Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PDP ta yi taro don warware rikicinta na cikin gida
Kwamitin gudanarwa na babbar jam'iyar hammaya a Najeriya watau PDP ya gudanar da wani taro a birnin Abuja, don duba matsalolin da jam'iyyar ke fama da su.
Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ce wannan shi ne karon farko da kwamitin ya yi taro ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar na riƙo Ambasada Umar Damagun a bana.
Gabanin taron dai an so a samu yamutsi, inda tarin ƴan daba ɗauke da makamai suka mamaye ƙofar shiga shalkwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja, kafin daga baya jami'an tsaro suka tarwatsa su.
Taron na zuwa ne bayan da kotun ƙoli ta yi watsi da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na tsige Sanata Samuel Anyanwu daga mukamin sakataren jam'iyyar na ƙasa, inda ta maye gurbinsa da Hon Sunday Udeh Okoye.
Malam Ibrahim Abdullahi, mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar ta PDP a Najeriya ya shaidawa BBC cewa taron ya tattauna akan batutuwa da dama ciki harda matsalolin jam'iyyar na baya baya nan:
''Taro ne wanda ya shafi matsalolin jam'iyya musaman na baya baya nan waɗanda suke da alaƙa da matsayin kwamitin amintattu, don a yi mu su tuni cewa kujerun wasunsu ya riga ya kai ƙarshen wa'adi da kuma abubuwan da suka shafi ofishin shugaban jam'iyya watau sakataren jam'iyya na ƙasa ''
''Taron ya kuma yi nazari kan inda jam'iyyar ta kwana a yanzu, matsayin matsalolin da ke ƙasa duk sune aka tattaunawa don a samu shawarwarin yadda za a ciyar da ita gaba',' in ji shi.
Game da rikicin sakataren jam'iyyar kuwa, Malam Ibrahim ya ce kamata ya yi a yi hakuri a jira hukuncin kotu
''Yanzu abinda ya kamata mu yi shi ne mu yi haƙuri mu jira abinda kotu za ta zartar domin in dai magana tana gaban kotu ba a furuci a kansa''
Sai dai tuni wasu suka nuna damuwa akan ko jam'iyyar za ta iya taka rawar a zo gani a zaɓen 2027 idan aka yi la'akari da rikicin cikin gida da take fuskanta. Malam Ibrahim ya ce yana da ƙwarin gwiwa cewa jam'iyyarsu za ta 'taka rawar gani'.
''Tun da aka ƙirƙiro siyasa a Najeriya babu jam'iyyar da ta wuce shekara goma a tarihin Najeriya sai PDP, yau shekarar ta 27 kuma da ita ake yi , duk mutanen da ake ganin suna waje sun dawo, har tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya taɓa yanka katinsa ya yi wurgi da shi amma kuma ya dawo yana goyon bayan PDP''
'' Wannan ma wata gaɓa ce da idan Allah ya yada za mu wuce ta kuma za mu ƙwace mulki mu fidda Najeriya daga cikin wannan ƙangi na baƙin ciki na rashin tsaro da ta'annati da ake yi wa ƴan ƙasa wanda zai zama tarihi a shekarar 2027. Abinda ya ke maslaha yanzu a san yadda za a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajan ƙwato mulki daga hannun waɗanan mutane,'' in ji shi.