Ko yawaitar finafinan Hausa masu dogon zango na rage kuɗin da suke samarwa?

Asalin hoton, Abubakar Bashir Maishadda/Facebook
Ci gaban zamani da ya zo masana'antar Kannywood, wanda ya sa aka koma kasuwancin finafinan Hausa ta intanet, musamman ma a YouTube ya zo da abubuwa daban-daban.
Daga cikin abubuwan da kafar YouTube ta kawo masa'antar akwai dawo da harkokin finafinai, inda jarumai da dama da aka daina jin ɗuriyarsu suka fara komawa ƙadami.
Sai dai wasu na ganin finafinan da ake haskawa a YouTube ɗin sun fara yawaita, wanda a cewarsu, yakan toshe lokacin kallo, inda wasu kuma suke cewa ci gaba ne.
A watan Janairun wannan shekarar ta 2025, an fara fitar da sababbin finafinan Hausa masu dogon zango sama da 10, waɗanda ake nuna wa a tasashin YouTube daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar.
Tasirin YouTube

Asalin hoton, Saira Movies
Harkokin finafinan Kannywood sun koma YouTube ne tun bayan da tattalin arzikin masana'antar ya taɓarɓare a sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa YouTube ɗin zai inganta kasuwancin masana'antar kamar yadda yake a baya.
An daɗe ana finafinan Hausa masu dogon zango, amma fim ɗin Izzar so na Lawan Ahmad na cikin waɗanda suka fara jan hankalin masu shirya finafinan masana'antar, inda yanzu kusan duk manyan furodusoshi suka koma haska finafinansu a kafar.
A baya can, a kan nuna fim babba ne a duk rana, amma yanzu finafinan sun yi yawan da dole a haska biyu ko sama da haka, wanda hakan ya sa wasu ke cewa suna shan wahalar iya kallon finafinan.
Sababbin finafinan da aka fara a Janairu

Asalin hoton, Multiple
1. Jamilun Jidda
2. Mijin mace ɗaya
3. Sharaɗi
4. Duniyar nan
5. Budurwar Mijina
6. Aurena
7. Mahadi
8. Matar mijinta
9. Ke ce sanadi
10. Mijina
11. Ke ɗaya ce
Ci gaba ko koma-baya?
Ganin yadda finafinan masu dogon zango suke yawaita, sai wasu ke ganin hakan a matsayin ci gaba, a gefe guda kuma wasu ke cewa sun yi yawa.
Habibu Maaruf Abdu, mai sharhi ne a kan finafinai, ya shaida wa BBC cewa za a iya kallon yawaitar finafinan a matsayin ci gaba, sannan a gefe guda za a iya kallon hakan a matsayin koma-baya.
A cewarsa, "Ci gaba ne wajen samar da ayyukan yi ga jarumai da sauran ma'aikata, da kuma ba ƴan kallo damar samun sababbin finafinai a kodayaushe. Amma yawaitar yin finafinan zai iya taɓa ingancinsu sakamakon gaggawar fitar da su. Hausawa suna cewa "In dambu ya yi yawa, ba ya jin mai." Kuma za su iya cunkushewa a kasuwa a rasa samun wanda zai yi babbar nasara."
Sai dai ya ce shi ma yana da ra'ayin a haɗa ƙarfi, a fitar da fim gagarumi zai fi kyau, saboda "Ai da tarin yuyuyu, gwara ɗaya ƙwaƙƙwara."
Ya batun kawo kuɗi?

Asalin hoton, Habibu Maaruf Abdu/Facebook
Wani abun da mutane suke faɗa shi ne, yawaitar finafinan zai toshe hanyoyin samun kuɗi ga masu shirya finafinan.
A game da wannan ne Habibu ya ce, "Dole zai taɓa kuɗin shiga, tunda masu kallo za su raba hankalinsu. Ka ga YouTube su yawan ƴan kallo suke dubawa wajen biya. To maimakon fim ɗaya ya samu ƴan kallo misali mutum dubu ɗari biyar, sai ka ga bai fi dubu ɗari zai samu ba misali saboda akwai wasu finafinan da yawa."
Haka kuma yawaitar finafinan manyan furodusohi na hana kallon na ƙananan masu shiryawa, "finafinan suna da yawa, sai ka rasa wanne ne ba wanne ne ba," in ji shi.
Sannan ya ƙara da cewa ya kamata a samu tsayayyen tsari da zai riƙa ƙididdige finafinan da za a haska saboda ƴan kallo su sansu, kuma su san wanne za su bibiya.
Yaya ingancin finafinan a yanzu?

Asalin hoton, Abba El-Mustapha/Instagram
A game da inganci kuwa,masanin harkokin finafinan ya ce akwai bambanci tsakanin finafinan Hausa masu dogon zango da na ƙasashen waje.
"Ka ga masana'antar fim ta Hausa ba su daɗe da fara mayar da hankali wajen finafinai masu dogon zango ba. Su kuma sauran ƙasashe, misali Amurka da India, sun riga sun yi nisa. Don haka, salon rubuta finafinan da ingancin aiwatar da su ya sha bamban nesa ba kusa ba. Har ma yadda ƴan kallo suke ɗaukarsu ba ɗaya ba ne."
Sai dai ya ce idan ana so a yi gyara, dole masu shirya finafinan Hausa su ƙara dagewa wajen inganta ayyukansu.
"Akwai waɗanda fim ba harkarsu ba ce, kawai sai su ce za su shige ta gaba-gadi, kuma sai ka ga babban jarumin Kannywood ya shiga sun yi fim mara inganci tare da shi."











