Dole kowanne ɓangare ya mutumta doka a Gaza - Amurka

Gaza

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 2

Amurka ta ce tana sa ran kowanne ɓangare ya mutumta dokokin ƙasa da ƙasa a yaƙin Gaza, duk da cewa ba ta fayyace ko za ta gudanar da bincike mai zaman kansa ba a game da kisan ma'aikatan lafiya da na tsaro 15 da dakarun Isra'ila suka yi ba.

Da take amsa tambaya game da kisan, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Tammy Bruce ta ce: "Duk abinda ya faru, Hamas ce sila, kuma laifin ta ne.''

Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an harba makamai kan motocin ɗaukar marasa lafiya da ke yi mata aiki, a ranar 23 ga watan Maris, inda aka kashe mutane 15 ciki harda ma'aikatan lafiya da ke sanye ta kayan aikinsu.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun ta sun buɗe wuta kan wani ayarin motoci da ya tunkare su ba tare da bayyana ko su wanene ba. Ta kuma ce daga cikin wadanda aka kashe a wajen harda mayaƙan Hamas, amma ba ta ce komai ba game da sauran mutanen da harin ya ritsa da su.

Dokokin ƙasa da ƙasa dai sun haramta kai hari kan fararen hula a fagen yaƙi, kuma sun bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya.

Amurka ce tafi kowacce ƙasa sayar da makamai ga Isra'ila kuma itama doka ta haramta mata sayar da makamai ga ƙasar da za ta yi amfani da su ta hanyar da ta saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa.

Jonathan Whittall, shugaban tawagar bayar da agaji ta Majaliasar Dinkin Duniya a Gaza ya ce an yiwa ma'aikatan nasu da Isra'ila ta kashe kabari ɗaya, inda aka sanya alamar agajin gaggawa a kai.

Ya ce "Abin da ya faru babban abin tashin hankali ne domin kuwa bai kamata a kai hari kan ma'aikatan lafiya da masu aikin ceto ba''.

A ranar 18 ga watan Maris Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza, bayan an gaza cimma matsaya a yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ta da Hamas.

Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta ce mutum fiye da dubu aka kashe a Gaza tun daga lokacin.

Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza ne bayan Hamas ta kai mata farmaki a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda ta kashe mutane fiye da 1,200 ta kuma yi garkuwa da wasu 251.

Alƙalumman ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu sun ce kawo yanzu an kashe mutane fiye da 50,350 a Gaza.