Martanin duniya kan hare-haren Isra'ila da suka kashe Falasɗinawa fiye da 400

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen duniya sun fara tofa albarkacin bakinsu kan hare-haren baya-bayan nan da Isra'ila ta kai a Gaza da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 400.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya 'kaɗu' da hare-haren, kuma ya yi kira da babbar murya da a mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar.
Firaminstan Australia Penny Wong ya ce ƙasarsa na buƙatar ɓangarorin biyu su mutunta tsagaita wutar, inda ya ce ''wajibi ne a kare dukkanin fararen hula''.
Shi kuwa mataimakin Firaministan Belgium, Maxime Prevot, ya yi alawadai ne da hare-haren, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin su tsaya kan yarjejeniyar, domin'' kar a koma gidan jiya''.
Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov shi ma ya bayyana lamarin a matsayin abin damunwa.
A wani gefen kuma China ta ce ta ''damu matuƙa'' kan lamarin kuma tana fatan ɓangarorin biyu ba za su ɗauki wani mataki da zai ƙara ta'azzara lamarin ba, in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Mao Ning.
Da tsakar daren Talatar nan ne dai jiragen yaƙin Israila suka ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama a sassan zirin Gaza wanda shi ne hari mafi girma tun bayan da ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a watan Janairun da ya gabata.
Jami'ai a Gazar sun ce mutane fiye da 400 ne aka kashe, ciki har da wani babban jami'in Hamas na yankin, Mahmoud Abu Watfa.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce Isra'ila za ta ci gaba da kai hare-haren har sai an saki dukkanin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Isra'ila ta kuma ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda Hamas ta ƙi amince wa da shawarar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta mataki na farko.
Dakarun Isra'ila sun bayar da sabbin umurnin ficewa daga wasu yankunan Zirin Gaza, saboda a cewarsu za a ci gaba da kai hare-hare.
A yanzu haka bakiɗaya iyakar Zirin Gaza ta zama yanki mai mummunan hatsari, inda ake umurtar mutane su bar yankunan Beit Hanoun da Khuza'a da Abasan al-Kabira da kuma Al-Jadida.
''Su koma birnin Khan Younis da kuma yammacin Gaza cikin gaggawa'' in ji wani mai magana da yawun dakarun IDF a shafinsa na X.











