Isra'ila za ta faɗaɗa ayyukan soji tare da ƙwace yankuna a Gaza

Asalin hoton, Reuters
Ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya ce sojojinsu za su faɗaɗa farmakin soji a Gaza da kuma ƙwace yanki mai girma domin mayar da su yankunan Isra'ila.
A cikin wata sanarwa ranar Laraba, Katz ya ce faɗaɗa farmakin na da zimmar "lalata da kuma wargaza yankunan da mayaƙan Hamas ke zaune", kuma hakan na buƙatar kwashe ɗaruruwan Falasɗinawa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da asibitoci yankin suka ce an kashe aƙalla Falasɗinawa 15 a wani hari da aka kai cikin dare.
Ƙungiyar tsaro karkashin ikon Hamas ta ce masu ba da agaji sun gano gawawwaki 12, ciki har da yara, a cikin wani gida a birnin Khan Younis.
Rahotanni sun ce sojojin Isra'ila sun fara kai farmaki ta sama da kuma ruwan alburusai a kan iyaka da Masar, kuma akwai fargabar cewa Isra'ila za ta sake kaddamar da wani sabon farmaki ta ƙasa a Gaza.
A wannan mako, sojojin Isra'ila sun bai wa mutum aƙalla 140,000 a Rafah umarnin ficewa daga gidajensu, kuma ta ba sanarwar shirin kwashe mutane da ke wasu sassan arewacin Gaza.
Isra'ila ta riga da ta faɗaɗa farmaki a wasu sassan Gaza tun soma yaƙi, kuma ta ƙwace yankuna da dama da suka ratsa ta tskaiyar yankin.
Ta kuma kaddamar da sabon farmaki ranar 18 ga watan Maris, inda ta ɗora wa Hamas laifin kin amincewa da sabon tayin Amurka na tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin mutum 59 da take ci gaba da garkuwa da su a Gaza.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ita kuwa Hamas, ta zargi Isra'ila ta saɓa wa asalin yarjejeniyar da aka amince da ita a watan Janairu.
Ƙungiyar iyalan waɗanda ake garkuwa da su da kuma waɗanda suka ɓata a Isra'ila sun ce "sun kaɗu matuka" da suka tashi da labarin shirin faɗaɗa farmakin sojin Isra'ila. A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin Isra'ila da ta mayar da fifiko kan sakin dukkan sauran mutanen da ake garkuwa da su a Gaz.
A lokacin da yake sanar da shirin ƙwace ƙarin yankuna, ministan tsaron Isra'ila, Katz, ya kuma buƙaci ƴan Gaza da su yi abin da ya kamata wajen cire Hamas a Gaza da sakin sauran waɗanda ake garkuwa da su, ba tare da bayyana yadda take son su yi haka ba.
Batun jin-ƙai a Gaza ya taɓarɓare a makonnin baya-bayan nan, inda Isra'ila ta ki barin a shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza tun bayan 2 ga watan Maris - wanda shi ne lokaci mafi tsawo da aka hana agaji shiga tun soma yaƙi.
A watan da ya gabata, Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da cewa za ta rage ayyukanta a Gaza, kwana guda bayan da sojojin Isra'ila ta kashe likitoci takwas Falasɗinawa da masu ba da agaji shida da kuma jami'in Majalisar a kudancin Gaza.
Dakarun Isra'ila sun kaddamar da wani kamfe na wargaza Hamas, don mayar da martani kan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da Hamas ɗin ta kai mata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1,200 da yin garkuwa da 251.
Sama da mutane 50,399 ne aka kashe a Gaza tun bayan kaddamar da yaƙi da Isra'ila ta yi, a cewar ma'aikatar lafiya karkashin Hamas.











