Julian Lopetegui ya zama kocin tawagar Ƙatar

Julen Lopetegui

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lopetegui ya ci wa West Ham wasa bakwai cikin 22 da ya jagoranta a dukkan gasa a matsayin koci
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙatar ta sanar da naɗa tsohon kocin Real Madrid Julen Lopetegui a matsayin kocinta kusan wata huɗu bayan korarsa daga ƙungiyar West Ham.

Ɗan Sifaniyan mai shekara 58 ya sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a 2027, kuma shi ne zai jagoranci tawagarta a wasannin neman shiga Kofin Duniya na 2026 da ake yi yanzu haka.

Ƙatar wadda ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya ta gabata, ta gaza samun gurbi a gasar mai zuwa ta hanyar wasannin neman gurbin a karon farko, amma har yanzu tana da damar shiga a wani zagayen da ake yi yanzu.

Lopetegui ya taɓa horar da tawagar ƙasarsa ta Sifaniya. Ya fara aikin a 2016 amma kuma aka kore shikwana biyu kafin fara gasar Kofin Duniya ta 2018 a Rasha bayan ya karɓi horar da kulob ɗin Real Madrid.

Aikinsa ya zo ƙarshe a Real bayan wata huɗu da rabi, inda daga nan ya koma Sevilla kuma ya lashe kofin zakarun Turai na Europa League.

Ya koma Wolves a Nuwamban 2022 amma ya bar ƙungiyar kafin shekara ta zagayo.

Shi ne kociyan West Ham a farkon wannan kakar amma kuma sai aka maye gurbinsa da Graham Potter bayan wata shida.