Me ke hana jami'an tsaro cika umarnin Buhari na ceto fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna?

Asalin hoton, State House
Wata huɗu ke nan tun bayan sace fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna amma har yanzu jami'an tsaro ba su cika umarnin Shugaba Muhammadu Buhari ba na ceto su.
Ko da yake 'yan bindigar sun sako wasu daga ciki tun bayan sace su ranar 28 ga watan Maris na 2022, har yanzu akwai mutane maza da mata kusan 40 a hannunsu.
An sha jin Buhari na bai wa jami'an tsaro umarnin da bakinsa ko kuma ta bakin masu magana da yawunsa a lokuta daban-daban.
Sabon umarnin da ya bayar shi ne na ranar Lahadi, inda kakakin shugaban, Garba Shehu, ya ce Buhari ya yi dukkan abin da ya kamata har ma "ya wuce ƙima", a martanin da ya mayar bayan sabon bidiyon da 'yan bindigar suka saki.
"Fadar Shugaban Ƙasa na tabbatar wa da al'umma cewa shugaban ƙasa [Buhari] ya yi komai da komai, har ma ya zarta abin da ya kamata ya yi a matsayinsa na Babban Kwamandan Tsaro ta hanyar ƙarfafa gwiwa da samar da kayan aiki ga jami'an tsaro, kuma ba abin da yake jira illa kyakkyawan sakamako," a cewar sanarwar da Garba Shehu ya fitar.
Kafin haka, a ranar 21 ga watan Yunin 2022 - bayan sako mutum 11 daga cikin waɗanda ke hannun 'yan bindigar - Buhari ya ce ya bai wa jami'an tsaro umarnin ceto mutanen "baki ɗayansu kuma a raye".
A cewarsa: "Na bai wa jami'an tsaro umarnin su ƙara himma wajen ceto dukkan fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da suka rage a hannun 'yan bindga. Umarnin nawa a bayyane yake: wajibi ne a ceto dukkan mutanen a raye kuma cikin gaggawa."
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Me ya sa har yanzu ba a cika umarnin Buhari ba?

Asalin hoton, State House
Duk lokacin da shugaban ƙasa ya ba da umarni a matsayinsa na Hafsan Hafsoshin Ƙasa, to ana sa ran za a ga an aiwatar da wannan abin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma idan aka tambayi dalilin da ya sa ba a aiwatar da shi ba, wannan kuma abu ne da ke da matakai daban-daban, a cewar tsohon jami'in soja Kaftin Sadiƙ Garba mai ritaya.
"Sai mu duba mu gani, shi shugaban ƙasa da yake cewa ya bai wa sojoji dukkan abubuwan da suke buƙata, shin da gaske ya ba su?
"Amma ko ya ba su bai gama fita daga zargi ba. Saboda idan ya ba da kayan aiki ya kamata kuma ya dinga bibiya ya ga an yi aikin ko ba a yi ba.
"Idan ka duba sauran ma'aikatu a Najeriya za ka ga ministan ma'aikatar kan duba ya tabbatar kowa ya yi aikinsa, amma mu a aikin soja babu wannan.
"Duk da cewa akwai ministan tsaro, magana ta gaskiya bincikenmu ya nuna ba shi da wani ƙarfin iko a kan shugabannin sojojin; tsakaninsu ne kawai da shugaban ƙasa saboda bai saka wani da zai riƙe masa abubuwa ba, kuma a nan ne za a ɓace masa da zaren.
"Muna jin maganganu iri-iri na badaƙala, daga kan sojoji zuwa 'yan majalisa.
"To kuma shi shugaban ƙasa yana da shugabannin tsaro na farin kaya da zai saka su duba zargin idan akwai gaskiya a ciki.
"Ba zai yiwu a ce shugaban ƙasa yana da hannu a komai ba, sannan kuma duk lokacin da wani abu ya faru sai ya kira shugabannin sojojin nan ya gana da su.
Bai kamata ba, ya kamata a ƙyale minista ya shiga tsakani don su san cewa maganarsu ta ƙare daga nan."
'Umarni ne na siyasa kawai'
Da aka tambayi kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu game da ranar da za a ceto fasinjojin, sai ya ce: "Ba zan iya ce maka ga ranar da za a kuɓutar da su ba, amma abin da jami'an tsaro ke nema a wajen 'yan Najeriya shi ne goyon baya."
Ya sake nanata cewa "Buhari ya bai wa jami'an tsaro dukkan abin da suke buƙata kuma 'yan Najeriya su shirya don ganin abin da zai biyo baya".
Sai dai masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ganin cewa waɗannan umarni na shugaban ƙasa "na siyasa ne kawai tun da har yanzu babu wanda ya rasa aikinsa".
"An yi ne kawai dai saboda kar mutane su ce ba a yi komai ba, ko kuma su ce ba a ma san da faruwar abin ba," a cewar Malam Kabiru Sufi, malamin kimiyyar siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano.
"Idan ka duba za ka ga a daidai lokacin yake [Buhari] taya wasu murna a wasanni.
"To ka ga in da bai yi magana ba sai a ce bai ma sani ba, tun da ga shi yana taya wasu murna da suka yi nasara a wasanni."
Ana tsaka da alhinin rashin imanin da aka gani a bidiyon ne kuma, da safiyar Litinin Buhari ya wallafa saƙon taya murna a shafinsa na Twitter ga 'yar wasan Najeriya Tobi Amusan sakamakon kafa tarihi da ta yi a gasar tsere ta duniya da aka kammala a Oregun, Amurka.
Sai dai a makon da ya gabata shugaban ya ce "haɗin kai da tsaron Najeriya" zai ci gaba da sakawa a ransa ko bayan ya bar mulki, abin da Kabiru Sufi ya bayyana da cewa "a zuci ne kawai, ba a gani a aikace".
"Da ma an sani cewa duk wanda ya kai shekaru irin nasa kuma ya bauta wa ƙasa a matakai da dama dole haɗin kan ƙasa ya shiga ransa, amma tun da yanzu yana da dama amma kuma bai yi ba za a samu kokwanto.
"To kuma da ma haka abin yake damun kowa a zuciya, da wanda yake da damar da wanda ba shi da ita duka yana damun kowa.
"Amma dai sanda yake [Buhari] da damar yin wani abu bai yi ba."
Fasinjojin da 'yan bindigar suka sako zuwa yanzu
Tun bayan garkuwa da su a watan Maris, an sako mutum fiye da 20 daga dajin da ake tsare da su a rukuni-rukuni.
Rukuni na baya-bayan nan shi ne na mutum uku da aka saki ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, cikinsu har da mutumin da aka gani yana magana a sabon bidiyon jim kaɗan bayan sun gama lakaɗa wa mutanen duka.
Haka nan, tun da farko sun saki shugaban bankin harkokin noma na Najeriya, Alwan Hassan bayan an biya kuɗin fansa 'yan kwanaki da sace su.
Sai kuma wata mai ciki da suka sako bayan ta haihu a hannunsu.
A ranar 11 ga watan Yuni kuma aka sake sakin wasu mutum 11 saɓanin alƙawarin da suka yi tun farko cewa za su sako dukkan matan da suke tsare da su, kamar yadda mawallafin jaridar Desert Herald Malam Tukur Mamu ya ruwaito, wanda shi ne ke shiga tsakani a tattaunawar.
A ranar 10 ga watan Yulin nan kuma wasu mutum bakwai suka sake kuɓuta daga hannun masu garkuwar. Yanzu haka akwai mutum kusan 40 a cikin dajin.
Rahotanni na cewa dukkansu sun biya kuɗin fansa kafin a sako su. Wasu rahotannin na cewa sai da kowannensu ya biya naira miliyan 100.










