Ancelotti zai koma horar da tawagar Brazil

Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti zai ci gaba da tattaunawa kan karɓar aikin horar da Brazil kafin watan Yuni.

Mai shekara 65 ɗan kasar Italiya, zai gana da wakilan hukumar ƙwallon kafar Brazil (CBF).

Ancelotti ya ce batun makomarsa ''za a yi ta tattaunawa a makon gobe ba a yanzu ba'' bayan da Barcelona ta doke Real Madrid ta lashe Copa del Rey ranar Asabar a Sevilla.

An hangi wani attajiri ɗan kasar Brazil, Diego Fernandes, wanda ke wakiltar hukumar ƙwallon kafar Brazil , ya halarci El Clasicon da aka yi a Sevilla.

An fahimci cewar dalilin ziyayar Fernandes zuwa Turai, domin ya lallashi Ancelotti ya amince ya karbi aikin jan ragama Brazil da zarar an kammala kakar Sifaniya.

Kenan idan komai ya daidai ta, Ancelotti zai bar Real Madrid kafin Club World Cup da za a yi a Amurka a bana.

Ancelotti shi ne kan gaba da Brazil ke fatan ɗauka, domin ya maye gurbin Dorival Junior, wanda ta kora sakamakon da Argentina ta caskara Brazil 4-1 a Buenos Aires a watan jiya.

Brazil tana mataki na huɗu a teburin Kudancin Amurka a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Duk da ba ta gurbin barazarar kasa zuwa babbar gasar tamauola ta duniya, Brazil ta ɗora burin cewar Ancelotti ne kaɗai zai kai ta ga kara lashe kofin.

Tun kan fara Copa America a bara, Brazil ta yi ta kokarin ɗaukar Ancelooti, amma ba ta samu dama ba.

Ancelotti ya lashe La Liga biyu da Champions League uku a karo biyu da ya ja ragamar Real Madrid - har da kofi biyu da ya ci a bara.

Sai dai a bana Real Madrid tana ta biyun teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona ta ɗaya.

Haka kuma Real ta yi ban kwana da Champions League na bana, sakamakon da Arsenal ta yi waje da ita da ci 5-1 gida da waje zagayen kwata fainal.

Ana sa ran Real Madrid za ta maye gurbin Ancelotti da Xabi Alonso, mai horar da Bayer Leverkusen.