Wike bai isa ya hana mu gudanar da babban taronmu na ƙasa ba — PDP

Lokacin karatu: Minti 3

Ga dukkan alamu babban taron kasa da babbar jam'iyyar adawar Najeriya ta PDP ke shirin gudanarwa a jihar Oyo na fuskantar matsala, bayan da tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan birnin tarayyar kasar Abuja, Nyesome Wike, ya lashi takobin kin amincewa da gudanar da shi.

Wannan adawa da Wike ke yi da taron na da nasaba da rashin jituwa da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, wato gwamnan jihar da za a gudanar da taron.

Wannan lamarin dai na neman jefa jam'iyyar cikin sabon rikici, duk kuwa da cewa tana bayyana dinke barakar cikin gidanta da ta dade tana fama da ita.

Tuni da jam'iyyar PDP ta ce ta kamala dukkan shirye-shiryen gudanar da babban taron daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Satumbar 2025.

Malam Ibrahim Abdullahi, shi ne mataimakin sakataren watsa labaran jam'iyyar ta PDP na kasa, ya shaida wa BBC cewa, anjima ana kiran jam'iyyar ta dauki mataki a kan Nyesome Wike, amma sai aka lura cewa idan aka dauki wannan matakin zai iya haifarwa da jam'iyyar matsala.

Ya ce," To mun guji matsala amma kuma sai gashi yanzu tana binmu, domin shi Wike mutum ne mai son jan fada."

Malam Ibrahim Abdullahi, ya ce," Da Wike na biyayya ga jam'iyya to ya kamata ya rinka bi da amfani da manufofin jam'iyyar, amma ba ya yi, don haka duk wani mataki da yak e so ya dauka dangane da babban taron da jam'iyyarmu ta PDP zata yi, muma a shirye muke mu mayar masa da martani."

"Domin akwai wasu matakai da Wike ya dauka da ke nuna cewa ya riga ya karkata wajen tallata gwamnatin APC." In ji mataimakin sakataren jam'iyyar ta PDP.

Nyesome Wike, dai jigo ne a jam'iyyar ta PDP, kuma ya ce shi sam ba shi da labarin wannan taro, kuma ba zai amince da shi ba ko da an gudanar da shi, domin akwai matsaloli da yawa da jam'iyyar ta kasa magancewa.

Wike ya ce muddin 'yan tsirarun mutane suka gudanar da taron, to sun yi wa kansu ne kawai, ba zai wakilci taron kwamitin zartaswa na kasa ba, inda ya ce shi da magoya bayansa za su yi tsayin daka domin yaki da rashin gaskiyar da ke cikin PDP.

Akwai dai 'yan Najeriya da dama da ke yi wa Wike kallon kadangaren bakin tulu a jam'iyyar ta PDP.

A yayin wani taro da shugabannin gudanarwar jam'iyyar PDP na kudancin Najeriya suka gudanar a jihar Legas a ranar Alhamis 21 ga watan Augustan 2025, sun mayarwa ministan birnin tarayyar Najeriyar, martini.

Taron ya hada da shugaban kwamitin amintattun PDP Adolphus Wabara da gwamnonin yankin kudu maso yamma na Bayelsa da Enugu da Osun da kuma 'yan majalisar tarayyar kasar na PDP 12 da sauran su, inda gwamna jihar Oyo Seyi Makinde, ya ce Wiken na wuce gona da iri kuma babu wanda ya isa ya bata wa PDP tafiya balle kuma hana ta gudanar da taronta na kasa da aka riga aka sanya wa rana.