'Yan fashin daji sun faɗa wa BBC dalilin da ya sa suke kashe mutane

Bayanan bidiyo, 'Yan fashin daji sun faɗa wa BBC dalilin da ya sa suke kashe mutane

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a kullum, inda suke kai hare-hare kan kauyuka da masu ababen hawa tare da yin garkuwa da ɗaliban makaranta.

Kazalika, su kan kashe duk wanda ya nuna turjiya. Su wane ne wadannan mutane kuma me suke so?

A wannan rahoto na musamman, sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya kai ziyara Jihar Zamfara, inda ya tattauna da wasu shugabannin ‘yan bindiga da suka yi kaurin-suna.

Mayaƙan da gwamnatin Najeriya ke kira 'yan ta'adda sun bayyana wasu dalilai da suka ce su ne abin da ya sa suke aikata kashe-kashen da kuma satar mutane.