Haaland ya koma atisaye a Man City bayan jinya

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City, Erling Haaland ya koma atisaye, bayan fama da jinya.

Mai shekara 24 dan kasar Norway ya ji rauni a wasan da City ta doke Bournemouth 2-1 a FA Cup, zagayen kwata fainal ranar 30 ga watan Maris.

Tun farko Haaland ya ci gaba da motsa jiki shi kadai a shirin da yake na murmurewa, ya fara atisaye tare da sauran ƴan wasa City ranar Laraba.

Haaland ya ci ƙwallo 39 a tawagar Norway da ƙungiyar City a kakar nan, koda yake ba a fayyace ranar da zai koma taka leda ba.

Ana sa ran Pep Guardiola zai karin haske kan Haaland ranar Alhamis, wanda zai gana da ƴan jarida kan wasa da Wolves ranar Juma'a a Premier League.

Haka shima, mai Ballon d'Or na bana, mai shekara 28, Rodri ya ci gaba da yin atisaye tare da ƴan wasa, wanda ya ji rauni tun daga watan Satumba.

Rodri, ɗan wasan tawagar Sipaniya ya daɗe yana ta motsa jiki, domin ya murmure da wuri, wanda tun farko aka ce zai yi jinya zuwa karshen kakar bana.

Wata majiya na cewa watakila City ta yi amfani da Rodri a Club World Cup da za a yi a cikin watan Yuni zuwa Yuli a Amurka.

Kenan ba a sa ran Rodri zai buga wa City wasa huɗu da ya rage a Premier League da kuma karawar karshe a FA Cup a watan Mayu.

Yanzu haka City tana ta huɗun teburin Premier League na bana, kofin da Tuni Liverpool ta lashe a ranar Lahadi, kuma na 20 jimilla.

City za ta fafata da Wolves ranar Juma'a a Etihad, za kuma ta fuskanci Crystal Palace a wasan karshe a FA Cup a Wembley ranar 17 ga watan Mayu.