Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke jefa jam'iyyun Najeriya cikin rikici dab da babban taro na ƙasa?
Rikicin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke ciki yanzu ba wani sabon abu ba ne a ita kanta jam'iyyar, yayin da take shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a watan Nuwamba mai zuwa.
Da ma an daɗe da saka zare tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da shugabancin jam'iyyar, yanzu kuma sai ga shi an saka wani sabon zaren game da babban taron.
Wani rukuni da ke goyon bayan Wike sun ce ba za su bari taron ya tafi yadda aka tsara shi ba matuƙar ba a cika wasu sharuɗa da suka gindaya ba.
'Yan PDP ɗin da suka kira kan su Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of the PDP, sun faɗa cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa dole ne muƙamin shugaban jam'iyyar na ƙasa ya koma yankin arewa ta tsakiya.
A watan Agusta ne kwamatin gudanarwa na PDP ya yanke shawarar barin dukkan muƙaman jam'iyyar a shiyyoyin da suke yanzu haka, kuma suka ware wa yankin kudancin ƙasar kujerar takarar shugaban ƙasa.
Rahotonni sun ce daga cikin masu adawa da shirin babban taron jam'iyyar akwai tsofaffin gwamnoni Samuel Ortom (Binuwai) da Ayo Fayose (Ekiti) da Okezie Ikpeazu (Abiya), sai kuma sakataren jam'iyya Samuel Anyanwu.
Rikicin cikin jam'iyyu ya daɗe da zama yayi a siyasar Najeriya, musamman idan babban zaɓe ko babban taronsu na ƙasa ya ƙarato.
Hakan ya sha faruwa hatta a jam'iyya mai mulki, kamar yadda muka gani a APC daga 2020 zuwa 2021.
Sharuɗɗan da ɓangaren Wike ya gindaya
Babba daga cikin sharuɗɗan da suka gindaya shi ne cewa a mayar da muƙamin shugaban jam'iyya na ƙasa zuwa yankin arewa ta tsakiya, saɓanin hukuncin da kwamatin gudanarwa ya ɗauka na barinsa a arewa maso gabas.
Idan aka yi hakan, Ilya Damagun da ke riƙe da muƙamin a matsayin riƙon ƙwarya zai sauka daga muƙaminsa saboda ɗan jihar Yobe ne.
Kazalika, sanarwar rukunin ta ce dole ne a sake sabon zaɓen shugabannin jam'iyyar da aka gudanar na shiyyar kudu maso gabas, sannan a amince da sakamakon zaɓukan kudu maso kudu da aka yi a Kalaba - wanda ɓangaren Wike ya gudanar.
Kazalika, sun sharɗanta cewa lallai sai an gudanar da zaɓen shugabannin PDP na ƙananan hukumomin jihar Ekiti nan take.
"Muna yin gargaɗi cewa idan har aka gaza cika waɗannan sharuɗɗa, duk wani taron ƙasa da za a yi haramtacce ne saboda an hana halastattun 'ya'yan jam'iyyar 'yancinsu," a cewar sanarwa tasu ranar Litinin.
Zuwa yanzu PDP ba ta ce komai ba game da sababbin sharuɗɗan. A ranar Talata kuma ta rantsar da babban kwamatin shirya taron na ƙasa da za a yi a jihar Oyo a watan Nuwamba mai zuwa.
Sai dai kafin yanzu shugabanta na kasa Ilya Damagun ya fada wa BBC cewa Wike bai isa ya hana su gudanar da taron ba.
'Kasuwar bukata'
Ganin cewa PDP ta riga ta yanke shawarar barin mukamai a yankunan da suke, ana ganin ba za a bata lokaci ba wajen zabar shugabanni yayin taron na watan Nuwamba.
"Amma duk da haka daya daga cikin abubuwan da ke jawo zafafar rikici a cikin jam'iyyu gabanin zabe shi ne yunkurin neman biyan bukata daga 'yansiyasar," a cewar Dr Mukhtar Bello na sashen nazarin kimkyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano.
DDr Mukhtar ya kara da cewa bukatun nasu kan hada da tunanin yin wata takara a nan gaba, ko kuma taimaka wa wani da yake son yin takarar.
"Shi ya sa za ka ga 'yansiyasar na rububin dora wani rukunin shugabanni da suke so saboda tunanin kuri'un da za su samu idan an zo zaben fitar da gwani," in ji shi.
Duk da cewa Nyesom Wike ya yi takara a baya, an yi imanin ba zai nemi takarar ba a yanzu saboda ya ce ba zai yi hamayya da Shugaban Kasa Bola Tinubu ba a takarar 2027.
Masanin ya ce wani karin dalilin shi ne irin makarkashiyar da jam'iyya mai mulki ke yi a jam'iyyar adawa.
"Ba kawai APC ba a yanzu, ita ma PDP a lokacin da take mulki ta yi wa jam'iyyun adawa kafar ungulu saboda kada su kawo mata cikas a lokacin zabe.
"Kuma idan rugingimun suka yi yawa, to ko da bayan zaben za a ci gaba da fafatawa a kotu, wanda hakan zai kara bai wa jam'iyya mai mulki damar cin zabe cikin sauki," kamar yadda ya bayyana.
Rikcin APC
A watan Yulin 2021, jam'iyyar APC mai mulki ta tsinci kanta cikin rikici, yayin da ya rage 'yan kwanaki kafin gudanar da babban taronta na ƙasa.
Rikicin ya kawo ruɗani ne sakamakon wani hukuncin kotu da ya haramta shugabancin Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, inda alƙalan Kotun Ƙolin Najeriya suka ce saɓa wa tsarin mulki ne gwamna mai-ci ya riƙe da shugabancin jam'iyyar siyasa.
A watan Yunin 2020 ne jam'iyyar ta rushe kwamatin gudanarwarta kuma ta naɗa Mai Mala a matsayin shugaban kwamatin riƙo.
Zuwa tsakiyar watan Mrais na 2022 kuma, APC ta sake maye gurbin Mai Mala da gwamnan Neja na lokacin , Abubakar Sani Bello, a matsayin shugaban kwamatin 'yan kwanaki kafin babban taron a ranar 26 ga watan Maris.
A wannan taron ne kuma aka zaɓi Abdullahi Adamu tsohon gwamnan jihar Nasarawa a matsayin shugaban APC na ƙasa, wanda kuma ya ajiye muƙaminsa a watan Yulin 2023 'yan watanni bayan jam'iyyar ta sake cin zaben shugaban kasa.