da aka sani da lalurar ta Auerbach-Wiethe wadda kuma ake wa laƙabi da SM, an sha yi mata gwaje-gwaje na kimiyya tun daga shekarun 1980 a Jami'ar Iowa da ke Amurka.

A farkon shekarun 2000, wani mai bincike Justin Feinstein ya shiga binciken yadda zai tsoratar da SM.

"Mun nuna mata duk wani fim ɗin tsoro da muka sani," in ji Feinstein wanda yanzu ke aiki da cibiyar Float Research Collective a matsayin likitan ƙwaƙwalwa.

Hannun wani mutum a cikin jirgi ya dafa kujera cikin alamun tsoro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani bincike ya nuna cewa tsoro ba nau'i guda ɗaya ba

Finafinai irinsu The Blair Witch Project, Arachnophobia, The Shining, The Silence of the Lambs, Waverly Hills Asylum, babu wanda ya razana ta ko kaɗan.

"Mun kuma kai su wurin macizai da gizo-gizo, amma ban da tsananin rashin tsoro da suka nuna, har ma sun dinga nuna sha'awar kai musu hannu ko ma su yi ƙoƙarin hira da su."

Larurar Auerbach-Wiethe na faruwa ne idan mutum ya rasa wani ɓangare na sinadaran halittar gado da ke cikin ƙwaƙwalwarsa.

Amygdala wani ɗan ƙaramin rami ne mai kama da ƙirar dabino a ƙwaƙwalwar mutum, wanda shi ne ya fi samun matsala kuma ake alaƙanta shi da sarrafa tsoro da fargaba a jikin ɗan'adam.

Ita SM ta daina jin tsoro ne bayan lalurar ta lalata mata sinadarin halittar gado na amygdala.

"Wani abin mamaki shi ne maganar ta tsaya ne kan tsoro kawai - sauran abubuwan da suka shafi jin abu a jiki ba su samu wata matsala ba, kamar farin ciki, ko fushi, ko ɓacin rai," in ji Feinstein.

Nau'ukan tsoro

Akwai yiwuwar cewa sinadarin amygdala ya fi aiki a kan wasu nau'ukan tsoro sama da wasu. Misali, ya fi aiki wajen "daidaita tsoro". Gwaje-gwajen da aka yi kan ɓeraye sun nuna idan aka ɗoɗana wa dabbobi lantarki jim kaɗan bayan sun ji ƙarar wani sauti za su yi motsi daidai da wanda suka yi daga jin sautin kaɗai ko da babu lantarkin a jikinsu.

Duk da cewa SM ta san cewa bai kamata ta taɓa kasko mai zafi ba, wannan bai sa ta ɗauki hakan a matsayin wani abin tsoro ba - ma'ana ba ta jin wani bugun zuciya ko faɗuwar gaba da ake ji idan mutum ya ji raɗaɗi. Haka nan, ba ta iya ganewa idan fuskar wani ta nuna fargaba, amma kuma tana gane farin ciki da ɓacin rai a fuskokin wasu.

Sannan tana hulɗa da jama'a kamar yadda ya kamata, amma ba ta iya kauce wa shiga haɗari, abin da ya jawo aka dinga yi mata barazana da wuƙaƙe ko bindiga a lokuta daban-daban.

Wani ƙaramin yaro zaune cikin awaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mukan ji wata 'yar zaƙuwa duk lokacin da wani mutum ya kusanto mu, amma masu larurar rashin sinadarin amygdala ba su jin ta ko kaɗan

"Takan je kusa da mutanen da ya kamata ta kauce wa, wanda hakan ke jefa ta cikin haɗari saboda rashin fahimtar haɗarin," a cewar Feinstein.

A wani bincike, an tambayi wani baƙon mutum ya je kusa da SM, inda ta bayyana nisan da za ta iya jin rashin daɗi idan wani ya matso kusa da ita da cewa mita 0.34 ne - kuma wannan rabi ne na kusancin da sauran mutane ke faɗa. Hakan na nufin ba ta damu ba ko da wani wanda ba ta sani ba na matsawa kusa da ita.

"A irin wannan yanayi, SM da sauran mutanen da ke da matsalar za su iya zuwa har kusa da hancin wani baƙon mutum da ba su sani ba, abin da masu cikakken sinadarin amygdala ba za su yi ba," in ji Alexander Shakman, wani farfesa a Jami'ar Maryland.

Binciken Weinstein ya nuna cewa akwai nau'i biyu na tsoro a ƙwaƙwalwa, yana danganta ne kawai da cewa ko haɗarin daga cikin jiki ne ko kuma daga waje.

Wasu mutane na yin tsalle daga jirgin sama zuwa ƙasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maras lafiya "SM" kenan take faɗowa daga jirgi sanye rigar lema kuma ba ta ji komai ba larurar ƙwaƙwalwarta

Idan haɗarin na waje ne, sinadarin amygdala na aiki ne a matsayin jagoran, wanda zai faɗa wa ƙwaƙwalwa abin da ya kamata ta yi. Da farko yakan samu bayanai ne dangane da gani, da ƙamshi ko wari, da ɗanɗano, da kuma ji.

Idan ya hangi wani haɗari, kamar ɓarawo yana tunkarowa, ko maciji, ko wata dabba, zai aika wa sashen hypothalamus na ƙwaƙwalwa da ke saman wuyan mutum daga baya bayani, wanda shi kuma zai faɗa wa gaɓar adrenal glands cewa su saki sinadarai zuwa cikin jini.

"Hakan na jawo bugawar zuciya da sauri, hawan jini, da sauran abubuwan da ake ji na fargaba," in ji Feinstein.

Idan kuma haɗarin daga cikin jikin mutum yake, kamar hauhawar yawan iska a cikin jini, ƙwaƙwalwa kan yi a yanayi na musamman. Jikin mutum na fahimtar ƙaruwar yawan iska a jini a matsayin alamun shirin sarƙewar nimfashi.

Amfanin jin tsoro

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lamarin SM na musamman ne, saboda haka ba lallai ne abin da bincike ya gano a kan ta ya zama iri ɗaya da na sauran mutane ba.

Matsalarta ita ce, larurar ta lalata dukkan sinadarin amygdala da ke ƙwaƙwalwarta ba tare da taɓa sauran ɓangarori ba.

Dukkan halittu, kamar masu haihuwa, da tsuntsaye, da masu zama a ruwa, da kifi, na da amygdala wanda sinadarin halittar gado ne mai muhimmanci da ke taimakawa wajen guje wa haɗari.

"Duk lokacin da amygdala ya samu matsala a jikin dabbobi kuma aka mayar da ita cikin daji, mutuwa take yi cikin awanni ko kuma kwanaki," kamar yadda Feinstein ya bayyana.

"Saboda idan babu irin wannan abubuwa da za su taimaka wajen yin rayuwa da sauran dabbobi sukan jefa kan su cikin haɗari."

Amma SM ta iya rayuwa a duniya kusan shekara 50 ba tare da amygdala ɗinta ba, duk da cewa ta shiga haɗurra masu yawa.

"Abin a lamarinta ya nuna min shi ne, ba lallai ne a ce ana buƙatar tsoro ba a wannan zamani," a cewar Feinstein.