Maharan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun sake sakin mutum huɗu

Asalin hoton, Other
Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun ce ƴan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris sun sake sako mutum huɗu uku daga cikin fasinjojin jirgin da suke riƙe da su.
Mai shiga tsakani a sasantawa tsakanin maharan da iyalan fasinjojin Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
“An saki mutane huɗun ne a yau Juma’a da safe kuma sun zo har nan ofishina suka yi min godiyar shiga tsakani da na yi har maharan suka janye barazanar kashe su da suka yi a baya.
“Sun kuma roƙi dukkan masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya da ta tsaurara matakan ceto sauran fasinjojin da ke hannun maharan saboda halin abin tausayi da suka baro su a cikin dajin ,” a cewar Tukur Mamu.
Zuwa yanzu babu tabbaci kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sako mutanen, amma rahotanni na cewa na baya da aka sha saki sai da suka biya miliyoyin naira kafin su samu 'yancinsu.
Daga cikin fasinjojin da aka saka ranar Juma’a 19 ga watan Agustan har da dattijuwar da ta girmi dukkan fasinjojin, Mama Halimatu Atta mai shekara 90.
Dattijuwar ita ce wacce ake iya gani a wani bidiyo da maharan suka saki a watan da ya gabata inda suke dukan maza daga cikin fasinjojin.
Bidiyon ya ɗaga hankalin ƴan Najeriya sosai na ganin halin da fasinjoji ke ciki, sai dai kwana ɗaya bayan sakin bidiyon ne kuma sai magharan suka saki mutum uku daga cikin fasinjojin.

Asalin hoton, Sheikh Mamu
Wannan shi ne karo na bakwai da maharan suke sakin fasinojin jirgin ƙasan.
Ga jerin lokutan da suka sake su:
6 ga Afrilu – Suka saki fasinja na farko Alhaji Alwan Hassan, shugaban Bankin Noma na Najeriya
16 ga Mayu: Suka saki wata mace mai ciki
2 ga Agusta – Suka saki mutum biyu da suka hada da wani farfesa
11 ga Yuni ; Suka saki mutum 11
25 ga Yuli – Suka saki mutum uku, ciki har dqa wanda suka sa ya yi bayani a bidyon da suka sake wanda suke zane fasinjojin
10 ga Agusta – Suka saki fasinja tara ciki har da ɗan Ango Abdullahi
19 ga Agusta – Suka saki mutum huɗu.
Barayin fasinjan jirgin kasa sun yaudari gwamnati bayan sakin iyalansu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 12 ga watan Agusta, kwana biyu bayan sakin fasinjoji tara, fadar gwamnatin Najeriya ta ce 'yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin sun yaudare ta bayan ta biya musu wasu buƙatu yayin tattaunawar da suke yi da zimmar sako fasinjojin.
Fadar Najeriyar ta faɗi hakan ne 'yan awanni bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da 'yan uwan fasinjojin fiye da 60 da aka sace a watan Maris na 2022.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa gwamnati ta biya wa shugaban 'yan bindigar buƙatarsa da ya nemi a saki matarsa mai ciki, "amma sai suka sake bijiro da wasu buƙatun".
Ba wannan ne karon farko da aka ji cewa 'yan bindigar sun saɓa alƙawarin da aka yi da su ba a tattaunawar, amma shi ne karon farko da gwamnatin ta faɗa da bakinta da kuma ainahin buƙatun masu garkuwar.
"Shugaban 'yan ta'addan nan ya buƙaci a saki matarsa mai ciki. Gwamnati ta kai ta asibiti kuma ta haifi tagwaye, aka nuna masa cewa matarsa da 'ya'yansa na cikin ƙoshin lafiya, kuma aka miƙa wa iyayensa su," in ji Garba Shehu.
Yayin ganawar, Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi amfani da ƙarfi ba wajen ceto 'yan uwan nasu, yana mai cewa "abin da na saka a gaba shi ne a sake su da ransu".
Har yanzu akwai mutum aƙalla 31 da masu garkuwar ke riƙe da su a cikin daji, a cewar gwamantin, wadda ta ce ba za ta yi amfani da ƙrfi ba wajen ceto su.










