Yadda ƴar aikin gida ke takara a zaɓen Indonesiya

A cikin manyan layukan da ke kudancin Jakarta, na tsinci kaina a matse cikin ƙaramin gidan Yuni Sri Rahayu, inda falo ya rikiɗe zuwa ɗakin kwananta, wanda aka raba shi da wani katako kawai.
"Duk da cewa ina cin wahala da fuskantar kalubale wajen biyan buƙatu na, ina da kyakkywan ra'ayi game da rayuwa", kamar yadda ƴar aikin ta shaida min.
Rayuwa a babban birni a kan ɗan kuɗin da take samu ba abu ne mai sauƙi ba, duk da haka Yuni ba ta ja da baya a ƙudurinta na tsayawa takara a zaɓe mai zuwa ba.
"Za ku iya cewa kuɗaɗen da nake amfani da su wajen yaƙin neman zaɓena suna fitowa ne daga wanke banɗaki," in ji yuni, uwar 'ya'ya huɗu da ta rabu da mijinta.
Fiye da masu kada kuri'a miliyan 200 a Indonesia ne za su kada kuri'a a ranar 14 ga watan Fabrairu domin zaben shugaban kasar, da kuma 'yan majalisa da kansiloli a matakin kasa da na yanki.
Yuni na daga cikin ƴan takara da dama da ke neman ɗaya daga cikin kujerun majalisar birnin Jakarta 106, inda za ta fafata da tarin ƴan takara sama da 1,800.
Yayin da yawancin 'yan takara ke zuba miliyoyi ko ma biliyoyin kuɗin rupiah na Indonesia a yaƙin neman zabensu, Yuni na daukar wata hanya ta daban.
Tana keɓe mafi ƙarancin albashinta na kowane wata na rupiah miliyan biyar kwatankwacin dalar Amurka 317 kenan don amfani da su wajen yaƙin neman zaɓenta -
Wannan yaƙi ne da ke nuna alamun da wuya za ta ci zaben, amma duk da haka Yuni ta ci gaba da jajircewa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ms Rahayu ta ce "Ni 'ƴar takarar Dhuafa cee'," ma'ana 'ƴar takararar mutanen da ake la'akari da su a matsayin masu zaman kansu ko kuma masu rauni saboda yanayin rayuwa mai wahala da rashin tattalin arziki, ko rashin hanyoyin sadarwar tallafi.
Ms Rahayu ta kasance tana amfani da kwanakinta na hutun da ba kasafai take yi ba wajen yaƙin neman zabe, inda take zagawa lungu da sako na Jakarta a kan babur dinta, tana bi gida-gida don ganawa da masu kada kuri’arta.
Ta gabatar da kanta tare da mika kalanda da sitika da aka buga fuskarta a kai sanye da tambarin lemu na jam'iyyar Labour da take wakilta.
"Ina neman addu'arku da goyon bayanku a zaɓen da za a gudanar" kamar yadda ta ce take kira ga mutanen lokacin da take yaƙin neman zaɓe..
"Na fi amfani da kafofin sada zumunta wajen yaƙin neman zaɓe saboda ya fi araha" in ji ta.
Wasu mazauna wurin sun amsa mata da kyau, yayin da wasu kuma sun nuna babu ruwansu da komai, amma da alama hakan bai hana Ms Rahayu ba.
"Dole ne a sami wanda zai wakilcin ƴan aiki a majalisa don mu ba da gudummawa wajen tsara manufofinsu," in ji ta.
Rahayu, wadda makarantar sakandare kaɗai ta kammala ta yarda cewa ba ta da gogewar siyasa. Kungiyarta ta sa ta tsayawa ‘yar takarar jam’iyyar Labour.
"Da farko, ban so ba," in ji ta. "Amma daga bisani na amince don wajibi ne ana buƙatar aƙalla ƴan takara mata kashi 30, daga nan na shiga aikin rajista ba tare da son rai ba, kuma sai na ci duka jarrabawar da aka yi min."
Rahayu, wadda ta kasance ƴar aikin gida tun a shekarar 2018, ta ce ta fuskanci wariya da kuma cin zarafi iri-iri a wurin aikinta.

A cewar kididdigar Indonesia, akwai ma'aikata sama da miliyan 135 a kasar, inda kashi 60 cikin 100 ke aiki ba a hukumance ba, gami da ƴan aikin gida.
Akwai yarjejeniyoyin cikin gida domin kare su amma majalisar dokokin kasar ba ta amince da ƙudirin dokar ma'aikatan cikin gida ba, saboda haka masu ɗaukar ƴan aikin za su sami sauƙi wajen watsi da shi.
"Da yawa daga cikin ƴan aikin gida na fuskantar cin zarafi, wasu ma sun mutu sakamakon hakan," in ji Rahayu
"Na san wani labari da aka kona wata ƴar aiki da ruwan zafi, wata kuma da shokin na wutar lantarki aka kashe ta. Halin da ƴan aiki mata (na yau da kullun) ke ciki sai a hankali."
Sama da ƴan aiki 400 sun fuskanci tashe-tashen hankula daban-daban daga shekarar 2012 zuwa 2021, a cewar bayanai daga ƙungiyar kare haƙƙin ƴan aiki ta kasar (JALA PRT).
'Mutane gama gari kawai'

Daruruwan kilomita kuwa daga Jakarta, a cikin birnin Solo da ke tsakiyar Java, wani mai sana'ar sabulu mai shekaru 44, kuma mai buƙata ta musamman, Slamet Widodo, yana neman kujerar majalisar birnin.
"Ina kama da dan takara talaka saboda ni talaka ne," in ji Mista Widodo, hannayensa suna shafar gefen keken guragunsa.
Ya kamu da cutar shan inna tun yana yaro, inda ya ctar ta gurgunta kafafunsa biyu. Mista Widodo yana samun abin rayuwa ta hanyar kera da sayar da kwalaben sabulun ruwa.
Ya yi kamfen ne ta hanyar rarraba kwalaben sabulu kyauta mai dauke da tambarin fuskarsa, lambar takararsa da tambarin jam’iyyar Prosperous Justice Party – jam’iyyarsa ta siyasa.
"Ina rarraba kwalaben ga matan gida da na haɗu da su, duka a yaƙin neman zaɓe" in ji shi.
Kowace rana, yana ware rupiah 10,000 kwatankwacin dalar Amurka 0.64 kenan domin amfani da su wajen yaƙin neman zaɓensa.
"Ina yin odar sitika a duk lokacin da na samu riba. Idan kuma na sami ƙarin kuɗi, sai na sake bugawa," in ji shi.

Labarun Rahayu da na Mista Widodo na iya zama kamar allura a cikin siyasar Indonesia, amma ba su kaɗai ba ne.
‘Yan takara da suka fito daga yankunan da ba a sani ba na fafatawa a zaben 2024 fiye da kowane lokaci.
Jam'iyyar Labour tana yaƙin neman zabe ne a kan wata manufa ta "mutane gama gari kawai, ba masu kuɗi ba ko fitattun mutane ba.
Sannan kuma adadin mutanen da jam’iyyun siyasa 24 suka zaba a matsayin ‘yan takara ya fi yawa. Ya haɗa da ƴan takarar mata-maza da wakilan al'ummar ƴan asalin ƙasar da masu kai saƙo da babura ta intanet.
Ko yaya, damar da za su iya samun nasara a zahiri "kaɗan ne", a cewar masanin siyasa Hurriyah, daga Jami'ar Indonesia. Ta ce ba su da manyan kadarori uku: kudi da siyasa da zamantakewa.
Kadarorin kuɗi suna da mahimmanci don ba da kuɗin ayyukan yaƙin neman zaɓe waɗanda jam’iyyun ba za su rufe ba, kamar kayan yaƙin neman zaɓe da albashi da kuma wayar da kai.
Ana buƙatar kadarorin siyasa don sanya ɗan takara cikin dabara a kan takardar zaɓe - mafi girma mafi kyau.
Hurriyah ta ce "Dukiyoyin jama'a, kamar shahara ko sanin jama'a, suna da mahimmanci." "Idan muka yi lissafi, zai yi wahala ga ƴan takarar da ba su da magoya baya.

Asalin hoton, GETTY
Wannan abu kuma da ke damun Rahayu shi ne;
"Sau da yawa ina jin rashin kwarin gwiwa na yin takara da 'yan takarar da ke da wadatar kuɗi ko shahararru ko kuma masu hanyoyin sadarwa," in ji ta.
"Na san wasu 'yan takara da suka raba man girki da shinkafa ko kayan abinci na gaggawa ga jama'arsu."
Sai dai ta yi imanin cewa gogewarta a wannan zaben zai yi matukar amfani ga ƴan aiki masu zuwa da za su bi ta.
"Za a iya daukar shekaru 10-15 kafin mu samu kwararrun ƴan aiki a matsayin 'yan majalisa.











