Yadda matsalar tsaro ta shafi masu bukata ta musamman a Najeriya

Masu bukata ta musamman

Asalin hoton, OTHER

Lokacin karatu: Minti 3

Masu bukata ta musamman a Najeriya, sun koka kan yadda suka ce matsalar tsaron da ke addabar arewacin kasar tamkar su ta fi shafa.

Masu bukatar sun bayyana yadda suke ganin wasu gwamnatoci na yin biris da halin da suke ciki, wajen mayar da hankali a kan lamurran da suka shafi siyasa, maimakon magance matsalolin, ta hanyoyin shirya tarukan addu'a da kuma tallafa musu domin kawo karshen dabi'ar bara.

Malam Sani Muhammad, Sarkin Makafin Sarkin Musulmi na jihar Sokoto, ya shaida wa BBC cewa irin yanayin da matsalar tsaro ta jefa masu bukata ta musamman a arewacin Najeriya abin babu dadi.

Ya ce," Shekarar 2025 da ke karewa, shekara ce da ba zamu manta da ita ba, domin mun fuskanci kalubale da dama kuma wadanda ya kamata su tashi tsaye domin maganceta ba sa yin abin da ya dace, misali, idan an ce yau ga 'yan bindiga sun shiga garin da masu bukata suke musamman makafi da guragu, ta ya ya zasu gudu domin tsira da ransu, ai sai dai kawai su saduda su bar wa Allah komai ko kuma hawan jini ya kashe ka."

Sarkin Makafin Sarkin Musulmi na jihar Sokoto, ya ce," Maimakon kudaden da gwamnatoci ke samu musamman a bangaren jihohin arewacin Najeriya a rika amfani da su wajen yin addu'oi da sadaka da sauran abubuwan da ake gani za su kawo karshen matsalar tsaro, ba a yi sai dai aje ayi wani abu can da ba lallai ya amfani masu bukata ta musamman ba."

Malam Sani Muhammad,ya ce," Idan aka yi biki sai kaji mai waka ya samu naira miliyan 20, wanda da za a dauki wannan kudi a bawa sarkin makafi ya tara jama'a ayi addu'a ta kwana uku a rabawa duk wanda ya zo wajen addu'ar, da an samu saukin matsalar."

"Rashin tsaron nan ya sa masu bukata ta musamma kamar makafi da guragu da sauransu sun baro kauyukansu sun koma cikin gari, sannan nada masu bukata ta musamman a kauyuka na samun yadda za su ciyar da iyalansu ba sai sun koma cikin gari ba."

"amma saboda matsalar tsaro a yanzu kowa ma ya dawo birni ba wai masu bukata ta musamman ba, to manoma sun kasa noma ta yaya za a taimakwa mai bukata ta musamman?." In ji shi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sarkin Makafin Sarkin Musulmi na jihar Sokoto, ya ce," Yanzu an taru da 'yan gudun hijira da masu bukata ta musamman duk a cikin gari ta yaya za a samu taimako?,"

Ya ce," A bara da 'yan bindiga suka sace wani makaho aka kai shi daji sai da ya shafe wata uku ana neman yadda za a hada kudi domin fansarsa, daga karshe dai 'yan uwansa ne suka rika barace-barace suka tara kudi aka karbo shi, to yanzu bisa la'akari da wannan ai matsalar tsaro babu wanda ta fi shafa ma irinmu."

Malam Sani Muhammad, ya ce," Ya kamata gwamnatoci su sani tun da zabar aka yi, idan aka zo lokacin zabe fa da mu dan 'ya'ayanmu da matanmu dukka muna kada kuri'a, to amma kuma idan aka tashi abubuwa sai a manta damu, domin ba ayi mana wani abu da mu zamu san muma 'yan kasa ko jiha ne."

A cewarsa batun a ce akwai masu bukata ta musamman da ke barace-barace, ai dole ta sa su yi hakan domin da me za su dogara da kansu, ba a koya musu sana'a ba, sannan ba a basu jari ba ta yaya mutum zai dogara da kansa? Babu, sam gwamnonimmu a yanzu sam ba sa kula masu bukata ta musamman ballatana a tallafa musu."