Me ya faru da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Daniel Wittenberg and Lara Owen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare a sassan Gaza, watanni biyu bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma tattauna yadda za a tsawaita ta.
Alƙalumman ma'aikatar lafiya ta Hamas sun ce mutum fiye da 400 aka kashe ciki harda ƙananan yara, tare da raunata wasu ɗaruruwan. Hotunan da aka ɗauka na nuni da cewa akwai wasu da dama da suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin da aka ruguza.
Dakarun Isra'ila sun ce sun kai hare-haren ne a maɓoyar manyan jami'an Hamas, kuma an kashe da dama a cikin su.
Bayan shafe makonni ana zaman lafiya a yankin, sabbin hare-haren suna cikin mafiya muni a tarihi, tun bayan harin da Hmas ta ƙaddamar a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya tunzura wannan yaƙin.
Me yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta ƙunsa?
Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu tana da rukunnai uku. Ta ƙumshi sakin mutanen da Hams ta yi garkuwa da su a ɗaya ɓangare, da kuma sako Falaɗinawan da Isra'ila ke tsare da su a gidajen yarin ta. Kuma an tsara aiwatar da ita ne a matakai daban-daban da nufin kawo ƙarshen yaƙin.
A rukunin farko, Hamas ta saki mutane 25 da take riƙe da su, da kuma gawar wasu takwas, yayin da Isra'ila ta sako fursunonin Falasɗinawa aƙalla 1,800.
Haka kuma, dakarun Isra'ila sun janye daga yankin Gaza mai mutane da yawa domin bayar da dama ga Falasɗinawa su koma gidajen su.
An tsara fara tattauna rukuni na biyu na yarjejeniyar a ranar 4 ga watan Faburiru, amma hakan ba ta samu ba. Rukuni na biyu dai shi ne aka sa ran zai yi tanadin yadda za a kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, wanda zai haɗa da janye dakarun Isra'ila da kuma sakin dukkan mutanen da ake tsare da su.
Rukuni na uku kuma na ƙarshe kuwa, an tsara zai yi tanadin musayar gawarwaki tsakanin ɓangarorn da kuma sake gina Gaza, wanda ake sa ran zai ɗauki shekaru.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya faru daga lokacin?
Tun daga ranar 2 ga watan Maris Isra'ila ta rufe duk wata kafar kai agaji cikin Gaza, a wani mataki na tilastawa Hamas ta amince da sabon shirin Amurka na tsawaita tsagaita wutar, wanda gwamnatin Trump ta gabatar.
Abisa wannan shiri dai, za a saki rabin mutanen da ake tsare da su tun a zangon farko na tsagaita wutar, sannan a saki sauran rabin daga ƙarshe.
Sai dai Hamas ta jajirce cewa sai dai a aiwatar da rukuni na biyu na yarjejeniyar, kamar yadda aka tsara ta a lokacin tsohon shugaban Amurka Joe Biden.
An samu jayayya tsakanin ɓangarorin a kan yawan fursunonin da za a saki, da kuma lokacin da dakarn Isra'ila za su fice daga Gaza.
"Mun ga tsare-tsaren da Isra'ila da Hamas da kuma masu shiga tsakani suka gabatar, kuma duk an yamutsa su,'' in ji wakilin BBC a Gaza, Adnan El-Bursh.
Yarjejeniyar ta rushe kenan?
Lokaci ne kawai zai tabbatar ko wannan sabon salon Isra'ila ne na matsalamba ga Hamas domin ta amince da tayin yarjejeniyar ko kuma sabon yaƙi ta ƙaddamar
Isra'ila ta daɗe tana zargin Hamas da ci gaba da ƙin amincewa da tayin tsagaita wutar da kuma sakin mutanen da ta yi garkuwa da su.
"Daga yanzu, Isra'ila za ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren soji a kan Hamas,'' in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila Oren Marmorstein.
Marmorstein ya ce Isra'la ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a matakai daban-daban, amma ''Hamas ta hau kujerar naƙi, domin haka bamu da wani zaɓi da ya wuce ƙaddamar da hari kan Gaza''

Asalin hoton, Getty Images
Da aka tambaye shi ko hakan na nufin an rushe yarjejeniyar tsagaita wutar kenan, Marmorstein ya bayar da amsar cewa an rushe batun tsagaita wuta tun makonni biyu da rabi da suka wuce.
Ya ce "An ƙulla yarjejeniyar ne domin ta yi aiki tsawon kwana 42. A bisa yarjejeniyar kuma, babu tanadin cewa za a shiga rukuni na gaba kai tsaye ba tare da ƙulla sabbin sharuɗɗa ba,''
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya ce za su ci gaba da yaƙi a Gaza har sai an dawo da dukkan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, da kuma cimma muradunsu na shiga yaƙin''.
Hamas ta buƙaci masu shiga tsakani su ɗora wa Isra'ila alhakin duk abi da ya faru saboda karya sharuɗɗan tsagaita wutan da aka ƙulla.
Amma har yanzu akwai sauran fatan cewa masu shiga tsakani za su iya shawo kan dukkan ɓangarorin domin komawa teburin sasanci.
Wane hali ake ciki game da ayyukan jin ƙai a Gaza?
Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da sabbin harin nasu ne a cikin watan Ramadan, kuma a daidai lokacin da mutanen Gaza ke yin sahur.
"Ƙaraurawar tashin sahur bata gama bugawa ba kawai sai muka ji gidanmu yana rugujewa, ɓaraguzai na fadowa a kanmu,'' in ji iyalan Zain Al-Din, a hirarsu da BBC Arabic.
A ranar 2 ga watan Maris Isra'ila ta yanke safarar abinci da magunguna da man fetur da wutar lantarki da kuma sauran kayan buƙata ga mutane miliyan biyu da ke zaune a Gaza.
Ko kafin harin na baya-bayan nan, an yi ƙiyasin cewa an rusa kashi 70 bisa ɗari na gidajen da ke Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'in hukumar bayar da agaji a yankin Falasɗinu Muhannad Hadi ya ce yanayin da ake ciki ya ƙazance.
''Asibitoci sun cika kuma ga rashin kayan aiki'' in ji Nebal Farsakh, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Crescent.
''Daga cikin mutanen akwai masu karaya da ƙuna da kuma masu buƙatar a yi masu aiki,'' in ji Mohamme Zagout, babban daraktan asibitin Gaza.
BBC Arabic ta tattauna da ƴar uwan Ahmad Mo'in Al-Jumla, wanda aka zaƙulo daga ɓaraguzan gini, kuma ya samu karaya a wurare da dama. Ta ce ''Har yanzu yana jiran layi ya zo kanshi domin a yi masa aiki, kuma yana kwance ne a ƙasa,''
Yanzu dai rundunar sojin Isra'ila ta umarci mutanen Gaza su koma Khan Younis da ke kudanci ko kuma yammacin birnin Gaza.
Wane halin ƴan Isra'ilan da Hamas ke tsare dasu suke ciki?
Ofishin firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce daga cikin dalilan ƙaddamar da hare-haren harda neman mayar da martani ga taurin kan Isra'ila na ƙin sakin mutanen da ta yi garkuwa da su.
Isra'ila ta ce akwai mutanenta 59 da ake tsare da su a Gaza, kuma akwai tabbacin 24 daga cikin su suna raye.
Wata ƙungiya mai wakiltar iyalan waɗanda aka yi garkuwa da sun ta zargi gwamnatin Isra'ila da yin watsi da ƴan uwan nas, ta hanyar kai sabbin hare-haren saman.
"Babban abin da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, da ƴan uan nasu dake hannun Hamas da kuma sauran ƴan Isra'ila ya riga ya faru,'' in ji sanarwar da ƙungiyar ta fitar. Kuma ta fara shirya wata zanga-zanga a sassan Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images
Me ƙasashen duniya ke cewa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amurka ta tabbatar da cewa Isra'ila ta sanar da fadar White House kafin ta ƙaddamar da sabbin hare-haren. ''Da Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa dasu domin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutan, amma sai ta zaɓi a ci gaba da yaƙi,'' in ji kakakin majalisar tsaron Amurka Brian Hughes.
Ƙasar Masar, ɗaya daga cikin masu shiga tsakani a rikicin ta bayyana harin a matsayin ''babban aikin da ya karya tanadin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla, kuma wanda zai ruruta wutar rikicin.'' in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Masar Tmim Khallaf.
China ta ce ta damu matuƙa da hain da ake ciki, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Mao Ning ta ce, inda ta buƙaci ɓangarorin su kaucewa ɗaukar matakin da zai ruruta wutar yaƙin.
Kakakin shugaba Vladimir Putin na Rasha, Dmitry Peskov ya ce halin da ake ciki abin damuwa be, ya kuma yi kiran a kaucewa duk abin da zai mayar da hannun agogo baya.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinki Duniya António Guterres ya ce ya kaɗu da labarin harin kuma ya yi ''kira da babbar murya'' a mutumta yarjejeniyar tsagaita wutan.
Mene ne mataki na gaba?

Asalin hoton, Getty Images
Sharhin wakilin BBC Arabic Muhannad Tutunji, daga Jerusalem:
Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-haren ne da nufin tilastawa Hamas ta amince da sabon shirin tsagaita wuta da jakadan Amurka a gabas ta tsakiya, Steve Witkoff ya gabatar, kamar yadda majiyar siyasa a ofishin firaiministan Isra'ila ta tabbatar.
Akwai alamar ɗaukar matsaya ɗaya a tsakanin gwamnatin Netanyahu domin ganin an cigaba da yaƙin.
Kasancewar Eyal Zamir a jan ragamar rundunar sojin Isra'ila, wani mutum da Netanyahu ya daɗe yana neman ganin ya karɓi wannan muƙami, babu shakka firaiministan ba zai fuskanci wata turjiya ba kan duk wani shirinsa a kan ayyukan sojin Isra'ila.
Yanzu dai Netanyahu na fuskantar manyan ƙalubale a gwamnatinsa, ciki harda rarrabuwar kai game da kasafin kuɗin ƙasa da kuma jayayyar ci gaba da ware guraben aiki na musamman ga Yahudawa a cikin dakarun sojin ƙasar.
Yayin da Isra'ila ke iƙirarin cewa babban burin ta a yaƙin shi ne dawo da mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su, amma Hamas ta jajirce cewa Netanyahu na ƙoƙarin faranta ran ƙawayensa.











