'Barayin fasinjan jirgin kasa sun yaudari gwamnati bayan sakin iyalansu'

Asalin hoton, State House
Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan bindigar da suka yi garkwua da fasinjnojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna sun yaudare ta bayan ta biya musu wasu buƙatu yayin tattaunawar da suke yi da zimmar sako fasinjojin.
Bayanan na fitowa ne 'yan awanni bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya gana da 'yan uwan fasinjojin fiye da 60 da aka sace a watan Maris na 2022.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya faɗa wa BBC Hausa cewa gwamnati ta biya wa shugaban 'yan bindigar buƙatarsa da ya nemi a saki matarsa mai ciki, "amma sai suka sake bijiro da wasu buƙatun".
Ba wannan ne karon farko da aka ji cewa 'yan bindigar sun saɓa alƙawarin da aka yi da su ba a tattaunawar, amma shi ne karon farko da gwamnatin ta faɗa da bakinta da kuma ainahin buƙatun masu garkuwar.
"Shugaban 'yan ta'addan nan ya buƙaci a saki matarsa mai ciki. Gwamnati ta kai ta asibiti kuma ta haifi tagwaye, aka nuna masa cewa matarsa da 'ya'yansa na cikin ƙoshin lafiya, kuma aka miƙa wa iyayensa su," in ji Garba Shehu.
Yayin ganawar, Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi amfani da ƙarfi ba wajen ceto 'yan uwan nasu, yana mai cewa "abin da na saka a gaba shi ne a sake su da ransu".
Har yanzu akwai mutum aƙalla 31 da masu garkuwar ke riƙe da su a cikin daji, a cewar gwamantin, wadda ta ce ba za ta yi amfani da ƙrfi ba wajen ceto su.
Alƙawuran da 'yan bindigar suka karya

Asalin hoton, Other
Baya ga mata da 'ya'yansa da aka saki, gwamnati ta ce ya sake neman a saki wasu yara da aka kama a Jihar Adamawa, amma duk da haka ba su saki _mutanen ba kamar yadda aka nema.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
_"Cikin dare gwamnati ta tura jirgi ta sa aka ɗauko su, muna sa ran idan an ba su waɗannan za su saki dukkan mutane da suke riƙe da su.
"Amma abin da ya biyo baya sai aka ce sun ce kuɗi suke buƙata. Saboda haka kar a ce gwamnati ba ta komai."
Lokacin da 'yan bindigar suka saki wasu mutum 11 daga cikin fasinjojin a watan Yuni, mai shiga tsakani a tattaunawar Malam Tukur Mamu ya ce ba alƙawarin da aka yi da su ba ke nan.
Wasu majiyoyi sun shaida wa mai shiga tsakanin cewa 'yan bindigar sun rage yawan adadin mutanen da suka ce za su sako ne saboda buƙatar da gwamnatin Najeriya ta gabatar musu, inda su kuma suka kafa nasu sharaɗin.
"Tun farko an amince cewa za su sako dukkan matan da ke hannunsu yayin da ake ci gaba da sasantawa kan sauran mutanen, amma sai suka rage adadin mutanen da za su saka ɗin saboda gwamnati ta buƙaci a haɗo da duka waɗanda ke fuskantar matsananciyar rashin lafiya ko rauni," a cewar Mamu a wancan lokacin.
"Masu garkuwar sun kafa sharaɗin cewa za su saki mutanen ne kawai idan gwamnati ta sako 'ya'yansu matasa (da ba su kai shekara 20 ba) da jami'an tsaro suka kama.
"Masu garkuwar sun kafa sharaɗin cewa za su saki mutanen ne kawai idan gwamnati ta sako 'ya'yansu matasa (da ba su kai shekara 20 ba) da jami'an tsaro suka kama."
_______________________________________
Wasu daga cikin fasinjojin da aka sako sun faɗa wa BBC Hausa cewa yunƙurin 'yan uwansu ne ya kuɓutar da su ba gwamnati ba.
Kazalika, Malam Tukur Mamu ya yi iƙirarin cewa mahaifin yaran da aka saka ranar Laraba da ta gabata ma'aikacin Hukumar Majalisar Tarayya ne amma babu hannun Majasalisar Tarayyar ko kuma hukumar a sakin nasa.
Wasu rahotanni na cewa 'yan uwan fasinjojin sun biya miliyan 100 kan kowane mutum ɗaya kafin a sake su.
Shugaban Bankin Raya Noma na Najeriya Alwan Hassan, shi ne mutum na farko da 'yan bindigar suka saki kuma wata majiya tabbatar da cewa sai da 'yan uwansa suka biya miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.











