Wasannin da ke gaban Real Madrid zuwa karshen kakar nan

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid za ta bukaci maki 15 a sauran wasannin da suka rage mata a La Liga a kakar 2024/25 da zarar an shiga watan Mayu ranar Alhamis.

Tuni Arsenal ta yi waje da Real Madrid a Champions League, yayin da Barcelona ta lashe Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey a kanta a kakar nan.

Haka kuma Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya.

Watan Mayu zai kama ranar Alhamis, kwana uku tsakani Real Madrid za ta kara da Celta a Santiago Bernabeu a wasan mako na 34 a La Liga.

Daga nan ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta je gidan Barcelona a La Liga wasan hamayya na El Clasico ranar Lahadi 11 ga watan Mayu a mako na 35.

A wasan farko da suka buga a gasar a Santiago Bernabeu, Barcelona ce ta yi nasarar cin 4-0 cikin watan Oktoban 2024.

Daga nan Real Madrid za ta fafata a sauran wasan La Liga uku da za su rage mata, za ta karɓi bakuncin Mallorca, sannan ta je Sevilla ta karkare da Sociedad a gida.

Bayan kammala wasannin gasar La Liga na bana, Real za ta buga Club World Cup da za ta fara wasan farko da Al Hilal ranar 18 ga watan Yuni a Amurka.

Wasannin Real Madrid da suka rage mata a bana:

  • Real Madrid da Celta, La Liga mako na 34 (Lahadi 4 ga Mayu).
  • Barcelona-Real Madrid, La Liga mako na 35 (Lahadi 11 ga Mayu).
  • Real Madrid-Mallorca, La Liga mako na 36 (Litinin 14 ga Mayu).
  • Sevilla da Real Madrid, La Liga mako 37 (Alhamis 17 ko 18 ga Mayu).
  • Real Madrid da Sociedad, La Liga mako na 38 (Alhamis 24 ko 25 ga Mayu).